250+ Jerin Sunayen Mata da Ma'anarsu a Musulunci
Bada suna ya kasance babbar mataki ne ga kowanne iyaye. Sanya kyakkyawan suna shine kyauta na farko da iyaye za su iya bayarwa ga jaririn da zai manne da su har abada. Sanin sunayen mata da ma'anarsu a musulunci yana taimakawa wajen zaɓan sunayen da suka dace mu bawa yayan mu mata. Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kowacce yarinya tana da hakkin a sanya mata suna mai ma'ana.
Sunayen Mata da Larabci Masu Daɗi
Sunayen Larabci ga 'yan mata suna da tasiri a addinin musulunci.
Anan, zamu tattauna nau'ikan sunayen mata masu daɗi don ba ku zaɓuɓɓuka da yawa. Kuna son sunaye masu ban sha'awa, ta zamani, muna da tabbacin za ku sami sunaye da kuke so a jerin waɗannan sunayen mata da larabci:
Ramlat = Hatsi na yashi
Ma'ida = Mai kyau
Rashidat = Mai adalci
Mufeedat = Mai amfani
Fareeda = Na musamman
Sakinat = Aminci
Nuratu = Haske
Asisat = Mutum mai karfin
Siddiqa = Mai imaani
Nawwarah = Da kyar
Raheela = Tashi
Rafi'a = Tausayi
Zabba'u = Kulle kofa
Adama = Duniya
Rumasa'u = bokitin fire
Zineyra = Furen Aljanna
Sawwama = bukata
Bahija = Murna
Hamdah = Yabo
Ummuqultsum = Uwar Kulthum
Mansura = mai nasara
Farhana = Mai fara'a
Hannatu = tausayi
Sumayyatu = Sama fiye da
Suwaiba = lada ga ayyukan alheri
Hasana = Kyakkyawa
Ummusalma = Uwar Zaman lafiya
Ummulkhair = Uwar Alkhairi
Fadila = Fitacciya
Hamat = Muhimmanci
Asma'u = Mafi girma
Dayyibah = Kyawu
Nasiba = Sa'a
Basma = Murmushi
Usamtu = Na macen zaki
Abidah = Mai ibada
Bashara = Labari mai dadi
Zeenat = Ado
Badia = abar sha'awa
Zahara = Fure
Radiya = Luɓeɓɓe
Jamilat = Mai alheri.
Shahwat = Sha'awa
Husna = Kyawu
Nusaiba = Mai daraja
Nana Firdausi = Sunan Aljanna
Suhaila = Toushi
Taiba = Tsaftacciya
Mardiyya = Zaɓaɓɓiya
Zubaida = Babban tudu
Hajara = Mai haskawa
Zuwaira = Juriya
Zulaihat = Mai zaman kanta
Zurfa'u = Ƙirƙira
Asiya = Tunani mai kyau
Abidah = Mai sadaukarwa
Hamidah = Mai hankali
Zulaikha = Kyakykyawan kyau da mutane suka taru cikin mamaki
Suliat = mai ƙwazo da juriya wanda ke jin daɗin aikin yau da kullun inda zaka iya yin aiki da kyau kuma ta gama abin da ta fara.
Sikratu = Ambaton Allah
Rahma = Rahama
Sahra = Hamada
Salima = lafiya
Masauda = Farin ciki
Adira = Mai ƙarfi
Samhat = mai taushi
Fauziya = Mai nasara
Raudah = Lambun Adnin
Saudat = Rashin son kai
Samira = abokiyar dare
Hafiza = karewa
Ajila = Gaggawa
Bushra = Cikakkiya
Fakira = Mai tunani
Faiza = Mai amfani
Fakeenah = Natsuwa
Fakeeha = Mai fa'a
Haneefah = Mumini ta gaskiya.
Hanan = tausayi
Haseena = Kyakkyawa
Fateeha = Ga nasara
Ƙausar = Yawaita
Khudrah = Mai kalar ruwan ganye
Laila = Dare
Murjanatu = Mai jan hankali
Mahfuzah = Wacce aka kare
Afreen = Mai iya Sada zumunta
Naja'atu = Mutum mai nasara, mai kirki, mai zuciya.
