Kalaman Barkwanci a Soyayya
Akwai Kalaman na budurwa da saurayi akan shafin nan.
Kalaman Barkwanci na Budurwa
Kinsan meyasa nakeji a zuciya ta bazan iya rabuwa dake ba? Na farko, kina sani farin ciki, inbabu ke a rayuwa ta wacece zata sani cikin farin ciki? Na biyu, kina sani dariya a sanda nake cikin damuwa, inbaki nan wace ce zata sani hakan? Na uku, kina sani murmushi a sanda nake so nayi kuka, inbaki nan wace ce zata sani murmushi? Hakan yasa nakara sanin darajar ki a rayuwa ta. Irin wannan hadin turawa suke kira “perfect match”
Nasan kina tinanin in nafita ina kallon wasu matan, amma ina so ki cire wannan a zuciyar ki dan a zuciya ta baki da abokiyar takara. Babu abunda zai sa na kalli wata mace daban bayan ina da sarauniya irin ki.
Baya taba yuwa nayi tinanin wata mace bake ba. Zuciya ta taki ce ke kadai, ba wurin zaman wata bane. Duk da cewa ina wasu abubuwan da suke saki zargin cewa ina bin wasu a waje. Masoyiya ta, sonki nake bil haqqi.
Koda a mafarki ne bantaba samun budurwa da tasan sirrin rike saurayi kamar ki ba. Farko na dauka bansamu karbuwa ba amma yanzu kam kin shayar dani so zalla, farin ciki iya farin ciki, ga natsuwa wuce tsammani. Kinsan irin dadin da nake ji kuwa?
Masu bincike a kan so sunce “so ba’a iya ganin ta” Amma ni nagani kuma nasan yadda ake jinta a zuciya. Kuma ba’a ko ina naganta ba sai a idanun ki. Kulawan da kike nuna mun kawai ta ishe ni.
Zan iya yin shekaru ina misalta maki irin kyawun ki, amma inaso kigane cewa duk abunda nafada da baki bai iya bada cikakken misali akan kyawun ki. duk inna zauna nikadai sai nata murmushi cikin far’a da walwala amma babu wanda yasan dalilin hakan sai ni da zuciya ta.
Masoyiya ta, inaso kifadamun meyasa nakasa cire ki acikin zuciya ta? Kodai akwai abunda ke tsakanin ki da zuciya ta? Nidai bansani ba; abunda nasani shine ina kaunar ki kamar yadda shayi ke bukatar madara, kamar yadda waya ke bukatar batir yayi aiki, kamar yadda jikin mutum ke bukatar ruwa da iska dan rayuwa mai inganci. Nasan zakiyi tamtama sosai kan hakan.
Bantaba sanin akwai wanda ke saka mana ido ba. Yau ina zaune a kofar gida sai ga wani yazo ya same ni yana bukatar nabashi shawara akan yadda zai tafiyar da tashi soyayyar dan yana ganina cikin farin ciki a koda yaushe.
Yanzu nafara samun kwanciyar hankali kinsan meyasa? Abaya, ina yawan tinanin wani zai iya kwatar ki a hannuna, amma yanzu hankali na a kwance yake dan nasan babu wanda zai iya shiga tsakanina da ke. Hakan kawai ta ishe ni farin ciki.
Idan akace aljannar duniyar, ana nufin soyayyar dake tsakani na dake. Duk wani jindadi da farin ciki da mutum zai iya tinani, babu wanda bana samu a wurin sarauniya ta. Ga ta aminya ta ga ta abokiyar fada kuma.
Bantaba samun budurwa a rayuwa ta wacce take ganin duk abunda nayi daidai bane saida nasame ki. Duk da muna yawan fada a tsakaninmu, hakan baisa kin daina kula dani ba. Amma fa, kamar yadda nasa ba tonar fadan ki, hakan za’a cigaba. Sai kinyi hakuri da masoyin ki.
Kibar ganin ina yawan takura maki, ina yawan tonar fadan ki, bazaki san amfanin hakan ba sai a sanda kika fara kewa na. sai ajiki kina cewa wayyo baby na.
Irin son da nake maki ko, wasu lokuta har jina ke kamar zaman ki nake a wannan rayuwar, kamar yadda jini da ruwa suke zagayawa a jikin dan adam, hakan soyayyar ki je zagayawa a cikin jiki na kowani lokaci, duk safiya, rana, da kuma dare kafin na kwanta.
Sarauniyar rayuwa ta, wasu lokutan sai naji kamar na fashe soboda irin son da nake maki. Nakasa mantawa dake a cikin zuciya ta. Kinsan meyasa? Kujerar sarautar ki tana cikin zuciya ta.
Kamar yadda mutun ke jin tafiyar jini a jikin sa, haka nake jin soyayyar ki a jiki na, kamar yadda mutum ke jin yunwa, hakan zuciya ta ke muradin ganin ki, kamar yadda mutum ke jin kishi, hakan zuciya da kunni na ke son jin muryar ki.
Nasan wasu lokutan inna fara wasu abubuwan, duk da kina cewa in daina, sai naji nakasa daina wa. Kinsan meyasa hakan? Aduk sanda nake wannan abun farin cikin danake gani a fuskar ki kawai ta ishe ni farin ciki.
Abaya nayi tinanin mutun nasamun kwanciyar hankali na musamman so daya ne, amma yanzu kam na karya ta hakan yanzu. Kin nuna mun sabanin hakan. Nidai fatana wannan farin cikin dake tsakanin mu nakeso ta cigaba da wanzuwa har karshen rayuwar mu.
A duk sanda na bude baki na nace maki ina kaunar ki, bawai ina fada maki bane dan kisan ina kaunar ki ba, bawai ina fada maki bane danki kara yarda dani ba. Ina fada maki ne dan kisaka a ran ki cewa akwai wani saurayi na nan kece dalilin farin cikin sa kuma bazai so yagan ki cikin damuwa ba. Ki kulamun da kan ki.
Kinsan meyasa nake binki a baya kamar agwagwa? Soboda kinsa nayi abubuwan dana saka a raina bazan iya ba. Nayi abubuwan danake tsoron yi abaya. Kinsa nadai na fargaba akan komai kamar yadda nasaba yi abaya.
Ai nihin darasi na tattare da macen da tasan me ake nufi da kalmar so kamar ki sarauniyar su baki daya. Kamar yadda kowani namiji zai ce tashi budurwan tafi, amma ainda kike tasu taji kunya soboda sunzo gidan masu ita. bazasu iya ba.
Sai inji mutane suna cewa so nada zafi amma gaskiya banga alama ba. Soboda a dictionary dina babu kalmar zafi, bakin ciki ko damuwa acikin ta. A sanda ake tinanin kinyi abunda zai sa na guje ki ko na rabu dake, sai naji kamar alokacin na fara soyayya dake.
Da inzauna da wata har na tsowon rayuwa ta da na zauna da kena kwana guda, na gwanmace na zauna dake na kwana dayan da na zauna da wata wacce ba ke ba. Ni abunda nasani yanzu shine inbabu ke to babu farin ciki.
A duk sanda nafito waje daddare na kalli sama, tinanin ki kefado mun soboda hasken taurari a sama suna tina mun irin lokutan farin ciki da muka kasance tare da juna. Yau a gidan ku zan kwana, ko a gadon ki ko a zuciyar ki.
Kinsan meyasa nake so na rike maki hannu inmuna tare? duk inna rike maki hannu kikayi murmushi, sai naji kamar kema kin rike mun nayi murmushi. Kinga ahakan sai muce “life goes on”
Duk in aka tambaye ni yanzu a rayuwa ta akwai abunda nake so sosai wanda zanyi iya fada da iya karfin danake dashi nakare ta, sai nace eh ina da ita. sarauniyar zuciya ta, ai hakki na ne nakare ki.
Tinda nake yanke hukunci, bantaba yanke irin wannan hukunci bana kasancewa tare da baby na ba. bakomai yasa nayi hakan ba sai dan farin cikin da nake samu a wurin ki. kuma wannan hukunci dana yanke wa kaina bazan taba nadama akan hakan ba.
Nasan kina tinanin akan ko zamu kasance tare har tsawon rayuwa ko kuwa sabanin haka, inaso kisaka a ran ki cewa, duk rintsi duk wuya bazan guje ki ba.
A lokacin muna yara akace mana in kaga taurari na yawo a cikin samaniya daddare, ka kulle ido kafadi kudurin ka a zuciyar ka, wannan kudurin zai zama zahiri. Nayi hakan kuma kuduri na ya tabbata tunda nasame ki.
A duk tinanin danayi, banyi tinanin zan samu budurwa kamar ki wacce zata so saurayi iri na ba. Amma gashi kin share mun kokwanto. Duk darasi da kika koyamun yananan a zuciya ta babu abunda zai same su.
Wasu kan fara safiyar su duk rana da shayi ko coffee, wasu kuma chakuleti, ko kuma wani kayan makwalashe haka, amma kuma ni bayan natashi daga bacci bana sauka daga kan gado kafin tinanin ki ke zuwan mu. Tare dake na kwana a cikin zuciya ta, mun sha soyayya acikin mafarki na sosai.
Duk inna zauna dalilai nake nema akullin wanda zai sa nakara son ki fiye da yadda nake son ki. In yau nasami dalili guda daya nakara son ki, gobe nasami biyu, jibi nasami uku kinga soyayyar ki a zuciya ta zata karu sosai fiye da yadda kike tsammani.
Kinsan ba wani abu kwarara nake dashi dazan baki ba, amma dadan wadataccen abunda nake da shi, zan cigaba da faranta maki da shi matukar farin cikin da nake gani zai cigaba da kasancewa.
Alokacin muna yara, ana yawan bamu shawara muyi duk abunda zai kawo mana farin ciki da nishadi matukar bazamu shiga hakkin wani ba. A hakan ni yanzu na dauki farin cikin ki a matsayin abunda zai kawo mun kwanciyar hankali. Ina kaunar baby na.
Ance idan kana so kaga amfanin wasu mutanen a rayuwar ka, ka nisance su na wasu lokutan. Na gwada hakan kuma maganar gaskiya banji dadin hakan ba. Naji kamar an cire mun zuciya ta daga jiki na. Yanzu kam nasan matsayin ki a rayuwa ta.
Kamar yadda malamin boko baya rabuwa da alkalamin rubutu, kamar yadda dalibi baya rabuwa da takardar rubutu, hakan rayuwa ta bata iya jure rashin ki a kusa da ita.
Abokai na sun tambaye ni kina da mahimmanci a rayuwa ta? Sai nayi dariya nace masu, kamar yadda guduma yake da amfani a wajen alkali, hakan soyayyar ki take da amfani a gare ni.
Kasancewa tare dake kawai kan sani farin ciki mai dorewa. Ni yanzu banda wani dalilin bakin ciki. soboda ina cikin farin ciki.
Ina kaunar ki da duk wani karfi da izzar da nake da ita. Soyayyar ki kawai tana kara mun karfi sosai.
Bansan yadda akayi wannan rayuwar tabani kyautar abokiyar fada da kuma kawa wacce take kula dani ba. Abun mamaki anan shine duk abinda ake fada akaina baya damun ki.
Kinsan meyasa baki da wani namijin a rayuwar ki kafin ni, dan ke tawa ce ni kadai, sai yanzu nayi nasarar zuwa gare ki.
Ina da wata kuduri a zuciya ta, wannan kudurin itace kasancewa cikin zuciyar ki har karshen rayuwa ta. Zan iya fada da kowa harda ke din matukar zaki shiga tsakani na da zuciyar ki.
Kamar yadda jirgin sama ke gudu bayan ya tashi hakan nake jin soyayyar ki a cikin zuciya ta.
Kinsan yadda na dauke ki a cikin zuciya ta kuwa? Duk abunda ke samar ma rayuwar mutum da kwanciyar hankali, wannan abun nada matukar mahimmanci. Toh kamar hakan kike da mahimmaci.
Na riga da na siya bindiga na yanzu. Kinsan mene zanyi da ita? Duk wanda ya nemi ya dami rayuwar ki, kifada mun kawai. Nayi maki alkawarin daga wannan ranar bazai kara kusantar ki ba.
Murmushi…. Kinsan meke tattare da murmjushin ki kuwa? Koda mutun makaho ne, indai kika yi murmushi yasan cewa akwai mace kyakkyawa akusa dashi. Balle mu masu idon hangawa.
Jin muryar ki kawai alama ce ta jin dadi da farin ciki. Daga sanda nagan ki na fara ji a zuciya ta cewa yau zan wuni cikin farin ciki.
Yadda kike damuwa da mutane ne yasa nakasa samun sukuni dan ganin cewa nayi komai dan ki kasance tawa ni kadai.
Ilimin ki da kwazon ki suka zama musabbabin fara soyayya dake. Abun dai kamar wasa, amma gashi son ki ya maimaye mun zuciya ta.
Soyayyar dake tsakanin mu bazai taba chanzuwa ba. Mu masoya biyu ne wanda baza’a taba samun kamar su ba.
Na zauna nikadai nafara tinanin yadda rayuwa ta ta kasance dake a cikin ta, tin da muka hadu nafara wannan tinanin amma har yanzu bangama ba, kuma bazan gama ba yanzu. Ba yau ba , ba kuma gobe ba, ba kuma har abada ba.
Wasu na son zoben azarfa, zinnare, ko kuma gwal. Amma matukar kina kusa dani, bana bukatar komai dan kece komai nawa.
Yammata, ni saurayi ne wanda baida aikin yi. Ina da takardar certificate daga makarantar masoya. Ina da diploma a shashin kulawa da budurwa. Sa’an nan kuma ina da degree daga makarantar sanya farin ciki a zuciyar budurwa, dan haka nazo neman aiki wurin ki shin zan samu kuwa?
Bani so nagan ki cikin damuwa, dan hakan na tasar mun da hankali sosai. Aduk sanda na kalli fuskar ki kina dariya, babu abunda nake hangowa sai rayuwar mu tare a nan gaba.
Ina kaunar ki baby na. Kinsan abunda nafi so a wannan rayuwar ta wa? Kalma ta uku a wannan zancen gaba daya.
Aduk sanda nafara tinanin ki sai naji kamar bana da lafiya, kuma inna je asibiti su duba ni suce lafiya na kalau. Amma kuma ni nasan akwai abunda ke damuna, kuma soyayyar ki ce.
Muyi wata haramtacciyar aiki. Zanzo na sace zuciyar ki daga baya kema kisace tawa zuciyan. Kinji abar kauna ta.
Duk inna kwanta sai na rungume pillow dina nayi mafarkin ki, buri na itace nayi mafarkin na rungume pillow dina yayin da nake rungume ki. Ina kewar ki.
Ni ba mai daukar hoto bane, amma a cikin kwakwalwa na, ina dauke da hoton mu tare nan gaba a yayin da rayuwa ke mana dadi mu biyu cikin aminci.
Ina son taurarin dake sama. Amma kuma nafi kaunar taurarin da nake gani ta cikin idanun ki masu sa farin ciki da annashuwa.
Amma fa abban ki barawo ne ko? Dan ya sace gaba daya taurarin dake cikin sama duk ya saka su a cikin idanun ki.
Yau kam nasha wahala awurin aiki, duk sai nake jin gajiya sosai. Amma tinda nasaki acikin idanu na, sai nake jina kamar wanda ya tashi daga bacci yanzu nan. Kallo daya ya kori gajiya gaba daya. Kifadamun wani namiji ne baison irin wannan alherin.
Nasan akwai lokacin da zanyi abunda zai baki haushi, kuma zaki bukaci bindiga ko wuka. Idan da bindiga zakiyi amfani, toh karki harbe ni a kirji, dan kina cikin zuciya ta. In kuma da wuka zakiyi amfani, karki cire mun kai, dan idanuna ke suke so, kunni na, muryarki suke so, kuma hanci na kamshin ki suke son ji.
Kinsan ni namiji ne mai kyau, kyawu na yayi maki haka ko kuwa kina so naje nakara siyo kyau soboda nakara daraaj ta awurin ki. Nifa sai kyawu na tafi taki zan hakura.
Ina so ki shirya dan zamu je asibiti dani da ke, kinsan meyasa zamu je? Dan jikin ki gaba daya daga kai har kafafuwa cike suke da kyau wuce tinani. Ina kaunar ki masoyiya.
Kamar kwarkwata haka kike a kaina, ga takura mun da kike yi amma bazan iya rabuwa dake ba. Dan rayuwa ta bata cika sai da ke a cikin ta.
Kinsan menene? Masoyiya ta sarauniya ta, ina so ki bani arar sumbata daya tak, nikuma zanbaki ita ba adadi. Har sai kin gamsu kince ya ishe ki.
Haryanzu kina jin wannan yanayin da ake shiga asanda mutum yaga wani wanda yake so a ranar farko. To wannan yanayin nakeji aduk sanda na kalli fuskar ki. yaushe zanga abar kauna ta.
Jiya cikin fushi na dauki waya ta na bugashi da kasa soboda na laluba daga kasa har sama banga number ki acikin wayar ba. Kinga amfanin ta ta kare a hannu na. Sai a samo wacce zata dauki number ki acikin ta.
Kinsan wani abun ban dariya? Asanda wasu mutanen ke faduwa daga kan keke, ko machine, wasu kuma daga bishiya ko daga kan gini, na rasa inda zan fada sai dai nakamu da soyayyar ki. Zuciya ta babu ke, mazaunin kunci zata koma.
Duk safiya idan natashi daga bacci ban kira ki ba, sai naji kamar ana sukana, bakin cikin da bansan dalilin ta ba. Aduk sanda mukayi wasa, bana manta wannan lokacin.
Jiya bayan mun rabu dana koma gida sai nake tinanin irin zantukan da mukayi. Sai na fashe da dariya nake tambayar kaina inda ace nida ke bamu tare, da wannan farin cikin narasa shi kenan.
Duk inna kalli fuskar wata budurwan ba ke ba, sai naga kamar kece, duk sanda na kalli fuskar waya ta asanda ake kira na sai nayi tinanin ke ce, duk inna kalli bangon daki na sai naga kamar sunanki na rubu ce a jikin bangon dakin. Wannan bakomai bane sai zunzurutun soyayyar dake cikin zuciya ta kuma taki ce.
Agurin wakan soyayya, da M. inuwa, M. sharif, MKT one, Abdul D one, Umar sky babu abunda zasu nuna mun matukar sarauniya ta zan rera wa waka. Yanzu dai kifada mun wata irin waka kike so na rera maki danki kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Wasu suce nacika surutu, wasu suce ni shuru shuru ne, amma duk basu bane agabana, abunda ke gaba na kuma nakeso naga na cinma wannan burin itace na sace zuciyar ki, na kori duk wani wanda ke cikin ta, na kulle kaina ni kadai na zauna acikin ta.
Nasan zakiyi tinanin wasu abubuwan da nake fada, ina fadar su ne dan kawai na kwantar maki da hankali, amma fa abar maganan wasa a gefe, zan iya siyar da gidan babanmu matukar hakan zai saki farin ciki. Zan iya komai don cin galabar zuciyar ki fa.
Na tina lokacin muna yara, burin mu duk in ana ruwa mushiga muita wanka acikin ta. A zane mu amma hakan bashi zai hana mushiga cikin ruwa ba gobe. Irin wannan dadin da muke ji a wannan lokacin bai kai na nishadin da nake samu ba a wurin ki.
Ni tinda kika furta cewa kina sona na daina shiga cikin kunci, nakoma kaman daushe, babu ruwa na da abunda mutane suke cewa akaina. Nidai soyayya da ke tafi mun komai.
Nifa banganin akwai wanda zai iya shiga tsakanin mu dake. Ko ma yayi yunkurin hakan kunya kawai zai sha. Dan kuwa nidake muta karaba.
Akwai wani mawaki a wata wakar say ace “zan iya komai akan son ki, zan iya komai kib ani kauna” nasha zuba kawai yakeyi, nayi tinanin baisan meke damunsa bane, she ni daban fara bane bansan komai ba. Amma yanzu kin shayar dani so zallar kuma na gamsu da me ake nufi da so ta gaskiya.
Ina son ki fiye da yadda kwakwalwan ki zai iya misaltawa, fiye da adadin jijiyoyin jikin ki, fiye da adadin jinin dake jikin ki. Amma ni bansan irin son da kike mun ba. Sai ki gayamun nima naji dadi kamar yadda kema kike ji.
Inaso ki kalli cikin idanu na kifada mun mene kika gani, kuma kada kice mun kwayan ido kika gani. Ni nasan babu abunda zaki gani face idanuwa cike da far’a da kuma walwala kuma ke ce silar haka. Nakusa kulle ki, na killace ki, na hanaki fita gaba daya, soboda banso kina fita wasu samarin naganin ki dan zasu iya kamuwa da sonki cikin sauki. Kinsan ke kyakkyawar budurwa ce.
Wata rana na nan zuwa; ranar da zanbaki mamaki, zaki fara tinanin wannan naki ne ko wani daban. Zan nuna maki irin kulawar da baki taba fuskanta ba, zallar so irin wacce baki taba ganin ta ba, girmamawa irin wacce baki taba zato daga gareni ba. Wannan alkawari ne.
Kinsan wani abu? Ni namiji ne wanda ke san tatsuniya matuka. Zanbaki wata tatsuniya amma sai kinyi alkawarin nima zaki bani labarin soyayya.
Amma meyasa baki taba tambaya ta akan mene manufar soyayyar mu ba. Kodai baki son gani na a rayuwar ki nan gaba? Karki damu fa, wasa nakeyi nasan kina so na kuma ni shaida ne.
Duk idan aka tambaye ni wani lokaci nafi jindadin kasancewa tare da ke? Sai nace masu yanzu da kuma har Abadan abaada.
Gaki fara kamar yadda kike da far’a, gaki da ilmi, baiwa, sanin kimar mutane amma saidai akwai tonar fadan masoyin ta.
Kizo mutafi wani gari da ake ma lakabi da garin masoya. A wannan garin babu abunda ake fuskanta awannan garin face farin ciki da nishadi, babu bakin ciki, babu shiga damuwa. A wannan gari zamuyi abubuwa daban daban, wasanni wanda zamu kara wa soyayyar mu karfi.
Gashi bamu tare da juna amma kuma gani nake kamar kina gaba na. Ina so kisani cewa duk tazarar dake tsakanin mu bazai sa namanta lokutan da muka kasance cikin farin ciki dake ba. Wannan kulawa ai yayi mun yawa. Kina koyamun shagwaba fa!
Haryanzu nakasa yadda cewa nakara wuni daya bangan ki ba. Gaskiya zan kai karar zuciyar ki kotu a bimun hakki na, zuciyar ki tanaso tasa tawa zuciyan ta buga kuma bazan yarda da hakan ba. Ina kewar ki sosai.
Nasan kinsan kowani mutum a wannan rayuwan yana da burin da yake so ya cinma. Nima haka nayi nasarar cinma nawa burin, kuma saki dariya matuka a sanda kike cikin tinani shine wannan burin ta wa.
Mama na da baba na sunce na gayyato ki kizo kici abinci koda sau daya, amma ni kuma ina son hakan ta kasance har abada. Bara nayi maki bayani; inaso kizama sirika a wurin su, ni kuma kizama rabin rai, kizama aminiyar zuciya ta da kuma mata ta.
Bara nafada maki abinda ke cikin zuciya ta, kullin idan natashi da safe, jinake kamar nazo gidan ku na rungume ki, na sunbace ki dan hankali na ya kwanta sai na koma gidan mu, washe gari ma nasake hakan, hakan ya cigaba da faruwa har karshen rayuwa ta.
Kyawun ki kawai na ajiye ni cikin dare naita tinani akan ki. Ni yanzu na maida tinanin ki tamkar aiki na. Himma ta cike a cikin tinanin ki. Zuciya ta tace nace dake kizo ki zauna a cikin ta. Ta dade tana jiran ki.
A lokacin da mutane ke jin sanyi sosai, kinsa babu abinda nakeji face dumi. A sanda kowa ke jin zafi, kin sa babu abunda nakeji face iska mai kwantar da hankali, da sa natsuwa a zuciya.
Nasan in kina gida ke kadai babu me tayaki aiki a gida. To ina so ki kirani da safe nayi maki wanke wanke, sai nayi maki karin safiya, da rana kuma nasaka ki dariya bayan mundafa abinci munci tare. Daddare kuma na ajiye maki hannu na ki kwanta akansa. Bazan bar gidan ku ba, sai na tabbatar kinyi bacci.
Wani aboki na ya kalle ni yace dani dankwali yaja hula. Nace masa babu komai tinda dankwalin na tattare da farin ciki. Na tabbatar masa da cewa ke ce dalilin farin cikin dake cikin zuciya ta.
Ina so soyayyar dake tsakani na dake tazama kamar soyayyar dake tsakanin turmi da tabarya, tazama kamar soyayar dake tsakanin mota da kuma man fetur. Kinsan daya bazai iya kasancewa ba inbabu daya.
Daga randa na kasance tare dake na tina wanene ni, nasan abunda zuciya ta take so, nasan mene ne yakamata nayi ma abar kauna ta taji dadi.
Kinfi kalmar karfi; karfi a cikin zuciya ta. Ni yanzu nadai na gane komai matukar babu ke a cikin ta.
Na fada cikin yanayin soyayya, kizo ki shayar dani dan na koshi nasami labarin da zan ba ya’yan mu nan gaba, su san karfin da mahaifiyar su take da ita.
Kalaman Barkwanci na Saurayi
Masoyi na farin ciki na, ina so nafada maka wata sirri; soyayyar ka tazamo tamkar ruwan dake cikin kogi, dan haka kishi nake ji ka shayar dani da ita dan nasami kwanciyar hankali.
Hubbi na, dan Allah ina neman wata alfarma a wurin ka dan nasami kwanciyar hankali. Bansani ba ko kana da zuciya biyu dan na karbi daya soboda soyayyar ka ta sace mun zuciya. Jina nake kamar wanda bai taba shiga damuwa ba.
Gaskiya akwai abunda ke damun idanuwa na wanda bansan dalilin hakan ba, mene ne yasa bazan iya cire idanuna daga naka ba duk sanda muka hadu? Meyasa zuciya ta take muradin ganin ka a kusa da ita?
Kamar yadda takaddar dictionary take dauke da ma’anar kalmomi haka soyayyar ka take kara wa rayuwa ta ma’ana. Bana bukatar na tabbatar da hakan dan duk wani sheda da zan nema nagan ta a idanun ka.
Amma in tambaye ka wani abu guda daya mana, anya bakayi mun asiri ba kuwa? Duk sanda tinanin ka yazo mun komai nake mantawa. Komai ficewa yake duk sanda nafara tinanin ka. Sai naji kamar gaka a gaba na.
Soboda kai, duk ranar rayuwa ta sun kasance wanda ko wacce mace ke marmarin samu a rayuwar ta, ka sa duk dare a rayuwa ta sun kasance tare da mafarki, farin ciki gaba da baya a rayuwa ta.
Baka san wani abun al’ajabi ba, duk sanda nayi tinanin nisantar da zuciya ta daga tinanin ka, sai naji tamkar a ranar na fara sanin ka. Sai naji duk na kosa nagan ka. Wannan wacce irin yanayi nakeji a cikin zuciya ta. Kaima haka kakeji akai na?
Murmushin ka mai matukar kayatarwa shine dalilin da nake kasancewa a cikin farin ciki a wannan duniyar da muke ciki ta masoya. Idan banda lafiya, bana bukatar komai sai murmushin ka, idan ina jin yunwa, murmushin ka kadai ta isheni, murmushin ka na share mun hawaye a sanda zuciya ta ke kuka.
Tinda na hadu da kai a rayuwa ta, ban riga na shiga cikin damuwa ko bakin ciki ba. Babu wata rana da zata wuce banyi tinanin ka da marmarin ganin ka ba. A duk sanda kake zolaya na ko kake bani lambar yabo, sai naji ni tamkar nazama sarauniya.
Idan ina tinanin wani abun daban a cikin zuciya ta, tinanin ka na zuwa sai ya kori tinanin da nakeyi, amma kuma duk sanda nake tinanin ka, babu wata tinanin dake zuwa mun a wannan lokacin. Idan kana wuri har kasa natsuwa nake.
Naga abubuwa daban daban, na hadu da mutane iri iri, amma mutum mai irin zuciyar ka bantaba gani ba. Kafi fifita ni fiye da yadda kake fifita kanka. Wai shin menene matsayi ta arayuwar ka.
Wasu lokutan sai nazauna nai ta tinani akan sunan da zan ringa kiran ka da ita, amma abun mamaki anan shine duk sunan dana zaba, zuciya ta bata kwanciya da ita, amma kuma yanzu nayi shawara da zuciya ta kuma ta yarda na kira ka da “mamallakin ta “ dan haka daga yau zuciya ta tazama taka.
Wani abu dake sani cikin farin ciki a kullin shine, duk wani hali ko abubuwan da nakeso a wurin saurayi, duk kana da linkin hakan amma nasan bazaka fahimci hakan ba yanzu. Kaine saurayin dana dade ina gani a cikin mafarki na kuma gashi mun hadu a zahiri.
Ance soyayya na tsufa, amma gashi kullin sai kara son junar mu mukeyi, sai dai kuma ni nafi sonka fiye da yadda kake sona. Kaina bai daukan lissafi abaya, amma soboda lissafi danake yi akan rayuwar mu gashi nazama gwana a fannin lissafi.
Ina so na kara gode ma kan wani abu guda daya, duk da farko ina jan ma aji, ka cigaba da bibiya ta duk inda na shiga. Baka yi kasa a gwiwa ba dan ganin ka siye zuciya ta, hakan ya nuna mun kana sona ne ba dan komai ba sai dan farin cikin da kake nema a zuciyar ka, kuma namaka alkawarin samar da ita gwargwadon iko.
Na kasance sauri ba zuwa, banda wani manufa, banda wani buri, banda wani abu na azo a gani, amma kallo daya kawai na saka burin kasancewa tare da kai, na sanya wa kaina manufar sanya farin ciki a zuciyar ka, kuma nafara yin nasara akan hakan.
Wasu lokutan inna zauna a gida, sai na fashe da dariya. Duk in aka tambaye ni mene ne ke damuna sai nace masu kar su damu dani. Amma kuma ranar da muka fara haduwa nake tinawa. Irin abubuwan da ya faru tsakanin mu. Wannan yanayin ba abun mantawa bane.
Kabani soyayya, kabani kulawa, kabani damar kasancewa cikin nishadi, da hikimar ka, ka san ba wata abunda nake buri kamar soyayyar ka a gare ni. Soyayyar ka ta riga ta bani duk wani abu da nake nema a wannan rayuwar.
Kasan wani abu guda daya, kashigo cikin rayuwa ta a lokacin da nake bukatar agaji, lokacin da nake neman abokin fada, nake neman wanda zan ringa tonar fadan su, wanda zan nuna nace ga masoyi na, ga habibi na kuma na same ka cikin kyaptawar idanu.
A duk sanda ka rike mun hannu kace mun kana sona, babu abunda zuciya ta ke fada mun face babu abunda zai iya shiga tsakanin mu koda ace mun shiga cikin wata hali. Nidai zuciya ta tana samun natsuwa ne a sanda take tare da kai. Kuma irin wannan yanayi na soyayya itace muradi na.
Duk sanda nake cin chakuleti, duk sanda na balla nasaka a baki na sai naji kamar duk balla tafi dadi. Toh haka soyayyar ka take, kullin sake muradin ganin ka nake yi. Amma nasan bazaka fahimci hakan ba. Ina sonka habibi na.
Wannan wani iri soyayya ce, duk safiya da kai nake tashi a cikin zuciya ta, duk dare, da kai nake kwana a zuciya ta, duk rana, banda wani aiki face tinanin ka, tinanin yadda goben mu zata kasance, farin ciki a tsakanin mu nake fata.
Soyayyar da nake maka tafi teku girma, tafi teku zirfi, tafi teku fadi, tafi adadin ruwan ta yawa. Bazai iya misaltawa. Kuma idan kanaso ka tabbatar da hakan, ka kalli cikin idanu na kaga yadda soyyayar ka ta samar ma kan ta wurin zama.
Duk sanda kayi mun kyauta, gani kake kamar kabani karamar abu, amma wannan abunda kake kira karami ya nuna mun matsayi na. Duk sanda na tina da wannan abun sai naji ina muradin ganin ka. Amma kasan meyasa nake so na ringa ganin ka a kusa dani? Ina son saurayi mai yawan sani dariya kuma ka riga ka nuna mun hakan.
Rayuwa ta ta kasance kamar lambu ne cike da fure iri iri masu kyan gani, amma akwai wata fure guda daya da duk wanda ya shiga wannan lambun soboda kyawun ta, da kalar ta, da kuma farin cikin da take sama idanu. To kai ne wannan furen a cikin zuciya ta.
Bana bukatar komai daga gare ka, kai ne wanda nake bukata. Ka rike hannu na mu tafi tare duk inda zaka. Ina so kayi mun alkawarin bazaka taba kyale ni ba. Zan iya kare maka fada fiye da yadda zaka iya kare kanka tunda nasan baka da karfi. Rayuwa ta na masifan son ka acikin ta.
Daga randa ka shiga cikin zuciya ta, zuciya ta ta kasance kullin cikin farin ciki da kwanciyar hankali soboda duk sanda na shiga damuwa, akwai wanda zan kaima kuka na, wanda zai share mun hawaye na, ya sani murmushi, ban taba tsammanin zan samu namiji irin ka a rayuwa ta ba.
Masoyi na haryanzu kana fushi da nine? Ka dai san nikadai ce wacce take iya fada da kai kuma tazo ta samar maka da farin ciki. Idan banyi fada da masoyi na ba, dawa zanyi fada, waye zan zolaya? Kai kadai ne kawai zan iya ma hakan.
Koda sau daya, ban taba jin soyayyar ka ta ragu a cikin zuciya ta ba. Duk gasan danayi da zuciya ta akan ka sai na fadi, amma meyasa zuciya ta ke son kasancewa tare da kai.
Bansan me nabaka da ya saka kake so na haka ba, har na fara tinanin anyi mune dan ju na, dan mu kasance tare har karshen rayuwar mu cikin aminci da farin ciki. Natsuwa da jindadi shine abunda muke fatar samu tare.
Kamar yadda rana take haska wannan duniyar da muke ciki da rana, haka murmushin ka ke haska zuciya ta. Ni yanzu koda an bata mun rai a gida bana damuwa kwata kwata soboda ina da mai sani murmushi a kowani lokaci. Hakan ma ai farin ciki ne.
A duk sanda nayi kokarin hukunta zuciya ta da rashin ka acikin ta, bana samun kwanciyar hankali har sai na nemo mata kai. Bandai san mekayi ma wannan zuciyar ba da take son ka a acikin ta.
Kamar yadda baza’a iya raba ruwa da sugar ba a duk sanda aka hada su tare, haka soyayyar mu take. Mai raba ni da kai zai ji kunya duk da irin shirin da yayi. Zuciya ta mutum daya ta sani kuma kai ne.
Kamar yadda babu wanda yasan adadin halittun dake cikin teku sai ubangijin daya hallice su, haka zalika babu wanda zai iya misalta irin kaunar da nake maka a wannan rayuwar. Kabani kwakkwarar dalilin kasancewa cikin farin ciki.
Masoyi na kasan wani abu kuwa? A kullin in na kalli fuskar ka, sai naga kamar kana kara kyau kullin. Ga shawara gare ka, kazama mai yawan murmushi dan murmushin ka magani ne ga masu bukatar kwanciyar hankali.
Gaskiya irin yanayin da nakeji yanzu ta musamman ce ba kamar ta baya ba. Koda ina cikin bakin ciki babu mai cewa komai sai dai suyi mun dariya. Amma gashi cikin wuni daya ka chanza komai a rayuwa ta. A tarihin rayuwa ta kai ne kan gaba.
Nayi dacen samun farin ciki kamar yadda muka rabauta da samun rana dan samun haske, kamar yadda muka rabauta da samun wata dan haskawa daddare a sanda babu rana. Kamar yadda muka rabauta da abinci a sanda muke jin yunwa.
Wai haryanzu fushi kakeyi dani? To inaso na sanar da kai wani abu guda daya, nida kai babu kalmar rabuwa a zahiri da badinin rayuwar mu.
Inaso na fada maka wani abu guda daya sai dai bansan yadda zaka dauki maganar ba; ka shigo cikin rayuwa ta kabani duk wani abunda nake muradi, ka karfafa mun gwiwa wajen samun abunda nake buri. Soboda haka nima inaso ka kalli cikin idanu na kafadamun a bunda kakeso nayi maka.
Masoyi na ina so ka zabi daya daga cikin wadannan sunayen, masoyi, habibi, hubby, sarki, mai gida, babyn baby, hayatii. Nasan duk basu maka ba, amma sai ka zabi daya.
Ni yanzu na riga na shirya takura maka masoyi. Nayi kokarin na kyaleka, sai dai kuma zolayan kara yawa yakeyi. Kuma zanyi maganin ka matukar baka daina ba. Amma duk da haka ina son ka.
Na daukar maka wani alkawari guda daya, na soka kamar yadda nake son kaina. Kuma nafara cika wannan alkawarin.
Wai tawani siga zan iya bayyana maka irin son da nake maka? Naga kamar baka fahimtar abunda nake nuna maka. Kada na fusata fa.
Kasan meyasa koda kayi abun haushi baya damu na? Soboda duk abunda kayi yanzu, anjima zakazo kana bani hakuri.
Bansan ya akayi ba, bansan ta wata hanya ka shigo cikin zuciya ta ba. Dan haka inaso na sanar da kai cewa tinda kashiga zuciya ta na fara samun farin ciki mara adadi.
Kai kadai kasan ta hanyar da ka shigo cikin zuciya ta, kamar yadda kayi iya bakin kokarin ka dan shiga cikin ta, nima zanyi bakin kokari na dan hanaka fita daga cikin ta.
Ba idanu na kadai bane ke san ganin ki, duk wani gaba a jikina nasan kasancewar ki kusa dasu; soboda su samu salama.
Tunda na kalle ka nasan cewa nasami wanda aka halicce ni soboda shi kuma zanyi duk abunda yakamata nayi dan mallake ka.
Na nemi soyayya sai na sameka, tun daga nan kuma rayuwa ta ta dawo dai dai.
Inason ka soboda kana sani kara son ka kullin. Kazamo tamkar aminiyar dana rasa. Ka share mun hawaye.
Inaso na kasance tare da kai yanzu, anjima, yau, gobe, gata, a kowani lokaci, zuciya ta kai take bukata.
Bana kaunar muna tare da kai abokan ka suzo su dauke mun kai. Banaso komai ya shiga tsakani na da mai sani farin ciki.
Ita lamarin so tana faruwa ne kamar siddabaru, sai dai kuma duk inda take, mazaunin farin ciki ne kuma na rabauta da samun wannan yanayin wanda yake abun marmari.
Ni yanzu na dai na shiga damuwa kwatata kuma kaine musabbabin hakan. Ka taimaki rayuwa ta matuka, bazan taba manta ka ba.
Babbar ma’anar rayuwa a wuri na itace soyayyar dake tsakani na da kai. Duk komai nawa ta musamman, akwai ka a cikin ta.
Bana tinanin akwai wani abu da zai faru a rayuwa ta yanzu babu kai a cikin ta.Yanayi na jindadi, natsuwa, ko sabanin hakan. Inason ka.
Ina fushi da kai kasan meyasa? Soboda jiya bangama ganin fuskar ka kafin tafi ka kyale cikin kewar ka ba. Kuma zanrama nima.
Yanzu zuciya ta tana bugawa cikin salama, kwanciyar hankali soboda tasame ka acikin ta. Ka samar mata abunda take nema.
Wannan wani irin siddabaru kakeyi haka, a kallo guda daya ka sace zuciya ta, tunda nagan ka ban kara samun natsuwa ba har sai da na same ka.
Ga wasu kalmomi guda uku masu dadin fada, burin kowani masoyi afada mai ita, kunnuwa suji ta, baki ta fade ta, kuma zuciya taji dadi “INA SON KA”
Ni yanzu babu abunda nakeso a rayuwa ta kamar na kare rayuwa ta da kai a cikin ta. Masoyi na kaima kana jin hakan kuwa?
Kasan wani abu? Ka cigaba da so na kamar yadda kakeyi. Irin wannan yanayin ita nadade ina nema. Ina matukar kaunar ka.
Inaso kayi mun wata alkawari guda daya; bazaka kara kallon wata mace ba sai dai ni kadai. Bazan iya jurar ganin wata mace a kusa dakai ba ni ba.
Karka kara mun magana, wannan kalmar a gun wasu akwai dadin ji, sun dauke ta wasa. Wannan kalmar tashin hankali ne a wuri na. ni taka ce.
Komai a rayuwa za’a iya sabunta shi amma banda wani abu guda daya mai mahimmanci, soyayyar ka. Bana wasa da duk wani abunda ya shafe ka.
Jiya ni taka ce, yau ni taka ce, gobe ni taka ce haka zalika zan cigaba da kasancewa taka kai kadai har karshen rayuwa ta.
Nazamo kamar mafarki a rayuwar ka, kai kuma kazama kamar bacci ne a rayuwa ta. Kaga komai yazo dai dai, hakan na nufin burin mu zai cika tunda dukkan mu muna tare.
Ni yanzu ban yawan damuwa dan bana kusa dakai. Tinanin ka kawai a zuciya ta nayaye mun damuwa sosai. Bana so ina kewar ka.
Zan iya siyar da wannan jihar dan samu dukiyar da zai sa mu more rayuwar mu cikin aminci. Duk abunda ke kawo maka farin ciki abun muradi ne. ina alfahari dakai.
Nakasa banbance tsakanin farin ciki da kwanciyar hankali, narasa wanne nake ciki, amma kuma zaifi dacewa ace muna tare sai ka fayyace mun komai ta sigar soyyaya.
Inaso na nuna maka irin soyayyar da nake maka. Zanje na kwanta a tsakiyar hanya soboda babbar mota tazo ta takani a kafa matukar hakan zai nuna maka matsayin ka a raina.
So akace makaho ne, shiyasa nake bukatar farin cikin ka soboda nima nawa zuciyan ta haskaka dan nasami haske wadatacce.
Soyyayar ka ta fara ramar dani bansan meyasa ba. Zai iya kasancewa yawan tinanin ka ne yakawo hakan. Amma ina bukatar ka samar mun da natuswa dan nakara kiba.
Inaso kafada mun a cikin numbers kafada mun wanne kafi so sai nafada maka sirrin dake tare da wannan number. Zan nuna maka ni yar’ baiwa ce.
Inda ace zan iya yin asiri, maganin bata kawai zanyi soboda duk sanda nafara kewar ka sai nazo inda kake na rungume ka sai na koma. Hakan dai yayi ko?
Gani nake kamar ni ta daban ce a cikin mata. Duk wani buri da nake dashi a rayuwa ta na kasancewa tare da saurayi wanda yasan shika shaken soyayyar ya cika yau. A masarautar zuciya ta, kai ne na farko a cikin ta.
Ga sako daga zuciya ta gare ka masoyi na, ina kaunar ka. Kauna wacce ba’a misalta ta sai dai a jita a cikin zuciya. Nidai tare da kai, nasami mafaka.
Yau na tabbatar da kasancewa ta acikin zuciyar ka ta cikin idanun ka. Kana cikin rayuwa ta dari bisa dari babu ragi sai dai kari. Ta dalilin ka nafara sanin mene ne kauna.
Nagode da wannan so na da kayi a sanda nayi tinanin narasa ka. Amma ka share mun hawaye, jinake kamar ni da kai an haifo mu da manufar mu kasance tare. Ka cigaba da kula da ni, kaji?
Wani abu ne ke bani mamaki, yau natashi da safen nan tare da tinanin ka a cikin zuciya bayan nagama mafarkin ka cikin dare, amma kuma sati daya baya bamu hadu da juna ba. Ina son na tinatar da kai wani abu, ina son ka.
Ina so kasani cewa babu wanda zai iya miye gurbin ka a cikin zuciya ta. Yadda kake shigar ka, yadda kake runguma ta a sanda nake bukatar ta tasa ka siye zuciya ta nan take. Gata nabaka kyautar ta.
Naje aiki nagaji sosai yau, sai gashi daga shiga daki ka kirawo. Yanzu haka wannan gajiyan dana dauko daga wajen aiki na manta shi yanzu. Zuciya ta ta samu irin saurayin da take muradi.
Kina sani dariya a sanda nake kuka, kina sani murmushi a sanda raina yake a bace hakan yasa na saka a zuciya ta cewa ko da ace mun rabu da kai bazan taba manta lokuta na farin ciki tsakani na da kai ba.
Soyayyar da ka bani bazai taba tsufa a wuri na ba. Kasan meyasa kullin kara son ka nake yi a cikin zuciya ta.
Nifa kalmar ina son ki, ina kewar ki, ina son ganin ki ban wani dauke su da mahimmmanci ba matukar baka kyauta ta hakan. Idan kana sona kanuna mun kana so na bil haqqi.
Bai kamata na jira sai ranar zagayowan ranar haihuwar ka ko zagayowar ranar da muka kasance tare ba kafin na bayyana maka irin son da nake maka. Ina son ka tamkar yadda jikin mutum ke bukatar iska dan rayuwa.
Masoyi. Ni yanzu son ka ya riga na bi jiki na. Ban tinanin zan kwana daya batare da na saka ka a ido ba.
Ka shigo cikin rayuwa ta a sanda nake bukatar wanda zai sani farin ciki. Zuciya ta bata samun sukuni soboda bataso ta kara shiga cikin halin da ta shiga kafin haduwar mu. Zaka rike mun amana ta?
Yanzu munyi shekara daya tare da juna amma a wannan shekaran tamu, babu wata rana dana taso ba tare da jindadin kana rayuwa ta ba acikin su wannan kwanaki 365. Allah mai iko!
Ina godiya da kasancewar ka aboki, masoyi, amini, sadauki da kuma baby na. Ina kaunar ka.
Zai iya yuwa bani bace irin budurwar da kake so, amma ina tabbatar ma da cewa zan soka fiye da yadda wata mace zata so ka a wannan duniyar.
Wasu lokutan sai na zauna naita tinanin nan gaba a rayuwar mu tare da juna ya zata kasance? Nidai babu abunda na hango a cikin ta sai nishadi.
Tun daga ranar da nafara ganin ka nake ta muradin kasancewa tare da kai a wannan duniyar. Sai dai kunyar ka nake ji a lokacin nakasa sanar da kai. Amma ina fatar yanzu ka gane hakan.
Abun dariya ne akace a rayuwar ka kana tinanin komai dai dai bayan baka da mace a gefen ka, nima sai da na saka ka a zuciya ta na fahimci hakan.
Kowa dai yasan candir daga sanda ka kunna mai wuta yake fara ci har sai yakare, to wadanda da basu son ganin mu tare haka zasu zauna suna kallon mu yayin da muke kone duk wani matsalar dake tsakanin mu.
A sanda nake tinanin ka, duk wani kalma na kwantance tazamo mai amfani ga kunnuwa na. Zan iya haukacewa idan har bansame ka ba.
Ina ganin namiji mai burika dawa a zuciyar sa kuma ina so na kasance tare dashi wajen ganin ya cinma wadannan burin gaba daya. Habibi na shine farin ciki na.
Wasu lokutan jinake kamar nayi shaye shaye idan ina tinanin ka. Murmushi kawai zan tayi marar karewa. Har anfara samun ido a gidan mu.
Kabani kwarin gwiwa da kuma saka ni na gane kaina, na yarda da kaina, nasan wacece ni. Ina godiya da wannan karfafawa irin taka masoyi na.
Bara nafada maka wani abun da bantaba fada wa kowa ba; duk tsakiyar dare sai na farka dan na kara godewa Ubangiji daya hada ni da kai. Nidai ina kara maka fatan nasara a rayuwa. Ina kaunar ka baby na.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here