Top 10 Littattafan Hausa Novel Complete Sites

 

Shin kina neman littattafan hausa novel complete kamar su jarababben namiji, gidan uncle, tayi mun kankanta, da matar hariji ko kuma makancin haka na romantic hausa novels complete? Toh mun san inda zaki same su cikin sauki ba tare da bata lokaci ba.


Indai harkar hausa novel ne, toh akwai websites da yawa wanda ake yi su dan saka maku labaran soyayya masu dadi da ratsa jiki. A wannan shafin, zamu jera maku websites din da zaku sami littattafen hausa ku karantasu cikin sauki ba tare da kun kashe kudi ba.

Wattpad Hausa Novels — Gidan Tsofaffin Hausa Novels

Wattpad shafi ne akan yanan gizo da ake daura novels. Dadin abun shine akwai litattafan da wasu marubutan Hausawa suka rubuta dan nishadantarwarku. Yawancin littattafen dake Wattpad tsofaffin novels ne. Akwai marubuta da yawa akan wannan website din. Amma akwa gida biyu da suka shahara indai wajen rubuta romantic novels ne. Cikin su akwai Real_ahmerd da kuma Aisha Nana. 

Daga cikin novels din Real_Ahmerd akwai Zan so ka a haka, Qalbina (Kece zaki fidda ni), Abin de ake guduMakauniyar hanya, da kuma Rayuwar Bintu, da dai sauransu. Akalla akwai littattafen labaran soyayya sun fi dari (100). Zaku iya duba shafin sa tawannan link din.

Ita Aisha Nana ba’a barta a baya ba. Itama ta daura wasu labaran masu dadi da ratsa jiki. Cikin wainda da daura akwai Da ciwo a rayuwata, Babban Goro, Me rabo ke dauka, Batul, da kuma Sabon salon da’namiji. Wainnan yan kwarani ne, zaku iya ganin sauran sunayen littattafen da ta daura a shafin Aisha Nana a Wattpad.


Hausa Novels Only – Best Writers on Facebook

Shida Hausa Novels Only group ne a Facebook wanda mutane da dama sukan iya daura novels a yaren Hausa. Zaku sami littattafen soyayya amma ba a jera su kamar yadda Wattpad ta jera su ba. Kuma novels din basu yi complete ba tun da ana daura su ne chapter by chapter idan aka rubuta su. Wannan dai ba matsala bane. 

Inda na so wannan group din a Facebook shine zaka iya magana da authors (maruba) ko wanne littafin da a ka saka a wajen. Kuma yawancin labaran da aka daura sabbin hausa novels ne. Amma fa akwai wasu marubutar da zasu butaci ku siya littafin su dan samun complete labarin dake cikin su.

TaskarNovels — Best Place to Download Complete Novels in PDF

TaskarNovels wani website ne wanda aka yi shi dan daura maku littattafen hausa. Akwai bangare guda uku da suka shahara akai. Su ne littatafan yaki da yake yake, littattafen soyayya wato hot romantic hausa novels, and littatafan almara. Ya kamata ku gane wani abun. Wainnan littafen ba su su ka rubuta su ba. Dukkan su suna da marubutar su daban daban, su kawai suna daura su ne. Dadin abun ga wannan shafin shine zaki downloading din su a PDF. 

Wannan zai sauwake maka aikin ka ba tare da ka bata lokaci a online kana karata su ba. Daga cikin romantic littatafan hausan akwai Ustaziya ko yar duniya, Zaki gane kuranki, yar hannu, wani namiji, aboki ko masoyi, sakatariya ta, da dai makamancin su masu dadi da ratsa jiki.

All Hausa Novels Android – Read Hausa Novels in App

Ga masu son su karanta romantic hausa novels a app, toh ga naku. Zaku iya karanta novels a app din All Hausa Novels wanda akayi wa masu amfani da Android. Idan iPhone kake da shi, baza ka iya amfani dashi ba. Kuma ya kamata ka san littafan hausa akan app dinnan basu da yawa kamar yadda suke dashi a kan Wattpad, Hausa Novels Only, da kuma TaskarNovels. Hakan ba yana nufin ba novels bane da zaku karanta a app din. 

Akwai littattafai kamar haka – Abokiyar nishadi, Maman Al-Amin, Hasken Zamani. Wani abun da zaku so a wannan app shine yana da tashosin hausa novels wanda zaku iya bi. Akwai YouTube channels na littafen hausa da films da zaku iya samun nishadantarwa daga nan.

Okada Books

Shi OkadaBooks wani app ne wanda marubuta ke iya saka novels din su dan karanta war alumma. Anyi wannan app din ne dan saka novels din turaci amma ayanzu, novels din Hausa akan sa kuna da yawa kuma marubuta akan app din kwararrune wurin rubuta romantic labaran so na Hausa. Amma fa, sai kun biya kafin ku iya karanta labaran Hausa da ke kan app dinnan. Amma littattafan basu da tsada tunda zaku iya siyan littafi akan Naira 200. Zaku iya kaaranta littafen aka app din koh website. A wannan ba talla so ba abun da zai matsa ma wurin karanta littattafen Hausa na love that kuka siya dan karantawar ku.


Daga Karshe

A sama mun jero maku websites da apps din da zaku iya karanta littattafen hausa novels masu dadi. Zaku samu hot romantic stories irin wadanda kuke so ku karanta dan jin dadi kun ba tare da kun biya ba. 


Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa