Menene So: Alamomin So Na Gaskiya (Saurayi da Budurwa)
Nuna alamar soyayya a wasu lokutan yana da matuƙar wahala a tsakanin maza da mata. Zaka ga mace na son namiji, amma duk alamar da ta nuna masa dan yagane tana son shi, amma kuma wasu na daukan hakan wasa. Hakan ma ke faruwa a tsakanin maza. Wasu halayen da zaka ga wasu matan ko maza na nuna wa hakan na nufin wani abu a tsakani. Domin sanin mene so na gaske da kuma tare da hanyar da ake ganeta cikin sauki, cigaba da karanta wannan rubutun dan wasu kuwa basu iya banbanta tsakanin so da kaina. In hakan na ma wahala, wannan rubutun takuce!! Menene So? Abunda ake nufi da kalmar so ita ce haɗin motsin rai, ɗabi'a, da imani masu alaƙa da ƙaƙƙarfan ji na ƙauna, karewa, zafi, da mutunta wani mutum. So wani abu ne da ke faruwa tsakanin mutane biyu kuma yana girma cikin lokaci ƙanƙanuwa ta hanyar sanin shi ko ita da fuskantar matsaloli masu yawa na rayuwa tare. An yi ta muhawara mai yawa game da ko soyayya zabi ce, abu ne mai dawwama ko mai wucewa, da kuma shin soyayyar da ke tsak