Kalaman So Ga Budurwa
Dan saurayi, kalaman soyayya ga budurwa na daga cikin abubuwan da zasu rike maka budurwar ka. A wannan shafin, mun jero maku zafafan kalaman soyayya ga budurwa dan inganta soyayyar ku.
Shiga cikin ka ga Lafazin soyayya masu dadi wa inda zaka iya turawa budurwa masu nishadantarwa.
-----
**1**
Masoyiya ta kinsan meyasa nake kasancewa cikin farin ciki a koda yaushe, ko wacce dare, muryar ki ke samar da natsuwa a zuciya ta kafin na kwanta bacci. Duk safiya inna tashi daga bacci, muryar ki ke samar mun da farin ciki. Da fatan kina lafiya.
**2**
Zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nidai dama nake bukata.
**3**
Ina so kiyi mun wata alfarma guda daya, inaso fuskar ki ayayin da kike murmushi ta zama fuskar da zan gani karshe kafin na kwanta, haka zalika fuskar da zangani bayan na tashi daga bacci duk safiya. Zaki iya bani wannan damar.
**4**
Daga haduwa dake, kinbani duk wani dalilin da zai sa nakasance cikin farin ciki a kullin. Na kasa auna irin farin ciki da natsuwan da nake samu daga wurin ki. Ke ta musamman ce a cikin mata. Kallon fuskar ki kina murmushi shine muradi na.
**5**
Nasamu babban rabo a wannan rayuwan kinsan meyasa? Nasami budurwa tamkar aminiya, mai kula dani, mai sani farin ciki, tana kaudar mun da bakin ciki. Hakimar dake tare da ke yafi mun komai a wannan duniyar.
Karanta Sauran Kalaman So Ga Budurwa Guda 200
Kalaman So Ga Saurayi
Kina neman kalaman soyayya masu dadi zuwa ga saurayi? Toh shiga cikin wannan shafin dan samun kalaman soyayya masu ratsa zuciyar saurayi. Ki fa tuna, da lafazin so kawai, zaki iya mallake saurayin har yaki kallon wata budurwan.
Mun jera maki kalaman so masu dadi guda dari biyu masu nishadantarwa da ratsa zuciya.
-----
**1**
Masoyi na, kasan meyasa nake son ka? Soboda babu abunda kafi so a zuciyar ka face sani farin ciki. Nazamo mace mai son namiji wanda zai damu dani, ya soni kamar yadda yake son kansa, kuma na sameka. Ina son ka.
**2**
Tunda nake a rayuwa ta, ban taba zaton zan shiga irin farin cikin nake ciki yanzu ba. Soboda kai, na daina shiga damuwa, na daina jin duk abunda mutane suke fada duk ta dalilin ka. Saurayi irin ka a wannan zamanin, kudi bai iya siyar su.
**3**
Duk safiya inna tasi daga bacci banji muryar ka ba. Sai naji kamar an soke ni a cikin zuciya. Shiga cikin damuwa nakeyi. Duk dare inban saurari muryar ka ba, ban iya bacci dan babu natsuwa a tare da ni ko kadan.
**4**
Na dade ina tinani akan wani irin saurayi ne ya dace dani, amma zuciya ta kasa bani gamsasshiyar amsa, amma haduwa ta da kai ta bani duk amsa dana dade ina jira. Ka shigo rayuwa ta da abubuwa na ban mamaki. Duk wani rashin jindadi ya rabu dani soboda kai.
**5**
Inda ace za’a bani dama a rayuwa ta na chanza abubuwa, bazanyi kasa a gwiwa ba wurin ganin na zabe ka a matsayin mai sarautar zuciya na. kasan irin son da nake maka kuwa? Banta ba tinanin zan so wani da’ namiji kamar yadda nake son k aba.
Karanta Sauran Kalaman So Ga Saurayi Guda 200
Kalaman Soyayya Text Message
Kalaman soyayya ba dole a furta taba. Akan iya tura ta text messages. A wannan shafin, mun jero zafafan Kalaman sace zuciya ta hanyan tura gajerun sakon soyayya SMS. Sakonnin suna ratsa jiki da jijiyoyi.
