Yadda Ake Soyayya Zalla (Mace da Namiji)


Soyayya ruwan zuma. Masana soyayya sunce rayuwa kamar fure take, yayin soyayya ta zama zuma a gare ta. Kasancewar mutum nada mai tsananin sonsa, hakan  yana ba ka ƙarfi, yayin da son wani kuma ke ba ka ƙarfin hali da kuma natsuwa. Mun fi rayuwa a cikin walwala lokacin da muke da masoya masu san mu. Soyayya ta wadatar da hakan, kuma abin da ba mu taɓa ba da isashensa ba shine soyayya na gaskiya. A matsayinka na saurayi ko budurwa mai neman sani akan yadda ake fara soyayya don zama cikakken mosayi ko masoyiya. Ku cigaba da karanta wa dan gane yadda ake fara soyayya!!

Menene Soyayya?

Soyayya wani tsari ne na motsin rai da ɗabi'un da ke tattare da kusanci, sha'awa, da sadaukarwa. Ya ƙunshi kulawa, kusanci, kariya, jan hankali, ƙauna, da amana. Soyayya na iya bambanta da ƙarfi kuma tana iya canzawa cikin lokaci.Yana da alaƙa da kewayon motsin rai masu kyau, gami da farin ciki, jin daɗi, gamsuwar rayuwa, da jin daɗi. Sanin menene soyayya na da mahimmanci, takan haifar da motsin rai mara kyau kamar kishi da damuwa.

Ita soyayya tana yiwuwa duka biyun ilimin halitta da al'adu suna tasiri. Ko da yake hormones da ilmin halitta suna da mahimmanci, yadda muke bayyanawa da kuma dandana ƙauna ya danganci tunanin mu na ƙauna.

Yaya Kuke gane soyayya?

Menene wasu alamomin soyayya? Masu bincike sun bambanta tsakanin ji na so da kuma son wani. wasu daga cikin wadannan alamomin sune:

 • Maƙele: Bukatar kasancewa tare da wani da son saduwa da fira ta zahiri 

 • Kulawa: Ƙimar farin ciki da buƙatun wani kamar na ku. 

 • kusancin ku: Raba tunanin sirri, ji, da sha'awar mutum tare da ɗayan.

 daga abubuwan dake taimakawa a soyayya sun haɗa da:

 • Kasance a shirye don gafartawa. 

 • A zamo masu bada haƙuri in anyi kuskure.

 • Ku zamo masu sauraro. 

Yadda Ake Fara Soyayya

Yadda ake fara soyayya na iya zama abun ban mamaki, musamman idan ba ku san abin da kuke tsammani ba. Amma babu wani abin tsoro - kawai ku mai da hankali kan kasancewa mai gaskiya da sanin yakamata tare da wanda da kuke so da soyayya.

Yadda Ake Fara Soyayya da Mace (Budurwa)

 • Kawai faɗi wani abu don jin daɗin tattaunawar: Yayin da kake jira don faɗin wani abu, da alama ba za ka iyi ba. Ba lallai ne ka faɗi wani abu mai burgewa ba! Kana buƙatar kawai samun tattaunawar ta gudana. Ko da sauki "Hi!" iya yi.

 • Ka kwantar da hankalinka da numfashi mai zurfi idan kana jin damuwa kadan: Kamar dabi'a ne jin ƙunƴa a yayin magana da wanda kake so! Idan ka damu, gwada yin numfashi mai zurfi. Rufe idanunka kuma ka shaƙa ta hancin ka zuwa ƙidaya huɗu. Rike shi don ƙididdiga huɗu, sa'an nan kuma numfashi zuwa ƙidaya huɗu. Tabbatar cewa kana shan numfashi mai zurfi daga yankin cikin ka. Yi wannan motsa jiki na numfashi kaɗan don taimakawa wajen kwantar maka da hankali.

 • Kwada yin mata murmushi ko zata mayar: Murmushi alama ce mai kyau dake nuna ana son magana da kai. Yin mata murmushi yana nuni da jin daɗin ganinta. Idan ta ba ka ɗaya, kana iya so ka kusance ta.

 • Ka yi la'akari da yaren jiki: Kyakkyawan yare na jiki yana nuna idan tana son yin magana da kai. Kana iya lura cewa ta juyo maka fuska, ko kuma ta zare hannayenta ko kafafunta. Za ta iya yin wasa da gashinta ko kuma ta fizge tufafinta.

 • Kawo ƙarshen tattaunawar a kan kyakkyawar fahimta: Idan abubuwa suna tafiya daidai, gwada saita wani abu na wani lokaci. Misali, kana iya neman lambar wayarta domin tura saƙo ko kuma kira, ko kuma ka nemi handle ɗinta na dandalin sada zumunta don ka iya tuntubar ta nan.

Yadda Ake Fara Soyayya da Namiji (Saurayi)

 • Ki sa hankalin ki kan dalilin da yasa kika fara son sa da farko:  ki tuna abu da ya burgeki game da shi da har yasa kika faɗa masa, ko wani abune na kera ko kuma wani abu mai taɓa zuciya. Ki tabbatar yana da abubuwan da kike so a tare da namiji. Misali, idan ke mai son namiji mai natsuwa ne, toh ki nemi irin sa wanda yake son ki da soyayya.

 • Nemo alamun cewa mutumin yana sha'awar fara dangantaka: Kula da ƙananan abubuwa da yake yi, kamar riƙe kofa ko ajiye miki wurin zama a wani wuri. Duk da yake kina iya yin la'akari da waɗannan halayen har zuwa na ɗan lokaci, suna iya zama alamar cewa yana son ɗaukar abubuwa zuwa matakin soyayya tare da ke.

 • Ki tambaye shi abin da yake so a abokin tarayya: Dubi idan kuna da wani kamanceceniya da shi, ko kuma idan kun dace da juna ta wata hanya. Idan ku biyun ba ku da wani abu na kamanni, zaki iya ceton kanki daga yawan matsala ta hanyar buɗe masa abubuwan da kike so da abin da kike so a cikin abokin tarayya, idan hakan mai yuwuwa ne.

 • Yi watsi da duk wani rashin tsaro da zai gaya maki ba ki isa ba: Ki tuna cewa shakku da sukar kai sun kasance kamar al'ada ne, kuma ya kan zo miki lokacin da kike tunanin fara soyayya. Wataƙila kina jin rashin isa, Yi watsi da waɗannan tunanin, kuma ki bi abin da kike so. Idan kina son fara tattaunawa da wani, kada ki bari rashin natsuwar ki ya tsaya a hanyar ki.

Yadda Ake Dawwama a Soyayya

Burin duk mai soyayya na gaskiya shine ya dawwama cikin farin ciki tare da masoyan su. Amma sanin abubuwan da zai sa soyayyar ta dawwama atsakini na zamowa matsala a wasu lokutan. Dan haka dan sanin yadda zaku rike masoyan ku kuji dadin zama tare a duba wadannan salon rike saurayi ko budurwa.

Yadda Ake Rike Saurayi 

Akwai hanyoyi da dama da ake rike saurayi dan kasancewa cikin farin ciki da walwala. Tayaya hakan zai yu? Ga amsar ku a tafe.

Salon Soyayya ga Saurayi

Akwai hanyoyi da dama da zaki iya rike saurayinki da zai so ki da zicyarsa, daga ciki akwai wadannan dana lissafo.

1. Kisa shi murmushi

Zuciyar mutum na san zama da mai sata farin ciki. Hakan ne yasa duk wanda zai iya faranta maki rai ya zama mafi soyuwa a zuciyarki. Dan haka, kinzama mai yawan sashi murmushi a duk lokacin da kuke tare. Hakan zai da inbaki wuri zai kasance cikin damuwa.

2. Kiringa bin bayansa

Inkuna wasa ko gasa a tsakinku da yan aji ko a wani wurin. Ki ringa bin bayan sa koda ace yabata maki rai. Hakan zai sa ya gane kina san sa kuma ya kara girmanki a fuskar sa.

3. Kisa turaren da yafi so

Namiji na matukar san yaga yaje gurin mace tana kamshi dan haka, ki kokarta kigane wani irin turare yafi so domin akwai turaren da bazai yi masa dadi ba. Inyazo wurinki yaji kamshi ta kwanta ma ran shi, sai kiga farinciki a fuskarsa fiye da yadda tinani.

4. Duk abunda yake so, ki maida dashi abun muradinki

Duk abunda kika ga yana so, kiso abun da zuciyarki. Wasu matan suna daukan hakan kamar zubar da girma ce, amma ba hakan bane, namiji na matukar so yaga budurwan da yake so tana son duka abun da yake so. Hakan na kara damkon soyayya a tsakani.

5. Ki ringa yin masa barkwanci 

Idan kina yawan sa shi dariya, hakan zai sa yaso ganin ki a koda yaushe. Amma wasu matan zaki ga in suna tare da saurayin su, sai kiga suna daure fuskarsu, wanda kuma bai kamata domin zaiga kamar yana takura maki ne. In hakan ya cigaba da faruwa wata ran bazaki ganshi ba.

Yadda Ake Rike Budurwa

Akwai hanyoyi da dama da ake rike budurwa taji kaf a duniya babu kamar ka dan kasancewa cikin farin ciki da walwala. Tayaya hakan zai yu? Ga amsar ku a tafe.

Salon Soyayya ga Budurwa

Ina samaran dake fama da yadda zasu rike yan matan su, to ku cigaba da karanta wannan shashi dan samun fahimta akan hakan.

1. Kazama mai natsuwa alokacin da take gayamaka matsalolinta

In kazama mai yawan natsuwa da nuna damuwa a sanda budurwan ka ke fada maka matsalolin da take fuskanta, hakan zai sa zuciyata ta samu natsuwa da kasancewa cikin farin ciki yayin da kuke tare. Soboda in budurwan ka na fada maka abubuwa game da rayuwarta, ka bata hankalin ka.

2. Kazama mai yawan yabonta

Mata suna san mai yaba masu a duk abun da sukayi koda baiyi kyau ba. Kazama mai yawan yabon budurwarka a koda yaushe ko intayi jarrabawa ko kuma intayi abu Inka gani, ka nuna mata ai tafi kowa iya wa. Hakan zai sa taso ka fiye da yadda kake tinani.

3. Kazama mai bata lokaci

Wasu matan in baka basu lokacin da suke bukata, gani suke kamar tarayyar ka dasu bata da amfani kokuma baka du dasu ba. Dan haka kazama mai yawan bata lokacin da take bukata a sanda take bukatar ka. Hakan zai sa ta gane ita sarauniya ce a rayuwarka.

4. Kace mata kana sonta duk sanda kuka hadu

Yana daga cikin sirrin mallakar zuciyar mace ka yawaita gayamata yadda kake sonta. Inso samune duk safiya inka tashi, ka kirata ko ka tura mata sakon soyayya tare da gaya mata kana sonta. Ji zatayi kamar tana saman kowa a duniyar soyayya.

5. Kuringa fita shakatawa

Koda sau daya a sati ko sau uku a wata kuringa fita shakatawa da abar kaunarka kuga gari. Hakan zai sa ta gane tana da matukar amfani da mahimmanci a zuciyarka. Kuma hakan zai sa tasan wasu wuraren, ko da ace baku tare, zata fade wa kawayen ta irin shakawa da nishadin da ta samu tare da farin ciki mai yawan a fuskarta.

Soyayya da Karamar Yarinya 

Soyayya da kamar yarinya a wannan zamanin yanada amfani kokuwa bai da ita, meyake haifarwa, tana da illoli ko bashi da ita? Domin sanin me soyaya da kamar yarinya ce kunce da shi, ku cigaba da karantawa da gane me soyaya da kamar yarinya ce haifarwa.

A maganar gaskiya dai soyayya da karamar yarinya a shawar ce bai kamata ba. Amma fadin kuma kalmar kamar yarinya, ina nufin yin soyayya da yarinyan da ka baka shekaru masu yawa. Zaka ga saurayi mai hankali da kima ya tashi soyayya sai kaga ya nemi yarinya da ya girma sosai wanda kuma bai kamata ba. Abun yama kaiga bagide ya nemi fara da yarinyar da shi sa'ar mahaifinta ne, wannan ay bai kamata. 

Abubuwan da hakan ke haifarwa sun kunci kaga yarinya tana ganin kamar kowa a ungwar su sa'ar ta ne, zata ringa gayawa kowa maganar da yashigo bakin ta. Mafi yawancin lokutan, in zatayi wasu abubuwan, bata neman shawar kowa dan gani take ta isa babbar mace dan tana da saurayi mai zuwa wajen ta. Zaka ga ta raina kowa, babu wanda ya isa ya bata shawara tabi, daga karshe, sai kaga ana lalatan da sukeyi ya haifar da ciki wanda alokacin zata fara nadama akan hakan, wasu ma har shaye shayen kayan maye suke koya wanda kuma bakin jini da damuwa zai kawo wa ahalinta. 

Amma a matsayinka na saurayi ka tashi yin soyayya, ka samu budurwan da baka girma sosai ba mai hankali, zaku yi soyayyar ku cikin jindadi ba da bacin rai ba dan kuwa soyayya da karamar yarinya cike yake da bacin rai da bakin ciki. 

Daga Karshe

Soyayya ita ce mafi kyawun abu a duniya. Kasancewa cikin ingantaccen soyayya shine kyauta mafi ban mamaki. Kuna da duk abin da kuke buƙata a nan. Idan soyayyar ku ta sami rauni, aiwatar da shawarwarin dake baje a sama na tsawon mako guda, ku dubi abin da zai faru. Comments

Post a Comment

Drop Comment here

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa