200+ Sunayen Jarirai Masu Daɗi ( Maza da Mata)

 

Sunayen jarirai wato sunaye ne da ake sa wa yara jarirai bayan an haifo su duniya. Wasu sukan bayar da wannan suna tun kafin ma bikin sa ainufin sunan. Jarirai ba'a haifo su da suna; sai bayan an haifi jariri ne ake sanya masa suna. Wasu iyaye musamman ma iyaye mata, suna son su fara kiran jaririn su da suna atake bayan haihuwar sa.

Sunayen Jarirai Na Mata Masu Daɗi

Mata aka ce ' Adon gari.'. Babu shakka da akwai sunayen jarirai da yawa da za'a  iya ba wa jarirai mata,  amma yana da matuƙar kyau da ayi duba ga sunaye ne masu daɗi. Waɗannan sunayen jarirai ne ga mata masu daɗi da za'a iya zaɓa.

  1. Ameerah = Gimbiya

  2. Khairat = Me alkhairi

  3. Samha = Mai kyau

  4. Noor = Haske

  5. Husna = Kyakkyawa

  6. Mufida = Me anfani 

  7. Amatullah = Baiwar Allah 

  8. Nawal = Kyauta

  9. Afrah = Farin ciki

  10. Faiza = Babban rabo

  11. Eiman = Imani

  12. Afaf = Kammamiya 

  13. Basmah = Murmushi 

  14. Nasreen = Wata fulawa mai kamahi a gidan aljannah

  15. Saliema = Mai aminci 

  16. Rauda = A cikin masjid nabawi 

  17. Qalbiy = Zuciya ta

  18. Siyama = Mai azumi 

  19. Sawwama = Mai yawan azumi 

  20. Kawwama = Mai Sallar dare 

  21. Nuriyya = Haskakawa 

  22. Intisar = Mai nasara

  23. Sabira = Mai haƙuri

  24. Meead = Alkawari

  25. Islam = Musulunci

  26. Ahlam =  Me kyawawan mafarkai 

  27. Siddiqa = Mai gaskiya

  28. Mannal = Wadata

  29. Sayyada = Shugaba

  30. Hannah = mai tausayi

  31. Sajeeda = Mai yawan sallah

  32. Hameeda = Godiya ga Allah

  33. Afnan = Ci gaba

  34. Nabiha = Mai kwazo

  35. Yusurah = Mai sauki

  36. Salsabil = Mai sauki da jin kai

  37. Mila = Mai kwazo = 

  38. Farrah = Mai farin ciki

  39. Amina = Amintacciya

  40. Jihan = Rai

  41. Amrah = Farin ciki

  42. Arwa = Alheri

  43. Asma = Mafi girma

  44. Atheelah = Mai aiki da adalci da gaskiya

  45. Aliya = Mai tashi 

  46. Azban = Sabo

  47. Baghoom = 

  48. Barakah = Wacce ke da taushin murya mai mace

  49. Bareerah = Mai tsoron Allah

  50. Barzah = Ta kasance mai ruwayar hadisi

  51. Buhayya = Mai dadi

  52. Bushrah = Labari mai dadi

  53. Fakhitah = Kurciya

  54. Fariah = Farin ciki

  55. Farwa = Rufewa

  56. Fasham = Babba kuma Fadi

  57. Fatima = Jan hankali

  58. Firozah = Mai Nasara

  59. Fakaihah = Fure

  60. Ghufairah = Gafara

  61. Habibah = Masoyiya

  62. Hannatu = Mai tausayi

  63. Halah = Halo a kusa da wata

  64. Halima = Mai hankali 

  65. Hammat = Abin kunya

  66. Hamizah = Abin sha'awa

  67. Nasiba = Sa'a

  68. Isma = Kariya daga zunubi

  69. Jamila = Kyakkyawa

  70. Jumail = tsuntsu mai waƙa

  71. Jumanah = Lu'u-lu'u na azurfa

  72. Juwairiyya = Yarinya karama

  73. Kareemah = Mai Karimci

  74. Khadijah = Amintacciya

  75. Na'ma = Komawa ga Tushen

  76. Khawlah = Barewa mace.

  77. Kulthum = Wani mai girman fuska

  78. Lailah = Dare 

  79. Lubabatu = Sarauniyar Aljanna

  80. Lubaynah = Madara mai tsafta

  81. Maria = Masoyiya

  82. Maymunat = Albarka

  83. Nahdiya = Mai sanarwa

  84. Najiya = Yanci daga haɗari

  85. Nusaibah = Dace

  86. Qutaylah = Jagora da zuciya

  87. Rakheelah = Tashi

  88. Ramlah = Mai hankali

  89. Raheenat = kaddara

  90. Rufaida = Ƙaramar mataimakiya

  91. Ruman = Soyayya

  92. Rumaisa = Fure-fure

  93. Ruƙayyah = Mai jan hankali

  94. Safiyyah = Tsafta 

  95. Sahla = Santsi

  96. Salma = Aminci

  97. Sarinnah = Kyakkyawan aboki

  98. Shifa = Waraka

  99. Shirin = Dadi

  100. Zeenat = Ado

Sunayen Jarirai Na Maza Masu Daɗi

Ga yawan iyaye, da gyaran sun haifi jariri, ɗaya daga cikin fatannin su ɗan jaririn ya zama ɗa namiji. Wasu sai sun haifi yara biyu ko fiye da haka suke samun ɗa namiji, wasu ma a haihuwar su ta fari suke haifan namiji; abun dai na Allah ne. 

