Top 10 Littattafan Hausa Novel Complete Sites
Shin kina neman littattafan hausa novel complete kamar su jarababben namiji, gidan uncle, tayi mun kankanta, da matar hariji ko kuma makancin haka na romantic hausa novels complete? Toh mun san inda zaki same su cikin sauki ba tare da bata lokaci ba. Indai harkar hausa novel ne, toh akwai websites da yawa wanda ake yi su dan saka maku labaran soyayya masu dadi da ratsa jiki. A wannan shafin, zamu jera maku websites din da zaku sami littattafen hausa ku karantasu cikin sauki ba tare da kun kashe kudi ba. Wattpad Hausa Novels Wattpad shafi ne akan yanan gizo da ake daura novels. Dadin abun shine akwai litattafan da wasu marubutan Hausawa suka rubuta dan nishadantarwarku. Yawancin littattafen dake Wattpad tsofaffin novels ne. Akwai marubuta da yawa akan wannan website din. Amma akwa gida biyu da suka shahara indai wajen rubuta romantic novels ne. Cikin su akwai Real_ahmerd da kuma Aisha Nana. Daga cikin novels din Real_Ahmerd akwai Zan so ka a haka , Qalbina (Kece zaki fidda n...