Nusrat = Nasara
Najma = Tauraruwa
Na'imah = Natsuwa
Na'ilah = Mai samowa
Nadira = Mai wuyan samu
Nabila = Madalla
Naa'rah = Mai kyalli
Aakifah = sadaukarwa ga
Namira = Mace mai tsabta
Rumaisa = Iska mai watsar da kura
Lantana = furanni na lemu da shunayya, ” shirye don wadatar da duniya
Fulaira = Gaskiya
Sunayen Yara Mata na Zamani da Ma'anarsu
Ku iyaye ne ga kyawawan yara yanzu. Kuma kuna iya neman sunaye masu nagarta da daraja a cikin al'adun Musulunci. Akwai sunayen 'ya'ya yara mata na zamani da yawa da suke da kyawawan ma'anoni da za su zaburar da ku kuma Kuji kuna son bawa yaran ku.
Ga sunayen yara 'yan mata guda ɗari ta musulunci wainda zasu dace da waɗannan kyawawan yaran ku:
Najah = Kamila
Najida = Mai kwakwalwa
Iman = Imani
Mahjabeen = Mai kallon wata
Mayra = Bakin ciki
Aadila = Madaidaiciya
Aadiva = Gentle
Afaat = Pure
Abeer = Kamshi
Ablah = Cikakkiyar halitta
Hanan = Soyayya
Afra = Kalar duniya
Khaira = Alheri
Ikhlas = Gaskiya
Haifa = haɗuwa
Husna = Kyakkyawa
Nasma = Iska
Adara = Budurwa.
Aaliyah = Maɗaukakiya
Amira = Gimbiya
Aabidah = Mai ibada
Sabira = Haƙuri
Aabirah = Mai wucewa
Aafia = Lafiya
Naasima = Shugaba
Naaima = murna
Nazneen = Kyakkyawa
Naadimah = ƙawa
Nafeesah = mai daraja
Nagma = Waƙa
Nahla = Shan ruwan farko
Nafiah = Mai riba
Nahleejah = Kamila
Mahnoor = Hasken wata
Majida = daukaka mai daraja
Manaal = Nasara
Munira = Kyalli
Musarrat = Nishadi
Naira = mai kwazo
Nasra = Mataimakiya
Nihlah = Kyauta
Laiha = kyalkyali
Laiqa = Chanchanta
Lamees = Toushi
Maarib = Buƙata
Mabruka = Sirri
Mabrura = Yarinya saliha
Madaniyah = Wayewa
Madiha = abin yabo.
Mahrukh = fuska kamar wata
Kadira = Mai karfi
Kalila = Mai farin jini
Kamilah = Masani
Karida = Wanda ba'a taɓa ba
Lailat = Dare
Latifa = Natsatse
Liyana = Mai laushi
Labbaanah = Madara
Labeebah = Mai hikima
Labeeqa = Mai ado
Lafiza = Mai zurfi
Jamilla = Kyawu
Jahida = Mai taimako
Jaide = Da kyau
Jaleela = Mai girma
Jumaana = ɓoyeyyen lu'u-lu'u
Jazmaine = Fure
Kalima = Magana
Kareemah = mai daraja.
Iqra = Karatu
Izma = Girma
Ibtihal = Addu'a
Ibtisam = Murmushi
Ifeta = Mai gaskiya
Iffaat = Nagarta
Ifza = Mala'ikan Kariya
Ihkam = ƙurewa
Inaam = Kyauta
Illeeyeen = Babbar matsayi
Jahida = Mai taimakon masu rauni
Hafsa = matashiyar zaki
Haifa = haɗaɗɗiya
Haiza = Sarauta
Haneeya = Jin daɗi
Ibadah = Worship
Ihsan = kamala
Ibtihaj = Farin ciki
Inara = Wanda aka turo daga sama
Meenal = Arziki
Haadiya = Jagora
Haaya = jin kunya
Humayrah = Ja
Habeeba = Mai farin jini
Ghadiya = Ruwan safe
Gufrana = Affuwa
Muhibba = Ƙauna
Faaria = Doguwa
Fahmeeda = Yarinya mai hankali.
Faheeda = Mai son sani
Ehteram = Girmamawa
Sunayen Mata da Halayensu
Sunayen mata suna da banbanci, haka zalika halayen su ma ya sha banban. Alamu sun nuna ko wace mace tana da yadda take halayyenta, kuma akan gane halayen mata ta Sunayen su. Idan aka ajiye mata goma masu suna ɗaya, Mafi akasari zaka sami wajen bakwai suna halayya iri ɗaya.
Ruqayyat; mace mai suna ruqayya tana da zuciya sosai. Ga taurin kai Kamar wani namijin. Ruqayya suna da musu, kuma ga zagi a bakin su tamkar katsinawa.
Binta; Binta mace ce da zaka ganta cikin tsafta a koyoushe. Kuma duk mai suna Binta tana da wayo sosai fiye da yarda kake tunani. Binta suna da maƙo!
Samiratu; Samira tana da son Maza. Duk wata mai suna Samira za ka ganta mai marar wasa da addini, kuma yawan son mazan ta bai hana ta jijji da kai ba.
Asma'u; Asmau zaka gansu duk gajeru ne kuma Allah yayi musu ƙaton kai! Duk mai suna asma'u ta iya kallon maza kamar sun warke maƙanta.
Saudatu; Saudatu suna sallar magana, ga shagwaɓa tamkar yara. Saudatu a cikin mata ta kasance mai ƙunya ne, kuma akwai su da koƙari.
Fatima; Fatima sun kasance mata ne da zaka gan su shiru shiru a koda youshe. Ba'a cika samun munana a masu suna Fatima ba. Duk kuma suna da koƙari.
Hajara; Akwai da zuciya, kuma ga iya tsara maza. Ga wayo kamar zomo!
Maryam; Maryam suna da addini amma ga yawan surutu. Yawancin su farare ne.
Lubabatu; Lubabatu mata ne masu son gayu. Suna da son gulma sosai Kamar rayuwar sun dogara da Ita.
Nafisa; Nafisa Wasu mata na daban. A koda youshe Zaka ganta shiru-shiru abar tausayi
Amina; Mafi akasari mata masu suna Amina suna da kyau. Ga koƙari wajen karatu. Amintattu ne kuma ba'a cika samun munana.
Halima; halima basu ɗaukan raini. A duk lokacin da ka gansu a shirye suke domin afkawa duk wanda ya ketara layin su. Mafi akasari kyawawa ne.
Rashidat; mace mai suna Rashidat ta iya zama da mutane kuma sun san darajar mutum. Sai dai wani zubin, akwai rashin ji
Salma; Iyayen ƙunya kenan! Salma suna da kamun kai, basu yin magana idan ba'a tambaye su. Maganar da ta shafe su kawai suke sa baki. Ga ilimi da sani.
Hauwa'u; Hauwa'u suna da hayaniya da shagwaɓa. Idan akwai mai suna hauwa'u a waje, ba sai an gaya maka ba. Allah yayi musu kyau, ga kuma yawan wasa.
Hussaina; Hussaina suna saukin kai, basu san abin da ake kira da taurin kaiba. Suna da far'a kuma ga sannin addini.
Habiba; Habiba suna da kyau sosai. Ban taɓa ganin habiba mummuna ba. Suna da jan aji amma suna da daɗin sha'ani ga wanda suka saba da shi. Kwata-kwata basu son rainin aji.
Hafsat; hafsat Allah yayi su da son maza. Mafi akasari suna da kyau da daɗin sha'ani. Idan baka san su ba, sai ka sha wuya zaka iya shiga rayuwar su.
Rabia'tu; Mace mai suna rabiatu, Allah yayi ta da kishi; suna da bala'in kishi. Suna son su ga sune a gaba a ko da yaushe. Amma fah suna kyau sosai. Ba su da munana har ma da bakaken su.
Zainab; Mace mai suna zainab tana da saurin sabo da mutane, ga son sa mutane dariya. Allah yayi su da saurin fahimta, hakan yasa zaka gansu masu kokari ne a gurin karatu.
Qubra; Suna da ƙunya sosai. Basu iya sakin jikin su idan suna cikin mutane saboda tsananin ƙunya. Suna da bala'in kyau.
Sa'adatu; mace mai suna Sa'adatu tana kyau. Suna da son Maza amma kinsan shekara ɗari ne, idan baka yi musu magana ba, to su baza su fara yin maka ba. Ga Jan aji Kamar hauka.
Saratu; mafi akasari mata masu suna saratu zaka same su natsatse ne. Zaku iya zama da su, idan baka yi musu magana ba, ba zasu ce maka komai ba. Suna da kamun kai da yawan son zaman lafiya da mutane.
Rahinatu; Allah yayi su da jin tausayin mutane. A yadda ka zo musu, haka zasu zo maka. Basu ɗaukan raini ko na minti ɗaya. Babbar alamar su shine kyawu.
Sakinat; mace mai suna Sakinat tana ɗaya daga cikin mata masu kyawu. Ga tsayi da tausassan murya. Bacin kyawun da suke da shi, Allah yayi su da saurin ɗaukan ilimi. A duk inda zaka gansu, suna tsare girman su.
Fareeda; farida suna da tausayin mutane kamar iyaye. A kwullun ka gansu, zaka gansu cikin natsuwa. Ga su da faɗin gaskiya.
Bilkisu; mace mai suna bilkisu, Allah yayi ta da tsoro. Suna da tsaro sosai a rayuwar su. Zasu iya yin komai domin a zauna lafiya.
Ummurumana; suna da jan aji kamar hauka. Sai ka sha wahala kafin su fara yin maka magana. Suna kirka kalaman su yarda ka san suna ajimin magana ko da yaushe.
Salamatu; waɗannan, Allah yayi su da son girma. Ga son a gaishe su. Gasu da rika mutum a cikin zuciya. Amma mafi akasarin su suna da son ilimi.
Jamila; suna da rike namiji kamar abun maƙale. Idan suna soyayya, da dukkan zuciyar su suke yi. Da yawan su zaka same su kyawawa ne, kuma ga ƙunya.
Maimunat ; maimunat basu son rainin wayo, suna da wayo kamar biri! Suna da riƙon addini sosai kuma ga biyayya.
Safiya; Suna da ladabi, ga subda girmama na na gaba da su. Amma idan ka tsokane su, zaka yaba wa aya zaki. Ga ilimin addini.
Aisha; mace mai suna aisha tana kula da mazan ta sosai. Ga ladabi da biyayya har ma da iya zama da mutane.
Bahijja; bahijja suna da wuyan gani. Suna da tsafta sakamakon iya kula da kansu. Ga jan aji da gayu.
Rahama; Mace mai suna rahama na da taurin kai, idan suka sa a ransu zasu yi abu, babu mutum da zai iya hana su komin girman sa. Suna da kyau sosai kuma Allah yayi musu far'a.
Latifa; suna da yawan shagwaɓa. Ba'a cika samun munana ba a cikin masu suna latifa. Suna da kaifin Kwakwalwa, Fatima yawan tsiya
Shamsiyya; Shamsiyya suna da gayu da son Jan hankali samari. Suna ɗaukan kansu tamkar sarauniya. Suna da kyau ba laifi.
Badia; Duk mace mai suna badia tana da koƙari wajen addini. Ga son zikiri da kuma iya mu'amala da mutane. Suna da karamci.
Hamat; Hamat suna da saukin kai. Abin da ya dame su kawai suke yi. Basu da jan aji kamar wasu matan
Khairat; Waɗannan ka bar su da gayu. Suna son yin ado kamar wasu fure. Ga son maza. Suna da rashin natsuwa musamman ma idan an ɓata musu rai.
Salaha; Mace mai suna salaha tana da natsuwa sosai. Ga koƙari wajen karatu. Suna daraja mutane a ko ina. Basu son hayaniya ko kaɗan
Khadijat; Khadija suna da yawan gaisuwa. Indai ladabi da biyayya ne, ba'a barin su a baya. Kyawawan su sun fi yawa.
Murshida; Murshida suna da wasa sosai, hakan yake sa ake ganin su kamar basu da wayo. Suna da son kallon mutane kamar sun warke maƙanta
Amatullah; Macen da ake kira da amatullah, zaka same su kamilai. Da kyar ake iya jin muryan su. Suna da jin ƙunya kamar kunkuru
Harirah; Wainnan ga bar su da son iko. Suna da son kai kansu inda Allah ba kai su bah. Ga kankanba da son girma
Salima; Suna da tsoro kaman me. Ga son maza da son kwalliya. A duk lokacin da ka gansu, suna tare da kayan kwalliyan su a jakar su
Surayya; Surayya basu da damuwa. Abin da ke gaban su kawai suka sani. Ga far'a ga kuma iya mu'amala da mutane.
Zakiyya; wainnan indai kyawu ne. Suna da kyau sosai. Sannan kuma suna da saukin kai. In an zo wajen karatu kuma, ba'a barin su a baya.
Hashiya; Ga kyau ga ƙunya. Zaka same su cikin tsafta a ko dayaushe. Ga kuma kamun kai.
Faiza; Faiza Allah yayi musu son maza. Suna son gayu da ababan zamani. Ga saukin kai anma basu da wani natsuwa.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here