200+ Sunayen Zamani Masu Daɗi ( Maza da Mata)
Sunan mutum a gare shi/ ta shine sauti mafi daɗi kuma mafi mahimmanci a kowane harshe. Ko yaran ku sun gaji Sunayen su ko ma basu gada ba, wannan ya daganci yanayin tunanin su ne. Amma akwai ɗan gaskiya a faɗin " suna na iya saita rayuwar mutum". Wannan shi yasa muka jero muku waɗannan sunayen zamani masu daɗi.
Sunayen Zamani na Mata Masu Daɗi
A zahiri Kuna son ƴarku ta daraja sunan da kuka zaɓa mata. A yayin da sunaye suka sha babban a kyau, yana da matuƙar anfani kuyi duba ga sunayen mata na zamani masu daɗi da kuma kyawun asali. Waɗannan sunayen mata ne masu daɗi da zaku iya zaɓa.
Eeman = Imani
Ameerah = Gimbiya
Ihsan = Kyautatawa
Intisar = Mai nasara
Husna = Kyakkyawa
Mufida = Me anfani
Amatullah = Baiwar Allah
Ahlam = Me kyawawanj mafarkai
Siddiqa = Mai gaskiya
Sayyada = Shugaba
Khairat = Me alkhairi
Afaf = Kammamiya
Basmah = Murmushi
Nasreen = Wata fulawa mai kamahi a gidan aljannah
Saliema = Mai aminci
Rauda = A cikin masjid nabawi
Samha = Mai kyau
Siyama = Mai azumi
Sawwama = Mai yawan azumi
Kawwama = Mai Sallar dare
Nuriyya = Haskakawa
Noor = Haske
Sabira = Mai haƙuri
Meead = Alkawari
Islam = Musulunci
Nawal = Kyauta
Afrah = Farin ciki
Mannal = Wadata
Faiza = Babban rabo
Hannah = mai tausayi
Sajeeda = Mai yawan sallah
Hameeda = Godiya ga Allah
Afnan = Ci gaba
Nabiha = Mai kwazo
Yusurah = Mai sauki
Salsabil = Mai sauki da jin kai
Mila = Mai kwazo =
Farrah = Mai farin ciki
Amina = Amintacciya
Jihan = Rai
Amrah = Farin ciki
Arwa = Alheri
Asma = Mafi girma
Atheelah = Mai aiki da adalci da gaskiya
Aliya = Mai tashi
Azban = Sabo
Baghoom =
Barakah = Wacce ke da taushin murya mai mace
Bareerah = Mai tsoron Allah
Barzah = Ta kasance mai ruwayar hadisi
Buhayya = Mai dadi
Bushrah = Labari mai dadi
Fakhitah = Kurciya
Fariah = Farin ciki
Farwa = Rufewa
Fasham = Babba kuma Fadi
Fatima = Jan hankali
Firozah = Mai Nasara
Fakaihah = Fure
Ghufairah = Gafara
Habibah = Masoyiya
Hannatu = Mai tausayi
Halah = Halo a kusa da wata
Halima = Mai hankali
Hammat = Abin kunya
Hamizah = Abin sha'awa
Nasiba = Sa'a
Isma = Kariya daga zunubi
Jamila = Kyakkyawa
Jumail = tsuntsu mai waƙa
Jumanah = Lu'u-lu'u na azurfa
Juwairiyya = Yarinya karama
Kareemah = Mai Karimci
Khadijah = Amintacciya
Na'ma = Komawa ga Tushen
Khawlah = Barewa mace.
Kulthum = Wani mai girman fuska
Lailah = Dare
Lubabatu = Sarauniyar Aljanna
Lubaynah = Madara mai tsafta
Maria = Masoyiya
Maymunat = Albarka
Nahdiya = Mai sanarwa
Najiya = Yanci daga haɗari
Nusaibah = Dace
Qutaylah = Jagora da zuciya
Rakheelah = Tashi
Ramlah = Mai hankali
Raheenat = kaddara
Rufaida = Ƙaramar mataimakiya
Ruman = Soyayya
Rumaisa = Fure-fure
Ruƙayyah = Mai jan hankali
Safiyyah = Tsafta
Sahla = Santsi
Salma = Aminci
Sarinnah = Kyakkyawan aboki
Shifa = Waraka
Shirin = Dadi
Zeenat = Ado
Sunayen Zamani na Maza Masu Daɗi
Sanya sunan ɗan yaron ku, shawara ne da za a iya yankewa a cikin rana guda, amma ku sani zai gaya wa duniya wani abu game da shi, addinin sa, asalin sa, da kuma al'adan sa. Kuna son suna wanda zai so kuma ya yi alfahari da shi. Don haka muka jero muku waɗannan sunayen maza masu daɗi kuma na zamani.
Tahmid = Godiya ga Allah maɗaukaki
Ammar = Wadataccen tsawon rai
Abd el-Hakim = Bawan mai hankali.
Ghassan = farkon rayuwa
Ismail = Allah ya ji
Ilham = Ilham
Ghalib = Cin nasara
Irfan = Fadakarwa
Abdul = Bawa
Adel = Mai daraja
Barack = Mai albarka
Ala = reshe
Jamal = Kyakkyawa
Bilal = Mai nasara
Ihsan = Yin abu mai kyau
Jalal = Girma
Gallal = Girma
Abbas = Zaki
Mukhtar = Zababbe
Junaid = Jarumi
Hamid = Yabo
Ala'Din = Nobility of faith
Fuad = Manufar "hankali da ruhu
Asim = majiɓinci
Baqir = Hankali
Abd al-Karim = bawan Mafi Karamci
Abd al-Hamid = Bawan mai bayarwa.
Jafar = Ruwa
Fihar = Kulawa
Hasib = Mai daraja
Gabar = Dan kungiyar addinin Iran
Sayi = farar ƙaramin fure mai laushi mai ƙamshi mai kyau.
Bilyamin = Mai hankali
Amjad = Mai Girma
Ali = Zakaran
Faiz = nasara
Abdur Rashid = bawan mai gaskiya.
Iman = Imani
Nazir = Mai lura
Abdullahi = Bawan Allah
Imran = Farin ciki
Fadi = Mai fansa
Mu'az = Mai kariya
Bassam = Mai murmushi
Yahuza = Wayayye
Baki = Murmushi
Afzal = Koyi
Fadil = Nagari madalla da cikawa
Isah = Addu'ar dare
Ahmad = Mai godiya ga Allah
Akram = karimci
Asif = Gafara
Mannir = Zauren wani kadara
Adnan = Mai shiryawa
Gamar = Faɗawa soyayya
Azhar = Haskakawa
Amal = Fata
Faris = Mahayin doki
Abdulkadir = Bawan mai iya komai
Sufyan = Tafiya da sauri
Anisi = Taimako
Atallah = Bawan Allah
Saifullah = Takobin Allah
Fahad = Damisa
Asad = Zaki
Hussaini = daga sunan Imam Husain bn Ali
Anwar = haske
Atiya = Kyauta
Munir = Haskakawa
Al'amin = Amintacce.
Jihan = Duniya
Musbah = Fitila
Sauki = kyakkyawa
Ayman = Mai sauki
Jabbar = Babba
Ansar = Mataimaki
Anas = Wanda ya iya zama da mutane
Alhassan = Mai kyau
Usama = Zaki
Dawood = Sunan annabi
Amir = Yerima
Hafiz = Mai kiyayewa
Basil = Bawan Mai faɗaɗawa
Haruna = Sunan annabi harun
Hamza = Tsayawa
Aqib = Na gaba
Aqil = Mai hankali
Yasir = Da kyau a yi
Abi fadil = Mai girma
Iskandar = Kare maza
Diya = Haskaka
Abd al-samad = bawan Jagoran mai arziƙi
Jabir = Mai ta'aziyya
Haidar = Zaki
Shariff = Daukaka
Kamil = cikakke
Mahdi = shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya
Uzaifa = wanda ke kaurace wa
Mubeen = bayyana
Mufaddal = Zaɓaɓɓe
Kammalawa
A karshe dai, yaran mu sun cancanci Sunaye masu inganci da zasu iya alfahari da shi. Hakkin yara ne akan iyaye da su saka musu suna ta yadda addini ya sanar. Don haka muyi koƙari wajen ganin cewa mun zaɓa wa yaran mu Sunaye na zamani masu daɗi.
Fuan
ReplyDeleteTaufid
ReplyDelete