Kalaman Soyayya Zuwa Ga Saurayi
Godiya so ba iyaka zuwa ga mafi abun ban mamaki da nasani a rayuwa ta. Ka nuna cewa akwai soyayya ta gaskiya. Bazan taɓa tunanin ranar da zamu rabu ba.
Idan da ace wani zai tambayeni akan irin namijin da na so, da ban sami kalaman da zan iya kamanta ka ba. Ka wuci duk yadda ake tunani.
Kyawun ka, natsuwar ka, da kyawawan ɗabi’un ka yasa nake kara faɗawa soyayya da kai a kowace rana! Kai ne komai na a rayuwa.
Wani zubin sai inji kamar ina mafarki, amma sai na fahimci zahiri ne. Tabbas ni mai sa'a ce a wannan faɗin duniyar. Nagode da zamtowa tawa.
A duk ranar da natashi, sai na ji tamkar ina cikin Aljanna saboda tsarin soyayyar mu. Ina son na mai da kai mutum mafi farin ciki a duniya.
Ya ɗauke ni kallo ɗaya kacal gare ka na ji zaka zamto saurayi na. A ƙullun ina miƙa godiya ga Allah da yasa na saurari zuciya ta. Sauran ya zama labari.
A yayin da shekaru ke tafiya nake koyin sabbin abubuwan da zan ƙaunata akan ka. Kaine mafi burgewan namiji a rayuwa ta.
Ina kewar kyawun fuskar ka,ni fah ko ban ci komai ba, Fuskar ka kawai ta ishe ni ƙoshiya.
Ka saka ina jin kamar ni mace ce ta daban a rayuwa. Kaine duk abunda nakeso a namiji. Ina rokan Allah da ya bar mu tare har abada.
Zan ƙauna ce ka sau ba iyaka, ina fatahn ka san da haka. Ko wace safiya ake wa ubangiji godiya akan ka.
Ina ƙaunar ka. Wannan shine abu mafi mahimmanci. Ko menene zai faru a rayuwar mu, muna ciki tare. Sai inda karfi na ta kare.
Faɗawa soyayya da kai ya saka na zamto mutum ta daban a halayya, Ina mai maka godiya don hakan.ba zan ya zanyi da rayuwa ta ba idan na wayi gari wata rana ba ka.
Ina jin kai na mafi farin cikin mace da mafi tsaro a duk lokacin da nake tare da kai. Ina sonka sosai, abun ƙauna ta!
Har abada zan wa Allah godiya da ya haɗa ni da kai. Kai ba saurayi na ne kawai ba; kai babbar aboki na ne. Ina ƙaunar ka amini na.
Zuciyar ka cike take da soyayya, kuma ni mai babbar sa'a ce da samun guri anan. Ina son ka!
Son ka shine babbar abunda na taɓa yi a rayuwa ta. Kuma ba zan taɓa yin nadama akan shi ba.
Ko wani rana a rayuwar mu tamkar ta fari ce don ba zan iya dai na son ka yau da ƙullun ba. Ina ƙaunar ka.
Babu kalaman da zan iya amfani wajen gwatance soyayyar mu. Ina matuƙar godiya gare ka.
Komai na rayuwa ta baci, kasancewar ka yakan sa komai yayi kyau, Ina godiya da samun ka a rayuwa ta.
Samun ka a rayuwa na ni'ima ne. Zan ci gaba da son ka a zuciya ta har abada.
Ban taɓa sanin so yakan zama abu mai kyau haka ba har sai da ka shigo rayuwa ta. Ina son ka fiye da yar da kake tunani.
Iya lokacin da mu ke tare, Iya yadda soyayyar mu ke kara ƙarko. Ba zan taɓa daina son ka ba.
Komin yawan shekarun da muke a tare a soyayyar mu, da kwai lokuta biyu da nakeson kasancewa da kai; yanzu da kuma har abada
Indai har ina da rai kuma ina numfashi, zan ƙaunace ka har abada masoyi na!
Kasancewa a soyayya da kai tamkar tafiya ce da bai da ranar dawowa. Tun da ubangiji ha hacce ni, bai taɓa jarabta na da son wani kamar ka ba, idanu na basu gani idan ba ka.
Abun ban dariya ne mutum yana rayuwa da tunanin cewar rayuwar sa ta cika, har sai ka faɗa soyayya. Yanzu a duk lokacin da bamu tare, ji nake tamkar rayuwa ta bata cika ba.
Ka kasance a kusa da ni komin nisan dake tsakanin mu. Matukar raina na bugawa, bazan taɓa nisantuwa da kai ba.
Ya kasance abu mai amfani a gare ni da na faɗa maka "I love you" ba don kawai ya zamo haliba, domin dagaske nake!
Na kasance mai babbar sa'a da samun daman yin rayuwa tare da kai. Zamu kafa tarihi mai girma da gaske.
Ka kasance haske ne a rayuwa ta. Rayuwar zata zama guri mai duhu da gaske in baka.
Na kasa tuna yadda rayuwa take lokacin da baka, kuma ba zan so na tuna ba!
Ina kewar ka kuma na kosa da na saka idanu na akan ka. Nagode da sanya rayuwa ta cike da farin ciki.
Burin rayuwa ta itace na so ka, kare ka, kuma na ƙauna ce ka har abada. Alkawarin da na ɗauka da zuciya ta gaba ɗaya!
Yin wannan tafiya ta soyayya da kai ya kasance abu mai girman gaske a rayuwa. A ranar da na haɗu da kai, Allah ya karbi Addu'a ta.
Da gaske ina alfahari da kai. Kana saka ko wani yini ta zamo tamkar kar ta wuce.
Soyayya ta gare ka bata misaltuwa. Karar muryar ka kamar waƙa ce a guri na.
Har na hakura da soyayya, amma zuwan ka ya canza mini komai!
Na gudo gurin ka ne don kai ne tsaro na. Kai ba zabi bane, kai buri na ne!
Kai kawai nake muraɗin gani. Ka kasance ɗaya ne cikin miliyan.
Idan nayi tunanin shekaru ashirin ɗina masu zuwa, ina ganin ka kusa da ni.
Ko wani sa’a guda nayi ba tare da kai ba, sai naji kamar rayuwar ne gaba ɗaya.
Ban taɓa tunanin zan so wani kamar yadda nakeson ka ba. Kai ne abu mafi girma da ya taɓa faruwa da ni.
Girman Soyayyar mu tana Saka zuciya ta cikin jin daɗi! Idanu na don kai ne kawai.
A kowani wucewar rana nake kara fahimtar girman sa'a ta don samun ka a rayuwa ta.
Ka canza min duniya ta a ranar da muka haɗu kuma ban kara wai gowa baya ba tun daga nan.
Ni kaina tafiya ce, amma na kan zamo karfin tafiyar idan kana tare da ni.
Tabbas nasan ba gwani, amma ba shakka ka kusa zama.
Sako Ɗaya kacal daga gare ka ya isa ya haskaka wuni na gaba ɗaya.
Daga ranar da muka haɗu, nasan zaka zamo tawa kuma na zamo taka. Ni da kai mun zamo ɗaya har abada.
Allah ya halicce mu ne don junar mu. Babu abinda zaka yi da zai sa na daina ƙaunar ka. Da kayi abun haushi ma sai inji na kara son ka. Ina son ka da dukannin zuciya ta.
Ina son soyayyar mu ta zamo irin wanda mutane zasu gani suce suna son irin ta. Da kai komai mai yuwa wa ne. Kar Allah ya nuna mana ranar da zamu rabu.
Ka san yadda zaka saka ni dariya ko da na kasance cikin kunci. Ina son ka hasken zuciya ta. Son ka ta zame mun farilla!
Kai ne dalilin rayuwa na. Kuma bazan iya misalta yadda nakeson ka ba. A duk faɗin duniyar nan, babu ma’aunin da zata iya awna girman soyayyar mu. Ka sha zamanka ka huta nawa!
Bana son duniyar, kawai kai nake so. Wani sahin sai inji kamar kai kaɗai ne namiji a faɗin duniyar nan. Bana tuna girman wanin ka idan ba kai ba. Ina ƙaunar ka jarumi na.
Soyayyar ka ne dalilin kyawawan Mafarki na da daddare da kuma jin daɗi na a rayuwa. Ka shayar da ni da ruwan soyayyar ka, tayi mun daɗi, kuma ba na son rabuwa da shi.
A duk lokacin da nayi yunkurin ɗauke zuciya ta daga gare ka, sai ta sullube. Zuciya ta kawai kai kaɗai take ƙauna. Nagode maka da shigowar ka cikin rayuwa ta.
Masoyi, babu abinda ke rikirki ta ni kamar murmushin ka. Ka game yin mun a rayuwa. Allah ya albarkaci ranar da muka haɗu, ɗaya daga cikin ranakun da ba zan iya mantawa ba kenan a rayuwa na.
Tunda na haɗu da kai, ban taɓa sekan ɗaya ba tare da nayi tunanin ka ba. Kana cikin tunani na da kuma zuciya a ko da yaushe.
Nagamu da abubuwan ban mamaki da dama, amma ban taɓa gamuwa da abunda ya kai ka ba. Girman ka a guri na ya wuce misaltuwa. Ina ƙaunar ka masoyi na.
Kaine duk abinda na ke bukata a rayuwa, ka sanya rayuwata ta zamo mai inganci da gaske. Wallahi wanin ka ba ya burge ni. Allah ya bar mu tare habibiy!
An ce soyayya tana koɗewa, na kasa fahimtar me yasa har yanzu tamu ta ki ta koɗe. Da duk alamun tamu ba mai koɗewa ba ce. Wai cin zan iya daina ƙaunar ka a cikin zuciyata?
Habibiy, ka shigo rayuwa na lokacin da nafi bukatar mutum a kusani, kuma ka sa na zamo mace ta daban. Nagode da wannan damar. Bazan taɓa barin ka ba.
Tun haɗuwar mu da kai, farin ciki da murmushi ya zame mun hali. Rayuwa ta zo mai inganci saboda kai. Ba zan dainayiwa Allah godiya ba da ya turo min kai.
Ba ka da masaniya akan yadda nake ji saboda ganin ka, Ina jindaɗin taraf da kai a yayin da kake murmushi. Murmushin ka ta zame mun magani.
Kafin haɗuwar mu da kai, idan kawaye na suka tambaye ni akan lokacin da zan fara soyayya, sai ince masu lokaci bai yi ba. Amma daga ranar da na sa idanu na akan ka, nasan kawai lokaci yayi. A kallan mu na farko nasan kai na cikar wannan lokacin da nake ta jira.
Idan naga yadda mutane ke samun matsala a soyayyar su, sai na tambayi kai na; wai shin tamu ba soyayya ba ne. Amma da gyaran na juya tunani na gare ka, sai naji amsar tambaya ta. Ina son ka ruhi na!
Kai kaɗai ne nake bukata a rayuwa na. Ya iya zamto ban iya aiwatar da abun nake ji ba, amma idan ka kalli idanu nu, zaka ga tekun soyayya, ladabi da biyayya, da kuma kulawa marar karshe da nake yi maka. Kai nawa ne kuma ba zan taɓa barin ka ba.
Nagode da sanya na yadda soyayya ta gaskiya zata iya zama asali tamkar wanda nake ci a tastunniya. Kai ne yerima na, Na mai godiya da irin ƙaunar da kake bani. Allah yasa kar mu bata hanyar mu. Ina son ka fiye da duk abinda kake tunani.
Ko da ace zanyi tafiya na zagaye duka faɗin duniyar nan don neman saurayi wanda ya dace, nasan bazan sami tamkar ka ba a komai. Kai halitta nena daban daga ubangiji. Ka shigo cikin rayuwa ta ka juya ta, ka kuma maida ita fiye da yadda nake tunani. Ina son ka fiye da yadda kalamai zasu misalta.
Wani lokaci sai in sami kaina da fatan duka matan duniya su sami mazaje na gari. Amma sai na fahimci tunanin wata ta ji daɗin irin soyayyar mu sai inji ina kishi. Kai nawa ne ni kaɗai, kuma bazan taɓa raba ka da wata ba.
A dukkanin ni'imomin ubangiji a rayuwa ta, ni'imar samun ka ta fiye mun. Soyayya da kulawar da kake nuna mun a duk shekarun da suka gabata nada tasiri da gaske. Zan so ka har karshen numfashi na da har ma fiye.