Sanya wa jariri namiji suna, mataki ne da za a iya ɗauka a cikin ɗan kankanin lokaci, amma a sani, zai faɗa wa duniya abubuwa da yawa da dama akan sa. Wannan shi yasa da gyaran an ga ɗabiar mutun aka dubi sunan sa, sai kaji ana bai bi sunan sa ba; duk da cewan sunan mutum ba shi ke nuna ɗabiar sa ba. Don haka muka tashi tsaye don ganin cewa mun kawa muku waɗannan sunayen jarirai maza masu daɗi. Yana da kyau a san cewa wannan sunaye basu kare akan jarirai kaɗai ba.

  1. Faiz = Nasara

  2. Imran = Farin ciki

  3. Shariff = Ɗaukaka

  4. Ghassan = farkon rayuwa

  5. Ismail = Allah ya ji

  6. Ilham = Ilham

  7. Ghalib = Cin nasara

  8. Mufaddal = Zaɓaɓɓe

  9. Abdul = Bawa

  10. Adel = Mai daraja

  11. Barack = Mai albarka

  12. Kamil = Cikakke

  13. Jamal = Kyakkyawa

  14. Bilal = Mai nasara

  15. Ihsan = Yin abu mai kyau

  16. Jalal = Girma

  17. Gallal = Girma

  18. Ansar = Mataimaki

  19. Mukhtar  = Zababbe 

  20. Junaid =  Jarumi

  21. Hamid = Yabo

  22. Ala'Din = Yarda da ƙaddara

  23. Mubeen = Bayyana

  24. Asim = majiɓinci

  25. Baqir = Hankali

  26. Abd al-Karim = bawan Mafi Karamci

  27. Abd al-Hamid = Bawan mai bayarwa.

  28. Jafar = Ruwa

  29. Fihar = Kulawa

  30. Hasib = Mai daraja

  31. Gabar = Dan kungiyar addinin Iran

  32. Sayi = farar ƙaramin fure mai laushi mai ƙamshi mai kyau.

  33. Bilyamin = Mai hankali

  34. Amjad = Mai Girma

  35. Ali = Zakaran

  36. Tahmid = Godiya ga Allah maɗaukaki

  37. Abdur Rashid = bawan mai gaskiya.

  38. Iman = Imani

  39. Nazir = Mai lura

  40. Abdullahi = Bawan Allah 

  41. Ammar = Wadataccen tsawon rai

  42. Fadi = Mai fansa

  43. Mu'az = Mai kariya 

  44. Bassam = Mai murmushi 

  45. Yahuza = Wayayye 

  46. Baki = Murmushi 

  47. Afzal = Koyi

  48. Fadil = Nagari madalla da cikawa

  49. Isah = Addu'ar dare

  50. Ahmad = Mai godiya ga Allah 

  51. Akram = karimci

  52. Asif = Gafara

  53. Mannir = Zauren wani kadara

  54. Adnan = Mai shiryawa 

  55. Gamar = Faɗawa soyayya

  56. Azhar = Haskakawa

  57. Amal = Fata

  58. Faris = Mahayin doki

  59. Abdulkadir = Bawan mai iya komai

  60. Sufyan = Tafiya da sauri

  61. Anisi = Taimako 

  62. Atallah = Bawan Allah 

  63. Saifullah = Takobin Allah

  64. Fahad = Damisa

  65. Asad = Zaki 

  66. Hussaini = daga sunan Imam Husain bn Ali

  67. Anwar = haske

  68. Atiya = Kyauta

  69. Munir = Haskakawa 

  70. Al'amin = Amintacce.

  71. Jihan = Duniya

  72. Musbah = Fitila

  73. Sauki = kyakkyawa

  74. Ayman = Mai sauki 

  75. Jabbar = Babba 

  76. Abbas =  Zaki

  77. Anas = Wanda ya iya zama da mutane 

  78. Alhassan = Mai kyau

  79. Usama = Zaki 

  80. Dawood = Sunan annabi 

  81. Amir = Yerima 

  82. Hafiz = Mai kiyayewa

  83. Basil = Bawan Mai faɗaɗawa

  84. Haruna = Sunan annabi harun

  85. Hamza = Tsayawa

  86. Aqib = Na gaba

  87. Aqil = Mai hankali

  88. Yasir = Da kyau a yi

  89. Abi fadil = Mai girma

  90. Iskandar = Kare maza

  91. Diya = Haskaka

  92. Abd al-samad = bawan Jagoran mai arziƙi

  93. Jabir = Mai ta'aziyya

  94. Haidar = Zaki 

  95. Abde el- hakim = Bawa mai hankali.

  96. Ala = Reshe

  97. Mahdi = shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya

  98. Uzaifa = wanda ke kaurace wa

  99. Fuad = Manufar "hankali da ruhu

  100. Irfan = Faɗakarwa

Kammalawa 

Jariran mu sun cancanci sunaye masu daɗi da zasu so idan Allah yayi musu tsawon rai suka yi girma. Jarirai ko nace yara, kyauta ne marar misaltuwa daga Allah . Don haka mu dage wajen ganin cewa mun zaɓa wa jariran mu sunaye masu daɗi.


Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa