Jerin Sunayen Soyayya Masu Dadi [Larabci da Turanci]
Soyayya akace ruwan zuma wasu kuma sukace tafi zuma dadi. Kiran kanku da sunayenku gaskiya tsohon yayi ne, dan kuwa hakan na nuna soyayya baishigo tsakaninku ba kenan. Kiran kanku sunayen soyayya masu dadi kadai ma dafi ne da zai kara shakuwa a tsakaninku. Abun jindadin anan shine, akwai jerin sunayen soyayya daban-daban da zaku Iya zaba dan kawunan ku. Zaku Iya kiran kawunan ku da sunayen soyayya da larabci (irinsu habibi) kokuma sunayen soyayya da turanci (irinsu baby ko sweetheart). Cigaba da karantawa dan ganin ire-iren jerin sunayen soyayya da zaku kira junan ku da ita na larabci da turanci. Amfanin Kiran Masoyi/Masoyiya Sunayen Soyayya Kiran kanku da sunan soyayya na da matukar amfani sosai dan zai kara damkon soyayya da shakuwa a tsakaninku ta hanyar da baku yi tinani ba. Misali ace saurayi yaje gurin budurwa sa, kawai ya kirata da sunan ta, in wata rana ta amsa, wata ranan bazata amsaba, cewa ma zatayi "bai iya soyayya ba" kokuma kaji tana cewa ni ba sa'ar