Kalamai baza su iya aiwatar da irin soyayyar da nake maka ba. Kai wanda ya cike mun inda nake da tawaya, wanda ya sa nake jin kai na a raye, wanda ya nuna mun so ta hanyar da ban taɓa tunanin zai yuu ba. Ina godiya da samun ka a rayuwa. Kai ne duniya ta da komai na.
Ki tuna don kula da kanka, masoyi na. Kai babbar kyauta ne ga duniya, Kuma ka camcanci duk wani rayuwan jindaɗin da rayuwa zata iya bayarwa. Kar ka dami kanka, ka bi komai a hankali kuma ina nan a shirye don taya ka. Ina son ka amini na!
Soyayya ta gaakiya tana da wuyan samu, ina mai albarka da samun ta tare da kai. Soyayya lallai makaho ne da bata iya ta gano babbancin mu ba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma taƙaita jira.
Ina so na faɗa maka irin kyawun ka don aa maka murmushi a fuskar ka. Kana nufin duniya ne a guri na, kuma daga lokacin da ka shigo rayuwa ta, ji nake kamar ba acikin duniyar nan nake ba. Har ila yau na kasa yadda da sa'a ta wajen samun ka a rayuwa ta. Allah ya bamu tsawon kwana.
Akwai taurari da yawa da dama a sama, ɗaya daga cikin taurarin nan tafi haske. Wannan tauraro yana nufin soyayyar da nake maka. Soyayya mai inganci, ta gaske, kuma marar karshe. Soyayya ce da ta fito daga ɓangaren zuciya ta, daga ni zuwa wajen ka. Masoyi, daga cikin zuciya ta, nasan zamu kasance har abada, ba zamu rabu ba.
Nasan idan na tsufa, zan tuna yadda muke gardama kan kananun abubuwa sai in ji soyayyar mu ta fi karfin waɗannan abubuwan. Ya kamata ka san har abada ina godiya da kasancewar ka a rayuwa ta, Zan ƙaunace ka har sai na mutu. Soyayya ta gare ka bata da sharaɗi kuma bata da karshe.
Kusan duk ta ko wace hanya, ka canza mun rayuwa ciki da waje, a yayin da abubuwa suke a rugurguje, ka shigo ka sanya komai ya fara dawowa daidai. Kuma ka cike mun rayuwa da farar aniya. Ina son ka sosai da har zan iya sadaukar da rayuwa ta don kai. Yadda kake kula da ni da kuma abubuwan da kake mun nasanya zuciya ta cikin nishaɗi da walwala. Duk abunda kake mun na narƙe mini zuciya ta da soyayyar ka.
A kullun ina yawan faɗa maka wannan, amma ya cancanci maimaitawa. Kai ne namiji mafi kyawu da nasani, ciki da waje. Kuma ina ganin hakan a kowa ce rana. Ina son komai game da kai, game da mu. Kayi mun abunda ba wani namijin da ya taɓa mun. Ka sanya ni cikin farin ciki. Jarumi na, Ina son ka daga cikin faɗin zuciya ta.
Barka da warhaka masoyi na. Ina zaune kawai sai na ji wani farin ciki ya shigo ni, Ashe kiran ka ne zai shigo ta waya ta. Allah ya ji ya gani bazan iya boye son ka. Da nasan haka soyayya take, da na fara yin so yay ya tun ina yar karama. Soyayya da kai ta sa Alheri ne, ina matuƙar son ka.
Kafin haɗuwar mu da kai, ina yawan tambayar kai na, wai cin me ake ji a soyayya ne? Haɗuwa da kai sai na ji ashe soyayya tafi zuma daɗi. Yin ta Kuma da kai yasa ma tafi daɗi. Allah ubangiji ya bar mu tare har abada.
Nayi bincike a duniya gaba ɗaya ta yanar gizo, akan adadin rayuwar soyayyar mutanen da nasu take da daɗi kamar tamu, sai naga ashe ba karamar sa'a na taka ba. Ni mace ce mai babbar sa'a da samun saurayi mai kulawa kamar ka. Soyayya ta gare ka bazata gushe ba.
Ka shigo rayuwa na, ka bani dalilin yin soyayya. Ka mallaka zuciya ta, ka sanya kai kaɗai take bugamawa. Zuciya kai kaɗai kawai take ƙauna a duk yawan samarin dake faɗin duniyar nan. Babbar abun mamakin shine, ni da kai mun dace da juna!
Idan na zauna, sai na ringa tunanin yadda rayuwar mu zata kasance nan gaba, kamar yawan yaran da zamu haifa, sunayen da zamu saka musu ta yadda zamu tarbiyattar da su. Ba san yadda rayuwa ta zata kasance ba idan ba ka. Ina son ka hasken idanu na.
Masoyi, na tuna ranar da mu ka fara haɗuwa da kai, kanasanye da tuffafin ka mai daraja. Tun daga nesa da na hango ka, zuciya ta bani alama cewan kai ne, kuma tabbas zuciyata tayi gaskiya, Kai ɗin ne dai. Kar Allah ya nuna mun ranar da zan dai na son ka.
A kullum mafarkin ka nake yi tamkar yanzu muka fara soyayya da kai. A ko wace rana son ka a raina take kara zama ɗanye, wai cin ya zanyi da rayuwa ta idan na wayi gari ba ka. Allah ya kara mana nisan kwana. Ina kewar ka amini na.
So, wasu suka ce ruwan zuma, wasu kuma suka ce ruwan guba. Ina tunanin ko ma wace Iriya ce, ya danganci wanda ake soyayyar tare. Ta mu dai ba shakka, ruwan zuma ne. Ji ma nake tamu ta wuci zuma a daɗi. Ina godiya da samun ka a rayuwa ta.
Masoyi na, ina kishin duk wata ya mace da take mu'amala da kai a gudanar da harkokin ka, ni fa dama zai yu, ka daina mu'amala da mace gaba ɗaya, amma ba zai yu ba. Ina son ka san a kullum kai ne tunani na.
Wani saurayi ya mallaka zuciya ta, ya mai da bakin ciki na zuwa farin ciki. Wannan saurayin dai ko wanene shi, ina ganin Allah ne ya turo sa. Ina ta mamaki, wai cin ka san wannan saurayin?
Amini na, bana tunanin son wanin ka idan ba kai ba, idan ina cin abinci, kai nake tunani, cikin barci ma kai nake tunani. Tunanin ka ya zame mun hali. Kuma ba zan so na daina tunanin ka ba har abada. I love you hasken rayuwa ta.
Akan soyayyar ka zan iya zuwa ko ina, komin nisa kuwa. Sai da na fara Soyayya da kai na fahimci cewan da gaske garin masoyi baya nisa. Lallai kam da duniya bata cika gurin zama ba idan da ace ba ka.
Na daɗe ina tunanin wai kai wani irin mutum ne, gaba ɗaya kabi ka canza yanayin tsarin rayuwa ta. Ba shakka, haɗuwa da kai shine zabimafi girman da na taɓa yi a rayuwa. Ban taɓa jin ina nadaman faɗawa soyayya da kai ba. Ubangiji yasa wa rayuwar mu albarka.
Na sha ganin soyayya bila adadin, amma ban taɓa ganin wanda yake da daɗi kamar tamu ba. Wata kila da akwai, amma ni dai ban gani ba. Soyayya irin tamu suna da wuyan gani. Ina son ka sosai annur.
Wai na kasa fahimtar cewa da zuciya nakeson ka ko da rai. Komai ruwa da iska akan ka, baza na daina kewa ba. Ka nuna mun so ta gaske, kuma nayi alkawarin ba zan ɗauki son ka a banza ba. Nagode wa Allah da ya saka mun son ka cikin zuciya ta.
Soyayya kawai nake gani idan na kalli cikin idanun ka. Kai ne ɗa namiji da na taɓa jin ina mutuwar so, kai ne buri na a rayuwa. A duk lokacin da baka kusa da ni, sai inji kamar na rasa wani ɓangare a jiki na. Soyayya ta da kai har abada ne da yaddar Allah.
Ko ka san abunda yafi bani karfin gwiwa don kammala harkoki na ta yau da kullum? Na samo amsar wannan tambayar ne ranar da nayi wuni ɗaya ban sa idanu na akan ba. Ganin ka shine tamkar cajin waya a gurina. Ina kewar ka nawa!
Da gyaran na tuna da kai sai inji wani nishaɗi. Idan naji muryan ka sai naji wani sanyi a cikin zuciya ta. Idan na ganka sai inji haske ya rufe ni. Rayuwa ba tare da kai ba, zai yi muni da gaske. Ina ƙaunar ka sosai a cikin zuciya ta.
Barka da safiya masoyi na, ina fatahn ka tashi cikin koshin lafiya. Nayi wani mafarki yau mai daɗi, mafarkin da yasa naji kamar kar na farka daga barci. Ban damu ba wannan mafarkin yayi ta zuwan a kullum. Wai ka san mafarkin kan wanene?
Hakika soyayya dace ne, ni kam nayi dace. Samun namiji irin ka a soyayya yana da wuya. Ka iya Kulawa dani, ka iya maida fushi na zuwa murna, ka iya rarrashi, ka iya duk wani abunda saurayi zai yi wa budurwar sa. Ina ƙaunar ka gwani na.
A duk fasin duniyar nan, kai ne namijin da nafi Ƙauna bayan mahaifina, ka nuna mun daɗin dake soyayya. Na amince zan ƙaunace ka har duniya ta naɗe. Son ka a zuciya ta bata misaltuwa.
A duk yanayin da na tsinci kaina, idan na tuna da kai, sai inji bana wani damuwa. Saboda kai ka kasance jarumi ne. Idan ina tare da kai, ji nake kamar nafi kowa tsaro a duniya. Ko gidan gwamnati sai haka.
Menene ya fi komai mahimmanci a duniyar nan? Kowa na da amsar sa ga wannan tambayar. Amma ga ni, Ka fi komai mahimmanci a rayuwa ta domin ka zame mun mafita ga kusan komai. Godiya ga mahaifiyar ka da ta haifo mun ɗan yaro mai hankali irin ka. Ka wuni lafiya masoyi na.
Da turanci in zan kira ka, darling ne tsari na, da larabci kuma sannu nuril qalbi na, Ka zarci yadda suke tunani acikin rai na. Saboda yadda kake nuna mun so, sai in tambayi kaina; wai cin kai da sauran mazajen duniyar nan ɗaya ne. Kulawar ka gare ni ya inganta mun rayuwa. Nagode da hakan.
Da na kulle idanu na, kai nake gani, da na buɗe, kai nake gani, wai ta yaya zan bi in cire ka daga zuciya ta ne? Amma da na tuna irin farin cikin da kake sa ni, sai inji ka kwanta mun a rai. Ba soyayya irin soyayyar ka!
Allah sarki na mallae wa wani zuciyar sa, na sace shi kuma na maida shi nawa har abada. Da na daina son ka a rai na, toh na daina numfashi ne, Mutuwa ce kawai zata iya hana ni son ka.
Abubuwan da baza ka iya cewa da bakin ka ba, zaka iya cewa da hannayen ka; Zan amsa maka kuma cikin sauki. Ba zan iya faɗawa barci ba idan ban ji muryar ka ba, wannan itace dalilin da yasa nake tabbatar da munyi waya kullum da daddare. Ina matuƙar ƙaunar ka.
Nasan mun yadda akan zama abokan juna ne, amma na kasa jurewa. ina son ka, kuma bazan iya ci gaba da boyewa ba. Bana son Lallata abunda ke tsakannin mu, kuma ina fatahn zaka fahimce ni. Maganar gaskiya itace, tun daga farkon haɗuwar naji ina ƙaunar ka, amma na kasa aiwatar da kaina. Dan Allah ka aminta da ni zuciya ta ta samu tsukuni.
Ban taɓa jin yadda nake ji a yanzu. Ka sa ina ji kamar ina da rai yanzu ba kamar da ba, na zama mace mai kwanciyar hankali, kuma mace mai tsima. Ba zan iya daina tunanin ka ba, kuma nasan abunda hakan ke nufi, ina ƙaunar ka. Hakan kamar hauka, koma dai menene, maganar itace dai ina son ka. Allah ya haɗa tare har abadan abada.
Kafin haɗuwar mu da kai, nayi shawara da zuciya ta kuma na amince cewa bazan iya yin soyayya ba kuma. Amma ka nuna mun hakan ba gaskiya bane.godiya gare ke,ka nuna mun rayuwa guri ne mai daɗi, kuma ba sai nayi ta ni kaɗai ba. Matukar kana tare da ni, zan iya yin komai. Ina son uban yaya na nan gaba!
Zan iya inyi ta kallon fuskar ka a ko da yaushe, yana bani mamaki wai baka san da hakan ba. Ina mutuwar ƙaunar ka kuma Ina jin lokaci yayi da nasanar da kai. Ina nayi sauran rayuwa na tare da kai.ina komai ya sami alaka da kai.
Ka bani tsaro tamkar wata minista, akwai dalilai sun kai miliyan da yasa nakeson ka. Gaskiyan lamarin shine ban san daga ina ma zan fara ba. Kowai ina son ce maka kanasani jin daɗi kuma ina son ka fiye da yadda kowa zai so ka a faɗin duniyar nan. Soyayya ta da kai ba ta da kishiya. Ina kewar ka abun ƙauna ta.
Ina alfahari da irin namijin da ka zama, kai ne mutum mafi ban mamaki da nasani a rayuwa ta. Na kasa yadda da cewa ni na same ka. Zuciya ta aminta da kai, idanu na kai kawai suke muraɗin gani, kunnuwa na muryar ka kawai suke son ji. Rayuwa ba tare da kai ba, bansan ya zata kasance ba.
Irin wannan soyayya ta bambanta. Ina jin tushensa yana girma da zurfi kowace rana, kuma yana cika ni da farin ciki da kwanshiyan hankali. Ba zan iya jira in ga abinda zai faru a nan gaba a gare mu ba. Ina son ka so ba iyaka.
Zanyi asara sosai ba tare da ƙaunar ka ba. Yana ɗaga ni sama lokacin da ruhina ya faɗi. Yana taimaka mini in shiga cikin mafi kyawun lokuta. Ina matukar hauka da wauta cikin soyayya da duk abinda kake da duk abinda kake yi, baby.
Soyayyar ka ta sa naji kamar ba a taɓa sona ba. Murmushin ka yana kawo min kwanciyar hankali da farin ciki. Muryar ka kiɗa ce ga kunnuwana. Ina son ka sosai, ina so in yi kururuwa game da shi daga kowane saman dutse!
A gaskiya naji tsoron kowane namiji kafin in hadu da kai. Anji mini rauni sau da yawa wanda ba zan iya amincewa da kowa ba. Ka canza duniyata gaba daya. Zan kasance har abada godiya ga ƙaunar ka, baby. Zuciya ta tana jin aminci a hannunka.
A wani lokaci a rayuwa ta na daina yadda cewa zan sake so. Cewa wani ba zai taɓa ƙauna ta ba tare da gaskiya ba. Zuciya ta ta wargaje cikin kananan guda miliyan saboda karfin soyayyar da nake mika. Kai ne mafi kyawun abinda ya taɓa faruwa da ni.
Soyayya tana da sarkakiya. Ina ƙin magana game da yadda nake ji da ƙoƙarin fahimtar dalilin da yasa nake jin abinda nake ji. Ina son ka kawai saboda kai. Ina son ka saboda kowane ɓangare na ka yanasanya kowane ɓangare na farin ciki. Ina son ka, kuma wannan shine abinda ya shafe ni.
Kana da girma fiye da yadda kake tunanii, baby. Da ma ka ganin kanka kamar yadda nake ganin ka. Ban taɓa samun sha'awar wani ba a tsawon rayuwata. Ka girgiza duniya ta kamar guguwa. Ina son ka har abada.
A gare ni, kai ne ma'anar soyayya. Duk abinda kake yi yana sa ni jin ƙauna da jindaɗin abinda nake tare da kai. Babu wani abu mafi mahimmanci fiye da mu, baby. Zan so ka har zuwa karshen zamani.
Ni ne ɗan adam mafi farin ciki a raye, saboda ina da kai. Ina ganin ka a cikin komai. Kowace waƙar soyayya game da kai ne da kuma yadda nake ji. Nasan kai na musamman ne, kuma kasancewar ka nawa ya sa ni ma na ji na musamman. Nagode da komai, ina son ka.
Babu wani abu da ba zai yiwu ba muddin muna tare. Soyayyar da nake maka tana sa na ji kamar ba wani dutse mai tsayi da zai hana ni zuwa wurinka, baby! Ina son ka kamar yadda wata ke son duniya, kuma kamar wata, koyaushe zan kasance a kusa da kai.
Ba zan iya tunanin cewa mutum zai iya zama mai kirki da ƙauna kamar ka ba. Ina son ka da kowane yanki na zuciyata, kuma ba zan taɓa sayar da kai ga wani ba. Kowane aibi ya dace a gare ni. Nagode da kasancewa mutumina.
Ina da mafi kyawun mutum a duniya! Ina so kowa ya sani cewa ni mace ce mai so. Ina so in raba wannan jin tare da kowane mutum ɗaya a duniya. Kana sa kowane burina ya zama gaskiya. Ina son ka, hubby!
Na kasance ina jiran mutum kamar ka tsawon rayuwa ta. Kallo daya ya ishe ni in kamu da sonka. Wannan soyayyar wani abu ne da ke sanya rayuwata ta zama kyakkyawar tatsuniya. Nagode da kawo tausayi sosai a cikin duniya ta.
Ina zama mafi kyawun sigar kaina lokacin da nake tare da kai. Shin ka taɓa lura? Lokacin da nake tare da kai, Ina jin kamar komai yanayiwuwa. Zaka zama babban jarumi na, baby.Ina son ka har zuwa cikin rai na.
Ina so in dauki lokaci don godiya da mamakin ka. Nasan cewa ba na yawan faɗin hakan ba, amma ina son ka har abada. Ban taɓa fuskantar wani abu makamancin haka ba. Nagode da kasancewar ka.
Kana bani nishadi lokacin da nake buƙatar hutu in ɓoye daga duniyar waje. Kana ba ni natsuwa, lokacin da na gaji da damuwa. Kana bani kulawa lokacin da nake buƙatar ɗan tausayi da kulawa. Kana ba ni duk abinda nake buƙata a wannan rayuwar, kuma ina fata ba za ta ƙare ba.
A duk lokacin da na ji kasala da bacin rai, nakan tuna cewa kana sona kuma ba zai taɓa yiwuwa a yi rashin farin ciki da kaunarka a lokaci guda ba. Kai ne kariya ta daga dukkan sharri da bakin ciki. Nagode da hakan, masoyi. Ina son ka.
Duk abinda ke cikin ka cikakke ne a gare ni. Ko da kana da wasu kurakurai, ƙaunata gare ka tana iya juyar da su zuwa babban fa'idodin ka. Wannan shine ikon ƙauna, kuma ina godiya a gare ka da kaka ba ni ita.
Sunan ka daidai yake da farin ciki. Siffar ka shine bayyanar kamala. Muryar ka shine mafi kyawun waƙar. Kuma tare mu ne hoton soyayyar kan ta. Nayi farin ciki da mun sami juna a cikin wannan duniyar.
Nayi imani cewa mafarki yana zama gaskiya. Ba da daɗewa ba nayi mafarki game da haɗuwa da ƙaunar rayuwata - kuma sai ga ka. Tare za mu sa mugayen mafarkan mu su zama gaskiya. Abunda muke bukata kawai shine muyi imani da ƙauna.
Ba kome ba idan ba kayi imani da kaddara ba, amma ina da tabbacin cewa mun haɗu da juna ne don dalili, Don sanya juna farin ciki da cancanta, Domin kawo zaman lafiya da jituwa a cikin zukatan juna, Don son juna a karshe kuma ba tare da sharadi ba.
Hanyar rayuwa cike take da kaifi da jujjuyawar ba zato ba tsammani, kuma ba za ka taɓa sanin tabbas abinda ke jiranka a can gaba ba. Nayi farin cikin gano wata taska ta gaske a bayan lanƙwasawa, kuma wannan taska kai ne. Nayi alkawari ba zan taɓa yin ciniki ko watsi da kai ba.
Duk lokacin dana rufe idona da daddare ina ganin fuskarka, Kanayi mani murmushi kana faɗin abubuwa mafi daɗi. Yadda nake fata abin ya faru a rayuwa ta gaske… Amma kai nawa ne, kuma ba zan taɓa yin shisshigi da shi ba, domin farin cikinka yana nufin duniya a gare ni, duk da cewa ba mu tare.
Baza ni taɓa daina son ka, domin kana bani karfin gwiwa da hazaƙa, zaman lafiya da lamana, dariya da farin ciki. Kana bani duk abunda nake bukata don samun ingantaccen rayuwa. Kuma a shirye nake da nasanar wa duniya hakan. ina ƙaunar ka.
Bana tsoron bayyana soyayya ta a ko ina, ko da ya kasance bai kamata ba. bana tsoron faɗa maka I love you, duk da cewan nasan baza ka faɗa mun hakan ba. Bana tsoron zama naka, duk da cewan kai ba nawa bane. So ta gaske bashi da bongo da iyaka, ana cin ta ne a cikin zuciya.
Rayuwar mu da ruhin mu sun haɗe sun zama yan biyu, na dogara ga kai, kuma kai ma zaka iya dogara ga ni. Yanzu muna da junar mu kuma mun fi komai kusa a faɗin duniyar nan. Ina fatan kar hakan ta canza.
Wani lokacin sai n bar soyayyar tana ratsawa cikin jiki na. Nakan ji shi ta cikin zuciya ta, jijiyoyi na, ruhi na, sai naji na maimaye da tsaro da jin daɗi. Ka sanya hakan ta yu, masoyi na. Kuma soyayyar mu, ina alfahari da ita har abada.
Na kasance mai tsaron faɗawa soyayya abaya, don akwai yu'uwar zata iya sani kuka. Amma yanzu komai ya zama daban. Ko da wani abu mummuna zata faru da mu, mu zamo bamu tare, ba zan taɓa daina son ka da kulawa da kai ba. Kasan da hakan.
Mutane na haɗuwa da juna su faɗa soyayya. Suna da mafarki da burin akan yadda rayuwar su zata kasance a tare. Amma kasan menene? Bana son cika tunani akan gabar mu sosai, saboda rayuwar mu yanzu tana da daɗin da ba zan iya daina shanawa ba.
Kai kaɗai ne nawa, kuma abunda nake so shine in zamo ta ka. Babu abu mafi zafi kamar ka barni. Don Allah ka faɗa mun zaka kasance tare da ni, idan ka tsaya, zai mayar da kai mutum mafi farin ciki a ban kasa.
Ya na kyau sosai mutum ya faɗa a soyayya, a rike wa juna amana, a faɗawa wa juna kalamai masu daɗi. Nasan yanzu muka fara kuma abubuwa sukan iya canjawa a ɗan kankanin lokaci.Amma bana son ma tunanin hakan. Cike nake da soyayyar ka da farin ciki, kuma ina alfahari da kai masoyi na.
Cin ka taɓa tunanin zamu yi aure wata rana mu fara zaman tare? Nasan ina ɗaukan komai da gaggawa, amma bana iya barci a ko wani dare, saboda mafarkin da nake yi akan tashin mu daga barci tare, yin karin safe tare, kallan fim tare a ɗakin mu... Waɗannan tunanin suna kwantar mun da hankali sosai.
Ban san ko mecece soyayya ba, amma duk lokacin da nake tare da kai, Ina jin ƙoshiya a ciki na. Na manta da duniyar, abunda nake tunawa kowai ni da kai ne. Menene ka mun ne? Ina jin na faɗa soyayya.
Zan so ace kana da wani karama, saboda ka iya ganin kanka ta idanu na. Domin ka fahimci iya burgewar ka a gare ni. Nagode da kasancewa tare da ni a duk wannan yanayin.
Akwai biliyoyin mutane a duniya, amma a ko wani yanayi zan so ka kai kaɗai. Kai kawai nake gani. Zuciya ta naka ne har karshen lokaci. Ina alfahari da samun ka a rayuwa.
Menene a duniyar nan nake yi kafin haɗuwar mu, na kasa tsammanin rayuwa ba tare da murmushin ka tana haska ka wuni na ba. Nayi matukar farin ciki da samun namiji irin ka.
Yin soyayya abu ne mai sauki domin ka zamo mai saukake soyayya. Ban san abunda nayi ba da Allah ya saka mun da kai ba, amma ina mai godiya da hakan.
Soyayya na bukatar mai da hankali sosai, wani zubin, samun karfin jure matsalolin dake cikin soyayya yana da wuya. Amma in don kai ne, masoyi, a shirye nake da in jajirce har karshe. Kai ne silar rayuwa ta, kuma bazan taɓa barin ka ba.
Bana son gobe idan har baza ka kasance da ni ba. Ko wani rana gare ni, yana da kyau ne don ka sa tayi kyau. Ka maida rayuwa ta mai inganci. Baby, ina son ka kamar hauka.
Zuciya ta tsare take idan naga kyakkyawar faskar ka. Natsuwar ka yana haukatar da ni. Yanayin maganar ka yana sa na fita daga cikin hayyaci na. Mu kasance a haka har abada.
Idan na kama ka kana kallo na, zuciya ta sai ta tsaya. Kana da wani abu mai dake kwantar mun da hankali yasa na shiga cikin tunani. Ina son wannan soyayya ta zama ta har abada.
Da na haɗu da kai da farko, nayi tunanin ba zan so ka ba ta ko wani hali. Amma ka dube ni yanzu, na faɗa zundum cikin soyayya da wanda na ɗauka a matsayin makiyi. Kai ne rabin rai na!
Kowai ina son tuna maka cewa babu wanda zai iya cike gurin ka. Yadda ka san hanyoyin sani dariya, yadda kake faɗa mun kana so na, na burgewa ne. Ina son ka, so ta hakika.
Besty, duniya ta tana haske idan kana tare da ni. Duk wani takun ka, duk wani motsin ka abun so ne gare ni. Kai babbar sirri na, kuma kai ne kwanciyar hankali na.
Ni da kai an halicce mune don kasancewa wa tare. Ina nan daram tare da kai daga cikin zuciya ta. Rayuwa tafi daɗi idan ina tare da kai. Mu kasance a tare, kar mu rabe.
Ban yadda farin jiki na zuwa cikin sauki ba. Sai ka jajirce da gaske. Nasan soyayyar mu ba wata mai kyau ba ce, kuma muna da matsaloli a cikin ta, Amma ina son ka, kuma wannan son ke bani karfin gwiwa da na ci gaba da koƙartawa.
Masoyi, nasan wasu lokutan mu kan yi gardama,kuma muna da matsaloli kamar sauran masoyan. Amma duk wannan ba shi bane, saboda soyayyar mu tana da karfi. Zamu iya maganta ko wani matsala kuma mu shawo kan ko wani damuwa idan har muna tare. Ina son ka. Har na ƙosa na gan ka.
A duk lokacin da zan hawo gado da daddare, Ina jin daɗi sosai saboda zan ganka a cikin mafarki na. Kasancewar ka da ni a mafarki ma ni'ima ne. Don Allah kar ka daina fito mun a mafarki na masu daɗi. Ina son ka!
Barka dai masoyi. Bana iya daina kirga mintoci a yayin da baka tare da ni. Komai rugurgujewa yake yi idan bamu tare. Hakan tana rikirkitar da ni. Ba zan taɓa saba da rashin ka a tare da ni ba.
A duk lokacin da nake tunanin ka, zuciya ta tana bugawa ta sauri. Ina cikin asirin ka kuma bata da alaman karshe. Bana ma fatahn zuwan karshen ta, saboda kai kaɗai ne a faɗin duniyar nan dake sani farin ciki.
Masoyi, ka san ina son ka har a lokacin da kake bata mun rai, ko saka ni kuka, banl zan taɓa daina son ka ba. Nayi alkawari!
Ina jiran ka, a lokacin da baka jira na. Ina tunanin ka, a lokacin da baka tunani na. Kuma nayi alkawarin zan saka ka a kebbaban wuri a cikin zuciya ta ko da ace ka daina so na.
Na tuna lokacin da kai ba komai bane a rayuwa ta, ban taɓa tunanin zaka zamo mutum mai mahimmanci a gare ni ba... Rayuwa tana da ban mamaki wasu zubin, zata iya haɗa mutane kamar mu, kuma zata iya raba su. Mu sa a ran mu cewan tamu bazata faru haka ba.
Ka ɗauke ni ka tafi da ni, ni taka ce. Nasan ba kada shakku akan hakan, kana shakka ne? Ka yadda da rabo da kaddara. Haɗuwa da kai kaddara ne, kuma kasancewa da kai rabo na ne.
Masoyi na, nasan kana tunani na idan bamu tare, nasan kai nawa ne, na ɗauka baza mu iya da juna ba, amma ka dube mu yanzu, mu zama ɗaya, kuma ban taɓa nadaman komai ba, saboda nasan kaddara ce ta kawo mu tare.
Ina son ka amini na, ban taɓa daina son ka ba. Idan mun samu matsala, idan muna nesa da juna, ban taɓa daina tunanin ka ba, kuma ban daina ƙaunar ka ba.
Ina anfani da kyawawan lokuta na da kai, ina godiya da hakan. Soyayya na da kai buɗeɗɗe ne tamkar rana, yana haskaka rayuwa ta.
Idan ina tafiya a hanya ni kaɗai, fatah na na isa zuwa inda nake zuwa. Amma idan ina tafiya tare da kai, sai inji kamar kar hanyar ta kai karshe. Ina ƙaunar ka a ko da yaushe.
Na faɗa cikin son ka gaba ɗaya ne. Ji nake kamar na faɗa cikin tarkon ƙauna, amma bana son a cire ni. Kaine duk abunda nake bukata a rayuwa. Kar ka bar ni, domin za nemo ka a ko ina.
Idan sakonnin ka na iso mun, ina kallon waya na sai in saki wata murmushi har sai an tambaye ni; lafiyan ki kalau? Lafiya na ba kalau ba man. Saboda soyayyar ka yana haukatar da ni.
Menene so, na fahimci nasan wannan amsar ne lokacin da na fara ganin fuskar ka. Na ɗauke ka tamkar duniya.
Idan babu abu mai dawwama, ta yaya zaka yi bayanin soyayya na gare ka? Nasan son ka yafi girman ko wani teku, kuma yafi dutse karfi. Kana sa na ji daɗin rayuwa yadda ya kamata.
Idan sako ya shigo waya na, addu'a nake ya zamo daga gare ka. Zuciya ta bugu take da sauri idan kana faɗa mun kana so na, kuma nasan kana kai ma kana so na.Don haka wannan tuni ne gare ka: Ina son ka. Kar ka manta da da haka.
Ka san ina mafarkin ka ko wani dare, ko? Ka cike mun tunani na, kuma yanzu ba zan iya dare ɗaya ba tare da kai ba. Kai komai nawa a rayuwa.
Ni taka ce har abada, ina son mu girma tare muga yadda zamu canza nan gaba. Amma ka san abunda ba zai taɓa canzawa ba? Soyayya na gare ka. Zata kasance da karfi har karshen lokaci.
A duniya da take cike da damuwa da ƙunshi, yana amfani sosai a sami wanda zai kawar da waɗannan damuwar. Kai mutum mai iya canza komai yayi kyau. Ina ƙaunar ka sosai.
Ba sai ka samar mun da duk abubuwan duniya ba, Abunda nake so shine kawai soyayyar ka marar karewa. Shi ne kawai abunda nake bukata.
Kai ba masoyi na ne bane kawai, kai aboki na ne, duniya ta, ban san yadda rayuwa zata zama ba idan babu kai. Saboda kai wani gaba ne na jiki na, kuma idan na rasa ka, na rasa wani ɓangare a jiki na. Haka soyayya ta gare takai.
Muna rayuwa cikin duniyar da mata basu da bukatar maza son rayuwa ba kuma. Amma ina bukatar ka kamar yadda nake bukatar iskan da nake shaka.
Ka san na riga da na gama shirya rayuwar mu nan gaba. Ko baka sani ba? Kai ne kawai abu dawwamamme a rayuwa ta, kuma zanyi komai don ganin hakan ya zamo zahiri.
A baya na rasa dalilin rayuwa. Amma sai ka bayyana. Soyayya da kai daban yake da yin soyayya da sauran mazajen duniya gaba ɗaya. Ji nake kamar kirji na zata fashe saboda ƙaunar ka.
Nasan yana da wuya ka gane irin tsananin son da nake maka, amma ya kamata ka yadda cewa kai ne mutum mafi mahimmanci a rayuwa na. Kuma ina alfahari da hakan.
Na tuna daidai lokacin da na faɗa soyayya da kai. Ina kallan ka da cewan kai ne kawai abunda zan bukata a duniya. Nagode sosai da kasancewa da tun waɗannan shekarun da suka gabata.
Ba sai kayi tunanin yu'u war bari na daga soyayyar mu ba. Domin barin ka tamkar cutar da kaina ne. Kai rabin raina ne. Ba zan taɓa barin ka ba.
Komin yaya na gaji ina samun karfin sauraren duk abunda zaka faɗa mun. Ni mai karfi ne idan akan ka ne.
Mutane suna tunanin komai ne zasu iya siya. Wannan ba gaskiya bane. Son da nake maka bata da farashi. Don Allah ka adana mun zuciya har karshen lokaci. Tabbas zan adana naka. Ina son ka yadda ban taɓa ba.
Ka san rayuwa takan zama abundariya. Wani rana rana kai bako ne a waje na, amma yanzu, kai duniya ne a waje na. Ba zan daina son ka ba saboda ni haka nake, ina da wuyar faɗawa soyayya, amma idan na faɗa, zanyi ta da gaske.
Nasan a soyayya ta ƙunshi koƙartawa daga masoya biyu. Amma a tamu soyayyar, ka ɗauki nauyin komai. Ina son yadda kake kula da ni. Allah ya bar mu tare.
Da na ji mutane suna faɗin so ruwan guba ne, sai na saki wata murmushi. Ba su sami wanda ya dace bane. Gaba ɗaya ka canza mun wannan yaddar.
A rayuwa na, bani da bukatar wani alarm, tunanin ka shine alarm ɗina. A ko da yaushe tunanin ka nake, menene kuma zanyi da alarm? Nagode masoyi.
Sou dubu idan za'a ajiye ka tare da wasu mazaje, zan zabe ka sou dubun. Zan iya yin komai saboda son ka. A rayuwa babu abunda nake son ji kamar muryar ka. Muryar ka magani ne a waje na.
A soyayyar ka nayi nisa, bana amsa ko wani kira in ba naka ba. Daga lokacin da muka fara soyayya, na riga nasan damuwa na da ƙunshi sun zo karshe. Kai ne mai kauda mun da damuwa, kaina mai sa ni farin ciki. Ina Alfahari da kai masoyi.
So ta gaskiya, na sha kowai a cikin fim ake yin ta. Amma haɗuwa da kai ya koya mun wannan darasi. Yanzu nasan har ni zan iya soyayya ta gaskiya. Ina godiya masoyi!
Saboda tsabadar son ka, idan na tashi da safe, hotan ka nake fara kallo. Haka ma idan zan kwanta barci da daddare, hoton ka nake kallo. Bana iya jure rashin ganin ka ko da na tsawon minti ɗaya ne. Ina kewar ka abun ƙauna ta.
A koyaushe ina tunanin wane irin saurayi zan so. Daga karshe na sami amsata. Shi ne ma'anar kamala kuma mafi kyawun irinsa; KAI!
Idan da ace zan mutu yau, abinda zan roƙa shi ne in sake ganin ka. Don ganin kyawawan idanunka, don jin zurfin muryar ka, don numfashi cikin kamshin jikin ka sau ɗaya. Wannan shi ne duk abinda nake so.
Na kasance ban yadda da soyayya ba, domin ba zan iya samun wannan ji na musamman a cikina ba. Amma ka sa na ji wani abu da ba zan iya bayyanawa ba. Ina so in ci gaba da wannan jin har abada. Ina son ka kamar hauka, masoyi.
Kai kaɗai ne a duk faɗin duniya da nake so in raba siri na da mafarkai da shi. Menene ƙari, Ina so in raba rayuwa ta da gida na tare da kai. Ina so in ba ka ƙauna mai yawa kamar yadda zuciyata ta yadda, kuma ina fatan gaske cewa kai ma kana da irin wannan niyyar.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here