250+ Jerin Sunayen Maza Da Ma’anarsu a Musulunci

 

Zakaga wasu lokutan mutane suna fuskantar kalu bale wajen zabar suna wanda zasu saka wa ya’yen su, kuma hakan ba laifin su bane. Wannan ba matsala bane dan wannan rubutun nawa na dauke da sunayen maza da larabci da ma’anarsu a musulunci har guda 250. Acigaba da karantawa dan neman sani wadannan sunayen.

Sunayen Maza da Larabci Masu Dadi 

Sunaye masu dadi nada tasiri akan maza koda ace baka hadu ba. Zakaga wasu lokutan namiji bai hadu ba, amma duk inda akaji sunan sa sai kaji ana sunan ya dauke shi. Dan sanin sunayen maza masu dadi da kuma na sunayen maza da larabci, acigaba da karanta wannan shahin dan nazo maku da guda 100

  1. Muhammad = sunan annabin rahma

  2. Nuraddeen = hasken addini

  3. Usman (zannurayn) = haske biyu

  4. Ramadan = wata mai albarka

  5. Murtada = murtala 

  6. Isma’il = samaila 

  7. Mudassir = mudassiru

  8. Muzammil = muzammilu

  9. Luqman = luqman

  10. Faruk = mai raba karya da gaskiya

  11. Abubakar = baban budurwa

  12. Saddiq = mai gaskiya

  13. Yasir = sauki

  14. Adam = mutum na farko

  15. Yahaya = rayyaye

  16. Al’ameen = aminci

  17. Sa’id = murna

  18. Zaid = cigaba

  19. Hamza = jarumi

  20. Sani = biyu

  21. Salis = uku

  22. Bello = mataimaki

  23. Junaid = mayaki ko jarumi

  24. Jibril = mala’ikan ubangiji

  25. Mustapha = zababbe

  26. Hassan = kyau

  27. Harith = jarimi ko mai karfi

  28. Hussaini = shugaba

  29. Abdullahi = bawan ubangiji

  30. Abdussami’u = bawan mai ji

  31. Abdurrahman = bawan mai rahma

  32. Abdussalam = bawan mai aminci

  33. Abdussamad = bawan mara karshe

  34. Abdurrazak = bawan mai wadata

  35. Abdurra’uf = bawan mai alheri

  36. Abdulmaliq = bawan mai mulki

  37. Fadeel = falala

  38. Abdulyakeen = bawan mai tabbata

  39. Abduljaleel =  bawan mai izza

  40. Abdussabur = bawan mai hakuri

  41. Rabiu = hudu

  42. Abdulqadir = bawan mai girma

  43. Abdulhafeez = bawan mai kiyaye bayin sa

  44. Abdulkareem = bawan mai tsarki mai daraja

  45. Abdulhadee = bawan na farko

  46. Abdulrahim = bawan mai jin kai

  47. Abdu’laleem = bawan masani

  48. Ansaruddeen  =  hasken addini

  49. Nasir = haske

  50. Auwal = na farko

  51. Yusuf = baiwa

  52. Dawud = masoyi

  53. Ishaq = mai gaskiya

  54. Ziyaulhaqq = hasken mai gaskiya

  55. Idris = annabin allah  masoyin rubutu

  56. Tijjani = ana hadashi da suna ahmad

  57. Ibrahim = annabin Allah (ana kiransa da khaleel)

  58. Khaleel = kyauta daga ubangiji

  59. Mudahir = mai tsarki

  60. Mu’azu = kariya

  61. Kamal = kamala 

  62. Ahmad = Muhammad 

  63. Sharif = mai daraja

  64. Alharun = haruna

  65. Sa’adan = sa’adanu

  66. Mubarak =  albarka

  67. Qaribullah = makusancin allah

  68. Najeebullah = najeebu

  69. Ubaidullah = masoyin ubangiji

  70. Hayatuddeen = rayyayen addini

  71. Shamsu = rana 

  72. Ja’afar = ja’afaru

  73. Sambo = sambo

  74. Bashir = bishara

  75. Nuh =  nuhu (sunan annabin Allah)

  76. Aleeyu = mai baiwa

  77. Musa = musa

  78. Ghalee = ghali

  79. Jabir = jabiru

  80. Sharhabil = sharhabilu

  81. Rislan = rislan

  82. Musbah = misbahu

  83. Dahir = tsarki

  84. Tawwab  = tuba

  85. Mukhtar = zababbe

  86. Nazir = gargadi

  87. Tasiu = tara 

  88. Suleiman = mai son zaman lapiya

  89. Muttaqa = muttaka

  90. Zakariyya = annabi akan kirasu da yau

  91. Salih = nagari

  92. Yunus = rayayye

  93. Shittu = fatar nasara

  94. Ridallah = yardarm ubangiji

  95. Habibullah = masoyin ubangiji

  96. Daha = daha

  97. Shafi’u = mai ceto

  98. bukhari = mawallafi

  99. Anas = farin ciki ko kwanciyar hankali

  100. Mus’ab = jarimi ko mai karfi

Sunayen Yara Maza na Zamani da Ma’anarsu 100

A wannan zamanin da muke ciki ba kamar ta baya bace wanda ake saka ma yara kowane irin suna. Yanzu kam akwai wadanda boye sunayen su sukeyi soboda duk sunayen wancan lokacin ne. Yaro ya taso dan zamani kaji ana kiransa da magaji, rabe, ko ilu, kaga ai dole wasu lokutan ya boye sunan musamman yana wurin yammata. Acigaba da karantawa dan sanin wadannan sunayen na zamani.

  1. Annur  = Haske

  2. Anfal   = sura cikin littafi mai girma

  3. Ansar   = nasir

  4. Affan   = sahabin ma’aiki

  5. Nurain  = haske guda biyu

  6. Anwar  = haske

  7. Ridwan  = kofa a aljanna mai girma

  8. Asur = asuru

  9. Khalil   = ibraheem

  10. Khaleed = khalid

  11. Khaleefa = jagora

  12. Abba  = mahaifi

  13. Rufaid  = rufaidu

  14. Imam    = shugaba

  15. Zayn  = zainu

  16. Mufeed  = mufeedu

  17. Isnad  = sunan wasu hadisai

  18. Akeem = akimu

  19. Jamal = mai karfi

  20. Salman = dangartakan suleiman

  21. Hafeez  = mahaddacin alqur’ni

  22. Adeem  = adeem

  23. Ameer  = shugaba

  24. Abeed   = abeedu

  25. Adeel    = adali

  26. Adnan = makusanci

  27. Afeef  = makarancin littafi mai girma

  28. Ahsan = mai kyau

  29. Ajmal = babba

  30. Aladdeen  = haladu

  31. Aleem = bawan masani

  32. Aqeel  = aqeelu

  33. Tasi’u = tara   

  34. Ashir = goma 

  35. Ayman = imani

  36. Azmii = mai girma

  37. Badrii = badar

  38. Salis = uku

  39. Hamis = biyar

  40. Bilal = ladanin farko

  41. Burhan = burhanu

  42. Deen = addini

  43. Ihsaan = imani

  44. Fadeel  = falala

  45. Auwal = daya

  46. Ihda = daya

  47. Hadi = mai shiriya

  48. Aleem = masani

  49. Gaffar = mai gafara

  50. Ahmad = Muhammad sunan annabin rahama

  51. Rahman = mai rahama

  52. Hateem = hatimi

  53. Haydar  = aleeyu sunan sahabi

  54. Kabir = mai girma

  55. Rahim = mai jin kai

  56. Jawad = jawadu

  57. Munir = mannir

  58. Na’eem = sunan aljanna mai girma

  59. Sabi’u = bakwai

  60. Samin = takwas

  61. Ra’eed = ra’eedu

  62. Sayf  = takobi

  63. Sadeeq = mai gaskiya  

  64. Nuh = annabin Allah

  65. Salah = sallah

  66. Salam = mai aminci

  67. Rayan  = rayyan kofa a aljanna mai girma

  68. Shafee’u = mai ceto

  69. Suhail = suhailu

  70. Aswad = dutse mai daraga

  71. Taheer = dahiru

  72. Tahsin = tahsin

  73. Safwan = safwa

  74. Areef  = masani

  75. Auwal = na farko

  76. Barak = albarka

  77. Nazeer = haske

  78. Monsoor  = Mai nasara

  79. Basheer = bishara

  80. Ma’aruf  = kyawun aiki

  81. Marwan = marwa

  82. Adam =  annabin farko

  83. Noor  = haske

  84. Rafeeq  = rafeequ

  85. Mifta’u = mabudi

  86. Shaheed  = shahada

  87. Suldan   = shugaba

  88. Taj  = Taju

  89. Sadees = shida

  90. Wassem  = wasimu

  91. Zameer   = zamiru

  92. Sayyad   = shugaba

  93. Furqan   = Alqur’ani mai girma

  94. Muhyiddeen = rayayyen addini

  95. Akmal = cikakke

  96. Farhan = farhanu

  97.  Jamsheed = haske tagwaye

  98. Mu’azzam = shugaba

  99. Muzaffar = mai nasara

  100. Umeed = umid

Sunayen Maza da Halayensu

Mutane dayawa wasu lokutan suna da yawan kwokwanto akan halayen mazajen dake tare dasu. Dan sanin halayen maza, wannan shashin rubutun na dauke da sunayen maza guda hamsin 50 da halayen kowa nen su.

  1. Aleeyu

A kan kirasu wasu lokutan da “haidar” Mafi yawancin masu suna aleeyu, zakaga sunada zuciya, karamin abu ke basu haushi amma kuma suna da saukin kai.

  1. Mustapha

Masu suna mustapha zaka gansu shuru shuru kamar basu magana, amma daga sand aka zauna dasu zaka gane cewa suna magana sosai kunya kawai suke da ita.

  1. Umar 

A kan kirasu wasu lokutan da “faruq” a farko daga ganin su, zakaga far’a a fuskar su. Amma kuma suna da saurin fushi ga zuciya. Idan kuma akazo bangaren son mata, masu suna umar saraku na ne a wannan fannin.

  1. Faisal

Mutane dai suna yawan ganin masu suna faisal kamar wanda basu cika fadar gaskiya ba. Amma wasu daga cikin su, idan ka zauna dasu, masu fadar gaskiya ne, kuma suna son mata.

  1. Usman

Idan akazo fannin maza wanda bazaka iya sanin halin su baka zauna dasu ba, toh masu usman ake nufi. Idan ka hadu dasu, kuna fara shakuwa zaka ga bambanci yadda ka sansu abaya da kuma yadda kake ganin su. Akwai son yin abubuwa a boye. Suma sarakuna ne wajen son mata.

  1. Abdul’azeez

Masu wannan suna dai zaka gansu shuru shuru basu magana, amma idan abu ya hada ku zaka sha zagi fiye da yadda baka tabaji ba. Amma kuma akwai wasa da dariya.

  1. Sani

Idan kana neman sarakuna gun shuru shuru kasami masu suna sani, kagama samu, amma idan sukayi wani abun, zaka dade kana tambayar kanka, sune sukayi hakan kodai kana mafarki ne. Kuma suna son mata amma ba sosai ba.

  1. Nazifi 

Idan iya gardama ne musamman siyasa da kwallo, idan kasamu masu suna nazifi kagama samu. Amma daga farko, zaka gansu kamar basu surutu. Ga son mata sosai.

  1. Mukhtar

Mafi yawancin masu suna mukhtar, duk abunda kaga sunyi, toh haka halin su yake babu wata boye boye. Suna da zuciya, suna da far’a. Suna da son mata sosai amma ba kamar masu suna umar ba.

  1. Imran

Iya yen zurfin ciki. Masu suna imrana, matukar basu so kasan wani abu gama dasu ba, duk iya binci ken ka, bazaka taba sanin hakan ba. Suna da far,a amma basu da dadin sha’ani idan aka kure su. Suna da son mata amma bazaka taba sani ba sai kuna tare dasu. 

  1. Mudassir 

A farko idan ka gansu, duk abunda zaka fada a wannan lokacin ka ajiye a zuciyar ka. Bayan kun shaku da juna, sai ka auna kagani akwai banbanci. Masu suna mudassir akwai son mata, far’a, da kuma son zama da mutane.

  1. Mansoor 

Iyayen tonar fada. Karamin abu ke basu haushi kuma basu iya boye fushin su. Suna da son mata. Idan ka tsaya ka duba da kai, duk inda akwai mansoor, zaka fuskar su kamar shuru shuru.

  1. Auwal 

Masu suna auwal zaka gansu da fuskar salihai, amma saraku na ne wajen son mata. Zaka gansu shuru basu son magana. Sai ka zauna dasu zaka son ainihin halin su. Amma kuma suna da dadin zama. Suna ji da kai amman ba sosai ba.

  1. Abdullah 

Basu magana sosai amma kuma idan suka ga mace, jikinsu har rawa yake yi. Suna da dadin zama kuma suna da far’a. Amma suna saurin fushi.

  1. Bello 

Masu suna bello zaka gansu da fuskar salihai. Amma saraku na ne sosai wajen son mata. Idan kana so kana da wacce kake so tana maka jan aji, kasami masu wannan sunan suka ka a hanya. Amma kuna suna da far’a. Matsalar su sun cika karya.

  1. Nuraddeen 

Idan ka fara haduwa dasu haduwar farko, zakace idan ka taba su babu abunda zai faru. Amma sai ka zauna dasu zaka san cewa iyayen surutu ne soboda suna da kunya sosai amma kuma sun son zama da mutane. Suna da fushi amma basu cika nuna ta ba.

  1. Suleiman 

Duk abunda aka fada maka akan masu wannan sunan. Ka yarda dan ayadda kazoo masu, irin halin da zasu nuna maka. Sun iya gardama kamar tare da ita aka haife su. Suna da biye biyen mata sosai.

  1. Abdussalam 

Basu cika son magana sosai ba. Amma kuma ba’a cinsu gardama. Zaka gansu kamar basu magana, amma sun iya magana da surutu sosai. Suna da son mata sosai sai dai kuma mafi yawancin su, nasu baya fitowa fili.

  1. Ameenu 

Musamman idan suka hadu da masu irin sunan su. Basu jin magana. Amma kuma suna da dadin zama kawai dai ra’ayin zuciyar su suke bi. Suna da son mata amma bazaka san hakan ba sai kuna tare da su soboda suna da kunya.

  1. Looqman 

Masu suna looqman suna da far’a da kuma dadin zama. Amma matsalar da suke da ita shine kalon mata. Suna da saurin fushi.

  1. Yusuf 

Masu suna yusuf zaka ga suna da farin jini wurin mata. Mata na son kasancewa dasu. Zaka gansu shuru shuru, amma miskilai ne. Sai ka zauna dasu zaka gane cewa suba wadanda kayi tinani ne ba.

  1. Ibraheem 

Mafi yawancin masu suna ibraheem basu son gardama. Ko me ka fada masu basu gardama akan hakan. Amma kuma da abunda ke zuciyar su suke amfani. suna da far’a da kuma son mata kadan.

  1. Musa

Masu suna musa zaka gansu shuru shuru kamar ka hure amma sunfi yadda kake tinani kuma sai ka zauna dasu zaka san hakan. Suna da dadin zama kuma suna da son mata sosai.

  1. Muhyiddeeen

Haduwar farko, zaka raina su amma dakun fara kasancewa tare dasu, zaka gane cewa suna da dadin zama dan akwai bada dariya sosai. Sun iya bada labara musamman na mata.

  1. Abdulmajeed 

Idan kana neman wanda suka iya saka mutum a kwalba da bakin su, ka sami masu sunan nan. Zaka gansu kamar basu surutu, amma idan suka takura maka, da kanka zaka basu hakuri. Amma kuma suna da dadin zama, ga son shiga cikin mata.

  1. Abubakar

Ana kiransu da “sadiq” duk inda kaga masu wannan sunan, zaka ga suna sun mata fiye da yadda kake tinani duk da dai wasu suna boyewa wasu kuma tasu ta fito fili. Amma kuma suna da dadin zama sosai.

  1. Abdulhakeem 

Iyayen karya. Nidai tunda nake, banriga naga mai wannan sunan wanda  bai tabawa ba koda kadan ne. kuma duk binciken dana danyi Ankara tabbatar mun da hakan. Suna da son mata sosai. Dadin abun shine basu fada ko kadan.

  1. Abdurrahman

Sun iya bada shawara kamar iyaye. Amma idan suka samu wuri basu jin kira. Suna nda son mata, ga zuciya karamin abu ke basu haushi sai dai kuma suna da dadin zama amma basu son raini.

  1. Shareef

Zaka gansu kamar bazasu iya aikata wasu abubuwan ba. Amma sai kuna tare dasu zaka gane cewa abunda fuska ke nuna wa bashi bane a zuciya. Suna da son bata amma baya fitowa fili, suna da dadin zama sai dai suna da takama kadan.

  1. Zakariyya 

Biye biyen mata afili, sai masu wannan sunan. Duk inda kaga mai wannan sunan zaka gane cewa su basu boye boye, komai nasu afili sukeyin sa. Sai dai kadan daga ciki ne ke boye nasu. 

  1. Ma’aruf 

Akwai su da kallon mata da  iya sarrafa mutane da bakin su. Amma kuma matsalar kadan daga cikin su itace basu da cika alkawari. Amma kuma suna da dadin zama.

  1. Ya’akub

Masu wannan sunan suna da son mata, karamin ne ke basu haushi kuma idan gaba ta hada ku sai ahankali. Suna son zama cikin mutane akoda yaushe. Basu da saukin sha’ani.

  1. Ismail

Masu suna ismail mutane ne wanda duk iya dadin bakin da zaka masu, bazaka iya juya masu tinani ba. Suna da matukar kaida amma kuma suna da dadin sha’ani. Suna biyeyen mata amma ba kamar su sadiq da faruq ba.

  1. Ishaq 

Masu suna ishaq mutane ne da basu iya boye abunda ke zuciyarsu. Alokacin da kayi masu abunda basu ji dadi ba, atake anan zasu gayamaka magana. Suna son mata amma ba sosai ba kuma komai nasu basu cika yin a boye ba.

  1. Sa’idu

Indai rike mutum aciki ne da yade yade kasame su kagama. Duk abunda ya shafe su kuma kaji shuru kamar ba’ayi ba. Ga son mata kamar soboda mata akayi su. Son matansu yayi daidai dana su umar sai dai nasu aboye yake.

  1. Mika’il

Idan ana maganr son baza da kuma gardama, sun hada duka biyu sunbar ma kansu. Suna da rigima, taurin kai, jayayya, wahalar shawo kansu. Idan kuma aka dawo fannin mata kuma ba’a magana dan sun wuce tinanin.

  1. Idris 

Iyayen shuru shuru kenan amma fa idan aka kure ba’a jindadi soboda sun iya zagi kamar mata. Basu cika shiga cikiin mat aba soboda kunyar da suke da ita. amma abun mamakin shine idan suka samu wuri, basu zubar da daman su.

  1. Jabir 

Masu suna jabir suna da jiji da kai ga takama. Amma kuma daga sanda kayi nasarar gane kansu, zaka iya juya su yadda kake so. Amma fa da matukkar wahala. Sun iya biye biyen mata.

  1. Shu’aibu

Mafi yawancin su, duk abunda suka gayaamaka ka yarda kawai gaskiyar kenan. Suna da gaskiya aba kinsu. Amma kuma suna zuciya sosai ga iya zagi.

  1. Shamsuddeen 

Zaka gansu kamar idan kasaka hannu a idanun su bazasu ce maka kaomai ba aqmma sai ka gwada zaka gane banbanci.suna da biye biyen mata amma kuma duk aboye suke hakan. Amma kuma masu mutuncin suna da dadin sha’ani sai dai kuma fankama dasu keyi.

  1. Ghalee

Duk inda kaga masu wannan sunan zaka samesu da gaskiya abakinsu. Suna da dadin zama ga kuma far’a. Amma inda ka ketare iya kar ka, zakayi nadamar hakan. Suma suna da son mata amma ba sosai ba.

  1. Yahuza

Masu suna yahuza zaka gansu suna da gardama da iya surutu. Zasu iya kwana cikakke suna gardama musamman na siyasa. Afannin mata kuma su sarakuna ne amma kuma suna da saukin sha’ani.

  1. Mudahir

Masu wannan sunan sarakunan gardama ne. duk iya bakin da kake da ita, sai dai kayi ka barsu soboda nan suka fi kwarewa. Suna da son mata kuma son nasu a fili yake.

  1. Jibril

Biye biyen mata amma duk aboye. Zaka zauna kana yin zaka ga kamar babu wanda ke ganin ka, idan akwai mai wannan sunan, komai akan idonsa kayi. Suna da zuciya amma ba sosai ba.

  1. Harun

Masu suna haruna zaka gansu da fuskar salihai shuru shuru basu magana amma daga sand aka zarce iya yar ka, zakayi mamakin hukuncin su. Suna da son mata kuma zasu iya yin komai soboda mace.

  1. Najeeb

Suna da gardama da jayayya amma bazaka sani sai kun shaku dasu tukunna. Suma suna bin mata amma ba sosai ba. Wasu daga cikinsu nada karfin zuciya.

  1. Yasir

Iyayen shuru shuru amma sai gardamar tsiya. Zaka gansu da fuskar malamai amma abunda sukeyi sai ahankali. Suna da son mata amma kuma suna da kunyar mata sosai.

  1. Shafiu

Masu wannan sunan zaka gansu shiru shiru babu ruwansu. Suna da dadin zama da iya bada shawara. Amma kuma wasu daga cikinsu idan suka bin mata agaba, babu mai yi kamar tasu.

  1. Nafiu

Halin su daya shafiu saidai kuma masu suna nafiu basu daukan raini amma kuma zasuyi wasa da dariya da kowa.

  1. Gaddafi

idan kaji ana kodame kazoo anfika, to su gaddafi ake magana. Suna da son mata, ga iya gardama dana kwallo dana siyasa. Karamin abu ke basu haushi kuma basu iya rike abu a zuciya. Idan fada ta hadaka dasu sai kayi dana sanin hakan.

Daga Karshe

Nasan yanzu kun san suanyen maza dana zamani da kuma me suke nufi a hausance. Halayen wasu daga cikinsu kun sansu. Idan kanada wani mai daya kaga cikin wannan sunayen da aka lissafo, sai ka san yadda zaku ringa mu’amala da juna.


Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa