Jerin Sunayen Shugabannin Najeriya
Najeriya ta kasance babbar ƙasa ce a afrika. Tafi ko wace ƙasa a afrika yawan mutane da kuma tattalin arziki na ƙasa. Mafi akasari ma idan kana neman wajen yin kasuwanci a faɗin afrika, toh najeriya ta zarce sauran. Yin shugabanci a najeriya abu ne da kamar wuya saboda babbanci da kuma yawan yarirrika da har ma al'adu da ake da su a ƙasar.
A shekaru da yawa da suka gabata, an sami shugabanni da suka jagoranci najeriya. Waɗannan shugabanni sun jajirce wajen ganin cewa sun bawa najeriya shugabancin da ya kamata. A wannan rubutu, zamu jero muku sunayen shugabannin najeriya. Duk da cewa wasu daga cikin su sun mutu, wasu kuma suna nan a raye.
Ire - Iren Shugabancin Najeriya
Najeriya bayan samun ƴan cin ta a shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da sintin (1960), Ta fuskarci yanayi na mulki daban daban. Bayan tafiyar turawan da suka jagoranci najeriya a lokacin mulkin mallaka, ya rage ga mutanen ƙasar su san yarda zasu mulki kansu. A wannan lokacin ne, a sanadiyar yanci, ƴan najeria suka fara mulkan kansu ba tare da takuran turawa ba.
Farkon irin shugabancin da ƙasar ta fara samu bayan ƴanci shine mulkin soja. A wannan lokacin, manyan sojoji na ƙasar suka ɗaura daga inda turawa suka tsaya. Sojojin sunyi mulki zuwa na wani shekaru sai kuma mulkin farar hula ya bayyana; wato ɗan ƙasa wanda ba soja ba ya zama shugaban ƙasa. Har ila yau dai a mulkin farar hular ake. Ƙasar tana canza shugaban ƙasa ne a duk shekara huɗu ta hanƴar zaɓe; da dokan cewa mutum zai iya shekara takwas a kan mulki idan har aka kara zaɓen sa karo na biyu.
Sunayen Shugabannin mulkin mallaka
Queen Elizabeth II: Ta Shugabanci Najeriya na tsawon shekaru uku bayan samun ƴanci. (1960 - 1963)
Sunayen Shugabannin Mulkin Soja
Nnamdi Azikiwie (1963 - 1966)
General Johnson Aguiyi-Ironsi (1966 -1966)
General Yakubu Gowon (1966 - 1975)
General Murtala Mohammed (1975 -1976)
General Obasanjo Olusegun (1976 - 1979)
General Muhammadu Buhari (1983 -1985)
President Shehu Shagari (1979 -1983)
General Ibrahim Babangida (1985 -1993)
Ernest Shonekan (1993 - 1993)
General Sani Abacha (1993 - 1998)
General Abdulsalami Abubakar (1998 -1999)
Sunayen Shugabannin Mulkin Farar Hula
Olusegun Obasanjo (1999 - 2007)
Umaru Musa Yar-Adua (2007- 2010)
Goodluck Ebele Jonathan (2010 - 2015)
President Muhammadu Buhari (2015 - 2023)
Asiwaju Bola Ahmed Tunubu ( 2023 - Zuwa yanzu)
Babbancin Ire-Iren Shugabancin Najeriya
Dukkanin waɗannan ire-iren mulki da najeriya ta fuskarta, suna da yanayin shugabanci daban-daban. A yayin da mulkin farar hula take anfani da takardar doka wanda ake kira da constitution, Ita mulkin soja tayi anfani ne da decree.
Ita Shugabancin farar hula ana canza Shugaba ne ta hanyar zaɓe. Wanda ake bada dama ga wadanda suka cancanta su kada ƙuri'u domin zaɓen wanda suke ganin zai iya shugabancin ƙasar. A karshe bayan gudanar da zaɓe, wanda ƙuri'un sa suka fi yawa, shi za'a fitar a matsayin wanda ya lashe zaɓe; kuma shugaban kasar na wannan lokaci har zuwa shekaru huɗu lokacin wata zaɓen.
Ita kuma mulkin soja, ba zaɓe akeyi ba. Mulki ne wanda ake anfani da karfi wajen canza shugaba. Wannan irin mulki tana anfani ne da abun da ake kira da coup; Mutum na kan mulki kawai za'a ce masa ya sauka domin wani ya hau. Idan wanda ke kan mulki a lokacin ya ki sauka kamar yarda aka umarce sa, toh sai a tsige shi da karfi da yaji.
Kammala
Daga karshe, najeriya ta fuskarci shugabanci iri daban- daban. Abun mamaki kuma abun sha'awa a waɗannan shugabannin shine kasancewar su daga harshe daban-daban sakamakon yawan yarirrika da ƙasar take da. Babu shakka waɗannan shugabanni sunyi aiki tuƙuru wajen kawo cigaba wanda ya kawo ƙasar zuwa inda take yanzu.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here