Cikin Su Akwai na safe, rana, da kuma dare. Akwai kuma zallan zafafan kalaman so masu ratsa zuciya da jiki dan tura wa masoya a SMS.
-----
**1**
Komai zai iya faruwa a wannan duniyar da muke ciki; zasu iya yuwa masu karfafa mana gwiwa ko kuma masu saka mana kasala, amma ina so kisan wani abu guda daya, duk halin da zan shiga ko zaki shiga bazai sa nadai na irin son da nake maki ba.
**2**
Idan aka tambaye ni menene nake tsoron rasawa a rayuwa ta sai nace soyayyar ki da yardar ki. kina da matukar amfani a rayuwa ta kuma babu abunda wani ko wata zasuyi hakan ya sulwan ta.
**3**
A duk sanda ka shiga cikin damuwa, inaso ka tina cewa ina tare da kai kuma babu abunda zai iya raba ni da kai. Ka shiga zuciya ta ka samar mun da farin ciki kamar yadda bantaba tinani ba.
**4**
Yanzu nasan me ake nufi da kalmar “jindadi” ba komai yasa na fahimci hakan ba sai kasancewar ka a rayuwa ta. Nazamo budurwa mai ganin bata da daraja a idon mutune, amma kasa nagane ina da mahimmanci sosai.
**5**
Kasan meyasa nake kasancewa a cikin farin ciki a koda yaushe? Soboda nasan cewa duk halin da zan shiga a wannan duniyar, koda ace kowa zai guje ni, kai zaka tsaya mun kuma na tabbatar bazaka sa nayi kasa a gwiwa ba.
Karanta Sauran Soyayya Text Message Guda 200+
Kalaman Yabon Budurwa
Idan kana neman kalaman soyayya masu kwantar da hankali ta hanyan yabon mace Toh shigo nan. Yan mata nada son a yabe su. Da kalaman yabon budurwa masu dadi, zaka iya ratsa zuciyar su suyi sanyi.
Anan zaka samu kalaman soyayya masu sanyi da kwantar da hankalin budurwan ka ta hanyan yabo.
-----
**1**
Masoyiya ta, samun ki a rayuwa ta kawai babban robone. Kafin haduwa ta dake, na kasance me kokwanto a kan zaki amince dani ko bazaki aminta dani ba, amma gashi cikin sauki nasame ki, gaskiya kina da kyakkyawar zuciya.
**2**
Bazan iya rayuwa babu ke a cikin ta ba. Kinriga kin sa na zama gwarzo, babu abunda nasa a zuciya ta sai kyatata maki. Dan nishadin da nake samu a wurin ki bazai misaltu ba. Ashirye nake namaki duk abinda zai saki farin ciki.
**3**
Tinda nake a wannan rayuwar, babu ya’ mace da ta taba kallon cikin idanuna tace tana sona sai ke. Hakan ya nuna mun cewa ina da amfani acikin zuciyar ki. Gaskiya na yaba da hankalin ki da kuma tinanin ki.
**4**
Wasu lokutan in ina tinanin irin kyawun da allah yayi maki, sai na manta komai; hatta sunana ban iya tinawa, soboda a sanda nake tinanin ki, babu abunda ke da mahimmaci kuma agareni sai ke.
**5**
duk inkina wuri nazo ina jin hakan a zuciya ta, bansan meyasa hakan ke faruwa ba. Amma ina tinanin wani abu guda daya; kinsan meyasa? Soboda zuciya ta taki ce dan haka duk sanda kike wuri ina jin hakan.
Karanta Sauran Kalaman Yabon Budurwa Guda 100
Kalaman Birge Saurayi
Toh ya mata, bamu barki a baya ba. Idan kina neman kalaman birge saurayi dan kwantar da hankali Toh shigo nan. A wannan shafi, mun jero maku kalaman soyayya masu nishadantarwa dan birge saurayi.
Lafazin soyayya da muka jera a nan suna da matukan dadi da ratsa jiki da jijiyoyi.
-----
**1**
ina son ka masoyi na. duk abunda zaka fuskanta a wannan rayuwar ko alkhairi ko sharri ina mai tabbatar ma ina tare da kai. Nidai fatana mukasance tare a wannan duniyar masoya mai abun mamaki.
**2**
Har ila yau ina kara godewa ubagiji da ya hadani da saurayi wanda na dade ina mafarkin samu. Na dade ina rokar ubangiji da ya nuna mun irin wannan rana da zan sami saurayi wanda zai soni irin soyayyar da bazai iya misaltuwa ba kuma nasamu.
**3**
Masoyi na bansan yadda wannan maganar zata maka ba, kila ba mace irina kakeso ka ajiye a matsayin matar ka ba. Amma ina so kasan kaine saurayin da nake so na kare rayuwa na dashi. Ina matukar son ka.
**4**
Zuciyar ka a ciki take da kauna. Mazaje irin ka wahalar samu suke da ita, amma gashi na rabauta da samun sarkin su. Wannan abu ne wanda bazan taba mantawa ba arayuwa ta.
**5**
Sahibi na, na kasance ina cikin damuwa tinda na tashi daga bacci, kuma abu guda daya ne kawai zai iya kaudar da wannan damuwar tawa, ganin fuskar ka. Murmushin ka kawai sau daya, ya ishe ni har tsawon wuni.
Karanta Sauran Kalaman Birge Saurayi Guda 100
Kalaman Barkwanci a Soyayya
Inda dan kalaman ban dariya ka/ka zo nan, Toh ga barayin. A wannan shafin Akwai kalaman so da kauna masu sa dariya. Zaka iya koh ki iya furta su dan nishadantarwa. Kalaman love na ban dariya suna da dadi da sace zuciya cikin sauki.
Ka zaba daga cikin zafafan Lafazin soyayya na love masu nan dariya dan bada dariya. Kalaman so cikin shafin nan suna da dadin gaske.
-----
**1**
Masoyiya ta sarauniyan zuciya ta, nazama namiji mai son naga na chinma burina, daya daga cikin wannan burin dana boye wa zuciya ta itace naga nasaki dariya a koda yaushe, ko da ace ina cikin wani hali.
**2**
Na dauko shayi ina sha da safe, amma duk sugar dana sa mata bai isa ba, sai daga baya na fahimci cewa izinin ka ne ban nema ba kafin nasha shayin. Dafatan kana lafiya. Dan lafiyar ka itace kwanciyar hankali na.
**3**
Masoyiya ta, kinsan meyasa nake jindadin kasancewa tare da ke, soboda duk wani damuwa ta, kina share mun ita da kallo daya kawai. Tinanin ki yakan kaudar mun da yunwa sai naji na koshi ba tare dana ci abinci ba.
**4**
Habibi na, inaso nida kai muyi wani wasa, kuma wannan wasa nada sharda da bazan fada maka ba. Inka karya doka za’a cika tara. Ina so ka kalli cikin idanuna kafada mun irin son da kake mun ba tare da ka kyapta ido ba. Muje zuwa!
**5**
A duk sanda nake baka dariya, zuciya ta sai ta sami sukuni da natsuwa. A sanda kake dariyar, har wani kyau kake yi, amma fa duk da haka nafi ka kyau sosai. Dan kuwa a inda nake, kai mai muni ne.
Karanta Sauran Kalaman Barkwanci a Soyayya Guda 100
Kalaman So Na Barka Da Safiya
A wannan shafin, mun jero maku Kalaman soyayya masu zaki na barka da safiya. Za ku iya tura wa masoyan ku daya daga cikin Wainnan kalaman so masu dadi da ratsa zuciya. Amma ba lalai bane ku tura wainnan Lafazin so ba, zaku iya furta su.
Amma ka daku sake Baku yi amfani da kalaman so da kauna masu ratsa zuciya ga masoya kullun da safiya ba.
-----
**1**
Barka da safiya abar kauna ta, dafatan kintashi cikin koshin lafiya? Sanin yadda kike aduk safiya yazamo alhakin dana daura ma kaina. Duk safiya inna tashi daga bacci kece wacce nake fara kira dan sanin lafiyar ki.
**2**
Dafatan kin wayi gari lafiya, bara nabaki wani labari mai dadi; jiya bayan na kwanta bacci, sai nayi mafarkin nida ke mun wayi gari cikin farin ciki da aminci a matsayin sarki da sarauniyar sa. Shin hakan zai faru a tsakanin mu kuwa?
**3**
Duk daren da banji muryar ki ba, da bacin rai nake tashi da safen dan zuciya ta bata iya jurar rashin ki a cikin ta. Banaso na ringa tashi daga bacci da damuwa a tare dani. Abar kauna ta dafatan kintashi lafiya?
**4**
Akace safiya lokaci ne da mutum ke zama ya shirye abunda zai aiwa tar a wannan ranar, dan haka niban da wani aiki da zan aiwa tar daya wuce nayi tinanin ki, nazo naga murmushin ki, naga kyakkyawar fuskar ki, ni sun ishe ni. Masoyiya ta sai kitashi daga bacci.
**5**
Masoyi na, sahibi na, habibi na, jiya dakai na kwana a zuciya ta kuma gashi na wayi gari da tinanin ka. Kai din na musamman ne. bana tinanin akwai wani da’ namiji da zai iya miye gurbin ka acikin zuciya ta.
Karanta Sauran Kalaman So Na Barka Da Safiya Guda 100
Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci
Bayan an gama zirga zirgan rana, lokaci yayi da za’a kwanta barci. Amma kafin a tafi, fadawa juna kalaman so masu dadi na kwanciya bacci na da kyau sossai.
A wannan shafi, mun jero maku kalaman so masu dadin gaske dan sace zuciyar masoya. Wainnan kalamai ana iya fadar Su ko kuma a tura a matsayin SMS.
-----
**1**
Sama cike yake da taurari duk wani dare. Amma ina so kisan cewa hasken ki a cikin zuciya ta tafi taurari haskawa. Nidai fatana daya; kamar yadda muka rabu lafiya yau, haka nakeso nagan ki gobe cikin koshin lafiya fiye da yadda kike yau. A tashi lafiya sarauniya ta.
**2**
Bayan na dawo yau ina duba nasarar dana samu a yau, sai nagane cewa babban nasarar aciki itace ganin ki, da kuma jin muryar ki mai dadin ji a kunni, masu warkar da duk wani damuwa ta. Atashi lafiya masoyiya.
**3**
Masoyiya ta, inaso na kwanta bacci yanzu, dan haka inaso kema ki kwanta dan mu hadu a mafarki mucigaba daga inda muka tsaya. Zuciya ta bazata iya jurar kewar ki ba. Inason ki.
**4**
Babban farin cikina da kwanciyar hankali na duk inna je kwanciya shine “ina da budurwa wacce ta san sirrin sanya farin ciki a zuciyar masoyin ta. Sai mun hadu da safe masoyiya.
**5**
Yanzu kina gidan ku nima ina gidan mu. Bamu tare amma gani nake kamar gaki nan agaba na ina ganin ki. Inaso kisan cewa ina tare da ke. Ki kula mun da kanki sahiba ta. A wannan daren inaso kiyi bacci cikin salama.
Karanta Sauran Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci Guda 100
Kalaman Soyayya a Waya
Yanzu da dadi ya koma a waya, Kalaman soyayya ma am koma yi sa a waya. Idan kuna neman kalaman so da kauna masu ratsa zuciya dan fadawa masoya a waya, to ga sashin ku nan.
Mun jero maku zafafan kalaman so masu dadi da kwantar da hankali dan nishadantarwar ku. Ku furta masu wainnan lafazin so dan nuna kaunar ku garesu.
-----
**1**
Masoyi na, bara na fada maka wata gaskiya; nasan kana tinanin kaine kace kana so na, amma bahaka bane. Daga ranar da na fara ganin ka na kamu da sonka, nayi tinanin nazo na sameka amma sai gashi faduwa tazo daidai da zama. Amma wannan abun yayi mun gaskiya kam.
**2**
A duk sanda na kalli fuskar ki na fahimci kina satar kallo na, sai naga kin kara kyau, ina rokon ki kicigaba da hakan. Hakanma nasani farin ciki sosai. Kinsan irin son da nake maki kuwa?
**3**
Tinda nafara ganin ka na daina shiga damuwa, tinda nafara jin muryar ka nadaina shiga bakin ciki, babu abunda nake yanzu sai nishadi da annashuwa, kuma kaine musabbabin hakan.
**4**
Duk in kika kira waya na ban dauka ba, abun na matukar sani cikin damuwa, dan banso naga kina wahala soboda ni, muryar ki kawai nada gurbi wurin nishadantar dani. Dan haka keta daban ce hubbi na.
**5**
Bazan iya banbance me nafi so gane dake ba, zai iya zama muryar ki ko kuma kyawun ki, amma inmun hadu sai na tabbatar da hakan tinda zuciya ta bataso nayi son kai. Dan haka inmun hadu sai na tantance tsakanin su dan share kokwanto na.
Karanta Sauran Kalaman Soyayya a Waya Guda 100
Kalaman Bada Hakuri a Soyayya
Idan kuka ba masoya fushi, bada hakuri ya zama dole. A wannan shafin, mun jero maku, kalaman bada hakuri a Soyayya guda dari (100) a soyayya.
A soyayya na Hausa ka san ba’a fara bada hakuri da kalaman soyayya. Ka san yadda zakayi kafin ka fara amfani dasu.
-----
**1**
Masoyiya ta! Ina so na roki wata alfarma guda daya wurin ki, ina mai rokon ki kimanta da abunda ya faru a tsakanin mu, zuciya ta ta kasa hakura dake, nayi tinanin zan iya zama ba da tinanin ki ba amma hakan bazai yu ba. Zuciya ta tana kewar ki.
**2**
Haryanzu nakasa yarda cewa nina saka ki a wannan hali da kike ciki. Dan allah, kidawo gare ni masoyiya ta, munsamu sabani a tsakanin mu amma ba hakan zai zamo sanadiyar rabuwar mu ba.
**3**
Kamar yadda ake fada cewa babu wanda baya kuskure a wannan rayuwan, nayi kuskure kuma na karbi laifi na nabaki kunya danayi. Amma ina mai maki alkawarin cewa zan zama irin wannan namijin wanda kike mafarkin shi a zuciyar ki.
**4**
Na kasance wulakanta ka ce kawai abunda nakeyi a baya, bansan meyasa nayi ma hakan ba. Amma yanzu nadawo cikin hankali na kuma rayuwa ta koyamun darasin da bazan taba mantawa ba. Dan allah kadawo gare ni masoyi na.
**5**
Gaskiya nasan bai kamata nayi miki duk abunda nayi maki ba. Hakan yasaka ni cikin damuwa wuce yadda nayi tsammani. Abun da na dauka wasa yafara samun tasiri a kaina. Ina bukatar ki a rayuwa ta. Ina matukar kewar ki sosai.
Karanta Sauran Kalaman Bada Hakuri a Soyayya Guda 100
Fitattun Kalaman Soyayya Masu Dadi
**1**
Duk sanda na zauna ni kadai ina tinanin yadda rayuwar mu zata kasance nan gaba, hakan babu abunda zai bani face kwanciyar hankali da natsuwa. Zuciya ta akullin kasancewa take cikin farin ciki.
**2**
Duk wani damuwa ko ciwo da zan shiga bazai tayar mun da hankali ba don kuwa maganin ta na tare da mai sani farin ciki. Daga ranar da muka hada ido hudu nasan cewa wannan zuciyar wurin zama na ne kuma gashi hakan ya zamo zahiri.
**3**
Irin wannan soyayyar tamu dame zamu kira ta? Gaskiya najima banga irin wannan soyayyar tamu ba. Kullin babu abunda muke tinani sai dai cinma burin mu da nasarar junan mu tare. Duk abunda zai sa wannan farin cikin ya cigaba da kasancewa a tsakaninmu, na dauki alkawarin hakan.
**4**
Aduk sanda aka samu masoya irin mu masu son junar su kamar yadda suke son rayuwar su, nasara, kwanciyar hankali, jindadi, nishadi, muradin zama tare da kuma cin ma buri kadai ne abun da ake fuskanta. Kuma soyayyar nan tamu sai tazamo abun misaltawa.
**5**
Nagode da kasancewa cikin rayuwa ta a sanda kowa ya guje ni. Nagode da sani cikin farin ciki a sanda nake cikin bakin ciki, ina kara godewa da sani dariya a sanda nakeso nayi kuka. Nagode da samar ma rayuwa ta ma’ana a sanda nayi tinanin na rasa komai.
**6**
Tinda muka hadu na dai na shiga cikin damuwa, na dai na shiga bakin ciki, na dai na abubuwan da basu dace ba. Kuma nafara kasancewa cikin nishadi, annashuwa. Irin wannan zuciyar abun muradin kowani masoyi ne.
**7**
Duk wani tarayya, duk wani murmushi, duk wani kallo, duk wani fita, duk wani zance, duk wani sako, duk wani zama da mukayi ya kara sanya so a cikin zuciya ta wuce yadda nayi tinani. Rabuwa da juna ba tamu bace.
**8**
Nayi tinanin bazan iya yi ma soyayya hidima ba, amma kuma haduwar mu tasa yanzu babu abunda bazan iya ba soboda so, matukar hakan zai sa farin ciki da nishadi yayi tasiri.
**9**
Kafin mu hadu, rayuwa ta ta kasance irin rayuwar da bana so na tina irin ta. Amma haduwa rmu tasa na manta wannan duk abaya na. Gaskiya nayi dace sosai.
**10**
Tunda muka hadu na daina shiga cikin damuwa. Akullin ya kasance ina kasancewa ne cikin nishadi da muradin ganin wacce ke sani farin ciki. Irin wannan farin cikin na bukatan babban kyauta, kuma na dauki alkawarin yin wannan kyautan.
masoya
ReplyDeleteThank you oga love you too
DeleteMasha allah
DeleteGdya looodi looodi
Godiya so ba iyaka
ReplyDeleteAhmad
ReplyDeleteThank you so much sir this is very good article
ReplyDeleteI Am Krishna
Allhmmdllh
ReplyDeleteGodiya ta musamman, Allah ya qasa basira
ReplyDeleteA very good word
ReplyDeleteA very good word
ReplyDeleteAllah yakara basira sosai🙏💯❤️
ReplyDeleteAllah yabiya mina godiya
DeleteMasha. Allah. Allah. Kara bashira
ReplyDeleteAllah yakara basira
ReplyDeleteTnx
ReplyDeleteMasha Allah Allah ya karo basira
ReplyDeleteMasha allaah
ReplyDeleteGsky sunyi Allh yaqara basira
ReplyDeleteVery good
ReplyDeleteMasha allaah
ReplyDeleteHhhh wlh sai naji kamar wasan Yara Babu Kalma Daya Mai ratsa jiki ko zuciya
ReplyDeleteWlh😂😂
Delete👌👌👌
ReplyDeleteMasha Allah godiya mukeyi Allah yasaka da alkhairi
ReplyDeleteMuna godiya sosai Allah yakara basira
ReplyDeleteFirdausi
ReplyDeleteAbdulrazak
ReplyDeleteGodiya sosae
ReplyDeleteThank you so much
ReplyDeleteMasha Allah allah yakara basira Amma Dan Allah kuma na application mana ko PDF
ReplyDeleteAllah yakara basira
ReplyDeleteMasha Allah allh yaqara basira
ReplyDelete