200+ Sunayen Larabawa Masu Dadi (Mata da Maza)
Nasan kuwa akwai lokutan da zaka ga mutane na sha’awan saka wa yaransu sunan larabawa, dan kuwa idan ana maganar sunaye masu dadin ji, sunayen larabawa sunfi amsa wannan tambayar. Dan sanin sunayen larabawa masu dadi na maza da kuma na mata, ku cigaba da karantawa dan samun amsar tambayar ku.
Sunayen Larabawa na Mata Masu Dadi
Sunayen mata na labarawa suna dadin ji a kunnuwa kuma gasu da dadin fada abaki. Wani abun farin cikin anan shine, ba dole sai kana jin labarci ne zaka iya furta sunayen ba. Furta sunayen nada sauki har awurin wadanda basu jin larabci. Wannan shashin na dauke da sunayen mata na larabawa.
Aya = ayar alkur’ani mai girma
Dania = kusa (kamar kusa da abu)
Fatima = yarinyar annabin rahma
Huda = shiriya
Jannah = aljanna
Lina = kamar bishiyar dabino
Maryam = uwar annabi isah
Nuha = basira
Safa = tsarki
Salwa = wacce ke saka farin ciki
Abida = mai son bauta
Abeer = kamshi
Alima = masaniyar ilimi
Alina = mace mai zuciya sassauka
Amana = imani
Amani = kyakkyawar zato
Ahmina = tsararriya
Anisa = mace mai farin jini da mutunci
Aniya = kulawa, nuna soyayya
Asma = sararin samaniya
Aidah = mai zuwa gaida mara lafiya
Aqeela = kwarewa
Azza = yar barewa
Banan = bakin yatsa
Batoul = sunan yar annabin rahma
Bayan = mai iya bada bayani
Benazir = mace ta daban
Budaira = sabon wata
Bushra = labari mai dadi
Dariya = kyakkyawar dabi’a
Dalila = shiriya
Dimah = ruwan sama babu tsawa
Doreen = tauraruwa
Dunya = duniya
Fadwa = sadaukarwa
Farah = farin ciki
Ghazal = soyayya
Hadiya = mace mai shiryar da mutane ga hanyar shiriya
Hafiza = mai tsarewa
Hanifa = mace wacce ta yarda da kadaicin Allah
Hamida = godiya
Heba = kyauta
Huriyya = ma’abotan zama
Haya = wacce ake koyi da ita
Iba = mace ta kwarai
Ibtisam = murmushi
Ilham = kwarin gwiwa
Izza = kwazo
Iman = imani
Inaya = taimako
Izdihar = cinma buri
Jamila = kyakkyawa
Kamila = kwararriya
Kanza = dukiya
Katiba = mace mai rubutu
Khalida = har abadan (kamar zaman a wuri har abada)
Khaliya = kadaici
Lana = shiru shiru
Leen = mai tasowa
Lina = ichen dabino karama
Laila = night
Mahdia = wacce ubangiji ya kiyaye
Maira = mace mai kawo abinci
Maiza = mace mai banbance tsakanin abu mai kyau da mara kyau
Manari = kwararriya
Marwa = dutse ne inda hajar ta tsaya yayin da take neman ma danta ruwa
Marzia = mace mai nuna godiya ga ubangiji komin kankan cin abinda yayi mata
Matira = wurin dake wuyan samun ruwan sama
Mazna = mace wacce fuskarta keda ban sha’awa
Medina = kyakkyawar burni a makkah
Minna = kyauta
Mona = nuna so ga abu
Munya = fata
Naima = alheri
Nada = alheri
Najida = taimako
Najma = tauraruwa
Narina = fure mai daukar ido
Nawal = babbar kyauta
Nazira = kyau mai daukar fuska
Omaima = nuna soyyaya kamar irin ta uwa ga danta
Radwa = wani tsauni a garin madina
Rahila = mai tafiya
Ranya = mai nasara
Rayan = daya daga cikin kokofin aljanna mai girma
Safa = tsarki
Saba = iska mara karfi
Sahira = wacce bata bacci daddare
Salwa = wacce ke saka mutane farin ciki
Samara = wacce ke magana a sanda taurari ke haskawwa daddare
Sana = mace mai haskakawa
Sarah = matar annabi isma’il
Tamira = mai saida dabino
Tasnim = mahurar ruwan aljanna
Yusra = sauki
Zaina = kyawu
Zahra = fure
Sadaf = bakin teku
Nuha = basira
Najwa = mai tattaunawa ta kusa
Sunayen Labarawa na Maza Masu Dadi
Kamar yadda mata suke da nasu sunan na labarawa, haka zalika maza suna da nasu masu daukan hankali. Wasu sunayen mazan yafi na wasu matan dadin ji. Ga saukin fada a baki, ga dadin ji. Domin sanin wadannan sunayen mazan masu dadi, sai acigaba da karanta wannan shashin me dauke da sunayen maza da larabci.
Hasan = abu mai kyau
Abbas = zaki
Murad = muradi akan abu
Nour = haske
Amin = mai gaskiya
muhammed = sunan ubangijin rahama
Rashad = shiriya
Tareq = kwanan wata
Wahid = daya
Abid =mai bauta
Adam = mutum na farko a duniya
Adil = adali
Adnan = makusanci
Afif = gwarzo
Ahsan = mai kyau
Amir = shugaba
Ajmal = kyakkyawar namiji
Ali = babba
Alim = masani
Anwar = haske
Aqeel = mai baiwa
Amir = dan sarki
Ahmad = sunan annabin rahma
Ayman = mai kyakkyawar hali
Aziz = mafi kusanci
Badr = cikkaken wata
Bassam = wanda ke yawan murmushi
Basil = mai zuciya
Bakr = mai zuciyar yin abu
Bashir = bishara
Bilal = sunan daya daga cikin sahabban annabin rahma
Daleel = shugaba
Deen = addini
Iliyas = annabin Allah
Fadi = wanda ke sadaukar da rai dan jindadin wasu
Faheem = ganewa
Faiz = wanzuwa
Fathi = wanda ke shiryar da wasu
Fikri = tinani
Ghayth = ruwan sama
Habib = masoyi
Ghazi = jarumi
Hanin = mai nuna so
Haris = manomi
Hatem = wanda ke kawo karshe ga kokwanto
Hisham = alheri
Hashem = mai wargaza abu mara kyau
Hussein = mai kyau
Idris = mai fassara
Ihsan = mutunci
Imad = ginshiki
Iqbal = dacewa
Isah = annabin Allah
Jibril = mala’ikan ubangiji
Jamal = kyau
Jawad = alheri
Jameel = mai kyau
Jihad = aiki tukuru
Junaid = karamin jarimi
Kanz = wadata
Karam = mai budadden hannu
Katib = mai rubutu
Kazim = wanda ke iya rike fushi bai nuna ba
Khalil = aboki mai kusanci
Khali = kadaitacce
Kumail = cikkake
Lateef = mai saukin kai
Mahdi = wanda ubangiji ya kiyaye
Majd = babbar kyauta
Marzi = abunda aka yarda dashi
Mazin = taruwar hadari
Mansour = mai share hawaye
Milad = ranar haihuwa
Mujib = burgewa
Moumin = mumini
Muhsin = mai aikata aiki mai kyau
Muntazir = jira
Naeem = wadata
Naji = rayayye
Nawwar = haske
Nazir = gargadi
Nuh = sunan annabin Allah
Nouman = dan uwa najini
Omar = sunan sahabin annabin rahama
Naseer = mai taimako
Qasim = wanda ke rabo
Ramzi = alamar abu
Raed = shugaba
Rasheed = mai shiriya
Rayhan = kamsi mai dadi
Rayyan = wanda be jin kishi
salaam = zaman lafiya
Saad = farin ciki
Sabri = hakuri
Sami = jagaba
Subhi = sallar farko ta safiya
Wael = mai neman taimakon ubangiji
Zayn = ado
Yusuf = annabin ubangiji
waleed = yaro
Gabatarwa
Wani abun alfahari da sunayen larabawa shine, zaka ga masu sunayen suna da yawa, kuma zaka ga duk inda masu sunan suke, gane su bai wahala.Yana da matukar amfani yazamo duk musulmi sunan yaransa su zamo sunayen larabawa masu dadi ga yara maza da kuma mata.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here