Sunayen Mala’iku Guda Goma (10)

 

Ubangiji ya halicci mala’iku daban daban wanda kuma shi kadai yasan adadin mala’ikun sa. Wasu na cikin duniyar nan da muke ciki, wasu na cikin gidan aljanna wasu kuma na cikin gidan wuta da kuma sauran su inda ko kowanne daga cikin su yake yin aikin da Ubangiji ya umur ce su da ita.

Kamar yadda Allahu SWT kadai yasan adadin mala’kun sa, haka zalika shi kadai ne masanin sunayen su. Amma wasu daga cikin wadannan mala’ikun, an ambaci sunayen su a cikin littafi mai girma (Alqur’ani) da kuma hadisi tare da sanar da ayyukan kowanne daga cikin su.

Wannan rubutun nawa na dauke da jerin sunayen mala’iku tare da hidimar da suke yi wa Ubangiji mahalicci don haka, acigaba da karan tawa!!

Mene ake Nufi da Mala’ika?

Mala’ika halitta ne wanda Ubangiji ya halitta don yi masa bauta yayin da kowanne daga cikin su yake hidimar sa ga Ubangiji. An halicci mala’iku kafin halittar mutun da aljan kuma suna yin bautar su ga Allahu SWT. Ubangiji ya halicci mala’iku ne daga haske ba kamar mu yan Adam da aka halicce mu daga kasa ba

Akwai abubuwa dayawa da suka banbanta tsakanin mala’iku da dan Adam. Daga cikin su akwai siffa (siffar jikin su ba irin namu bane), kwazon aiki ba tare da gajiya ba, basu jin yunwa balle suci abinci ko su sha ruwa, basu gajiya balle su huta sa’an nan kuma basu sabon Ubangiji. Kowanne acikin su da aikin dayake yi kuma basu shiga aikin junar su ko kadan.

Jerin Sunayen Mala’iku da Kuma Ayyukan Wasu Daga Cikinsu

Kamar yadda muka fada a baya, mala’iku suna da yawan da Ubangiji kadai yasan iya kan su. Haka zalika sunayen su. Ayyukan mala’iku ya kasu kasha kashi. Akwai masu kula da gidan Aljanna, akwai masu gadin gidan wuta, mai kula da ruwan sama, masu rubuta kyau da sabanin haka, mai daukan rai, mai busa kawo, masu kula da tsirrai da kuma sauran su ba adadi.

Wannan shashin na dauke da sunayen wasu daga cikin mala’iku da kuma ayyukan da suke yi wa Ubangiji mahalicci.

  1. Jibril

Mala’ika Jibril shine mala’ika wanda ke saukar da wahayi daga wajen Allah SWT daga sama zuwa ga Annabin rahma Muhammad (SAW). Shine mala’ikan da Allah ya aiko da Qura’an mai girma zuwa ga mutane ta hanyar wahayi. Duk wani mala’ika yana kasan mala’ika Jibrilu ne. Allah ya anbace wannan mala’ikan a wurare uku cikin Qur’ani mai girma. An anbace shi da “Ruhul-Amin, Ruhul-Qudus, Ruhul-Karim”

  1. Israfil

Mala’ika Israfil yana daya daga cikin mala’iku na musamman a wurin Allah SWT. Mala’ika Israfil shine mala’ikan da ubangiji zai umurta ya busa kaho ranar tashin Al kiyama. A wannan rana Allah zai umurce shi ya busa wannan kahon, yana nan yana jiran wannan umarnin daga wurin Ubangijin sa. A ranar tashin Al kiyama sau biyu (2) zai busa kaho.

  1. Nakir da Munkar

Mala’ika Nakir da Munkar duk wani mutum mai rai a duniya zai hadu dasu kuma duk wani mamaci ya riga ya hadu da mala’ikun na su biyu. Tare sukeyi yin aikin su. 

Su ne mala’ikun da Allah SWT ya umurta su tambayi mamaci bayan an saka su a kabari. Irin amsar da kabasu zai tabbatar da yadda zasu kula da kai. Idan ka amsa da kyau zasuyi maka maraba da zuwa idan kuma sabanin hakan ta faru, zasu wa wannan mamacin azaba.

Tambayar da sukeyi wa mamaci shine; wanene Ubangijin ka? Wanene Annabin ka? Mene ne takardar ka? da sauransu. (muna rokon Allah yabamu ikon amsawa) 

  1. Maalik

Mala’ika Malik shine mala’ikan da babu wani dan Adam mai marmarin ganin sa dan kuwa ganin sa bala’i ne. Wannan mala’ikan bai bata murmushi, dariya ko far’a ba. Babu wani jindadi a inda yake sai dai azaba haka zalika ganinsa kawai tashin hankali ne

 Shine mala’ikan da Ubangiji ya wakilta yayi gadin gidan wuta tare da wasu mala’ikun da Ubangiji yayi masu lakabi da “zabaniyawa”(sunan da ake kiran masu azaba agidan wuta) tsakanin su da yan wuta babu mutunci sai dai tsantar azaba mai tsanani (Allah yayi mana tsari daga haduwa dashi da mutanen sa). 

  1. Mika’il

Mala’ika Mika’il shine wanda Ubangiji ya wakilta ya samar wa duniya baki daya da ruwan sama isasshe. Kuma aikin shi ba iya akan dan Adam kadai bane, aikin sa ya shafi duk halittun duniya ne baki daya. Kuma aduk sanda ake zafi sosai, aikin shi ne ya rage radadin zafin. Samar da walwala ga halittun duniya aikin sa ne. Duk ruwan saman da ake yi mana, shine mala’ikan da Allah ya umurta da saukar mana da ruwa.

  1. Izra’il

Acikin mala’iku baki daya, babu mala’ikan da aka fi sanin sunan shi kamar mala’ika izra’il. Kowa na tsoron haduwa dashi soboda babu wanda yasan awata siffa zaizo masa. Mala’ika izra’il shine wanda Allah SWT ya wakilta dan karbar rai daga duk wani halitta mai rai a doron kasa. A yau hatta kana nan yara sun san sunan wannan mala’ikan mai bautar Mahaliccin sa. 

Duk mai rai alokacin da zai bar duniya, sai yayi ido hudu da wannnan mala’ika. Ayyukan mu a duniya zai tabbatar da yadda zai zo mana. Cire rai alokacin mutuwa shine aikin sa kuma kullin, a wurare daban daban, lokaci daya yana cire rai tare da masu taimaka masa batare da makara na dai dai da sa’a daya ba.

  1. Kiraman Katibin

Wadannan mala’ikun sune ke rubuta duk aikin da bawa ke aikata wa a doron kasa walau mai kyau da kuma mara kyau. Sunan su Raqib da Atid. Babu wani aiki da bawa zai aikata ko furuci da basu rubuta ba. Duk wani aiki da ka riga kayi daga ranar da aka haife ka haryanzu, duk sun rubuta su baki daya.

Na farko shine Raqib shine mala’ikan da ke rubuta duk wani aikin da bawa ke aikata wa a duniya kuma shine mala’ikan dake zaune a damar mutum. Shikuma na biyun shine Atid, shikuma aikin sa shine rubuta duk wani aiki na alfasha mara kyau. Yana zaune ne a hagun bawa. Dukkan su biyun suna rubuta ayyukan bayi alokaci guda awurare daban daban.


  1. Ridwan

Wannan yana daya daga cikin mala’ikun da kowa yake so ya gani ya idanun sa. Mafarkin duk wani halitta kenan. Kuma duk wani dan Aljanna zai ganshi. Shine mala’ikan da Allah ya wakilta dan yin gadin gidan Aljanna. 

Duk wanda ke son haduwa da wannan mala’kan, sai yayi aiki na gari dan ganin sa. Yana daya daga cikin mala’iku na musamman a wurin ubangiji.

Karin Bayani 

Idan kun lura abaya nafadi cewa Allah ya halicce mala’iku wanda shi kadai yasan adadin su, don haka sanin sunayen su duka ba abune mai yuwa. Sai dai  fadar sunayen  wasu daga cikin su da kuma ayyukan su. 

Wannan rubutun  ya kunshi sunayen mala’iku goma (10) amma kuma ko kwatankwacin su ban lissafo ba. Hatta duniyar da muke ciki, mala’iku ke rike da ita kuma duk suna aikin su ba tare da kuskure ba.

Daga Karshe 

Bayan karanta wannan rubutu nawa nasan kun samu amsar da kuke nema akan sunayen mala’iku duk da dai ba duka aka samu ba. Amma kuma wasu daga cikin wadanda yakamata a sansu na dauke a wannan rubutun. 


Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa