Menene So: Alamomin So Na Gaskiya (Saurayi da Budurwa)

 

Nuna alamar soyayya a wasu lokutan yana da matuƙar wahala a tsakanin maza da mata. Zaka ga mace na son namiji, amma  duk alamar da ta nuna masa dan yagane tana son shi, amma kuma wasu na daukan hakan wasa. Hakan ma ke faruwa a tsakanin maza. Wasu halayen da zaka ga wasu matan ko maza na nuna wa hakan na nufin wani abu a tsakani. Domin sanin mene so na gaske da kuma tare da hanyar da ake ganeta cikin sauki, cigaba da karanta wannan rubutun dan wasu kuwa basu iya banbanta tsakanin so da kaina. In hakan na ma wahala, wannan rubutun takuce!!

Menene So?  

Abunda ake nufi da kalmar so ita ce haɗin motsin rai, ɗabi'a, da imani masu alaƙa da ƙaƙƙarfan ji na ƙauna, karewa, zafi, da mutunta wani mutum. So wani abu ne da ke faruwa tsakanin mutane biyu kuma yana girma cikin lokaci ƙanƙanuwa ta hanyar sanin shi ko ita da fuskantar matsaloli masu yawa na rayuwa tare. 

An yi ta muhawara mai yawa game da ko soyayya zabi ce, abu ne mai dawwama ko mai wucewa, da kuma shin soyayyar da ke tsakanin ’yan uwa da ma’aurata an tsara ta ne ta ilmin halitta ko kuma ta hanyar al’ada. Ƙauna na iya bambanta daga mutum zuwa mutum da kuma al'ada zuwa al'ada. Kowace muhawara game da soyayya na iya zama daidai a wani lokaci da kuma wani wuri. Alal misali, a wasu lokatai, ƙauna na iya zama zaɓi yayin da wasu kuma yana iya jin ba za a iya kamewa ba.

Wasu mutanen kullin shiga cikin kokwanto suke akan menene so da kuma kauna duk da yake yawancin mutane sun yarda cewa ƙauna tana nufin so mai ƙarfi, akwai rashin jituwa da yawa game da ainihin ma'anarta, kuma "Ina son ki/ka" na mutum yana iya nufin wani abu dabam da na wani dan ma'anoninta ba'a iya fadarsa duka. Banbancin so da ƙauna daga mahanga ta itace duk son da zakayi wa wani ko wata da har zakaji a zuciyarka/ki bazaki iya rabuwa dasu ba hakan yazama ƙauna.

Alamomin So Na Gaskiya: Yadda Ake Gane So?

A matsayin ka/ki na saurayi ko budurwa kaga wata ko wani kina so kuma kuka samu nasarar ganawa da juna. In soyayya tashigo tsakani, to ta hanyar Alamomin so ne kawai zaka gane hakan. Akwai alamomi da dama wanda ake gane wa in nasara tasamu. 

Alamomin Mace Na Son Saurayi

1. Yawan Kallo 

Yana daga alamomin kamuwa da so kaga mace tana yawaita kallon ka batare da kasan tanayi ba a wasu lokutan. A matsayin ka na saurayi kaga budurwa kuna yawan hada ido da ita. To hakan na nuna tana sonka.

2. Farin Ciki

Acikin alamomin gane mace na sonka, wannan shine alamar so na gaskiya kaga mace a koda yaushe in tagan ka, kaga tana cikin jindadi da walwalar da bazata iya rikewa a zuciyarta ba. Daga lokacin da ka fahimci hakan, bakomai bace face so da kauna.

3. Shiga Damuwa

Idan budurwa ta cika muna damuwa gareka musamman in wani abu mara dadi ko wani iftila'in ya faɗa maka, wannan alamar soyayya ce bayyanan na. Wasu lokutan ma zaka ga kamar basu da lafiya amma kuma soboda kai hakan ta faru. Kokuma in wani abun ya faru tsakaninku kanuna mata kaji haushi. Hakan nasa ta shiga damuwa.

4. Murmushi

Yawan murmushi na daya daga cikin alamomin soyayya wanda mafi yawancin mata ke nuna wa. Zaka ga mace inka kalle ta tayi murmushi, in tana ma magana, kaga murmushi tare da farin ciki mai ƙayatarwa a fuskar ta. Wasu lokutan ma zaka yi abunda bai kai na ayi dariya ba. Amma sai kaga tana murmushi. So da kauna ce ke kawo hakan. Soboda haka maza a lura kada ayi sake.

5. Yin Ma Magana

Wannan alamar son yafi aiki ne idan kai da ita baku magana kokuma kuna gaisawa ko a makaranta, wurin aiki ko a tsakanin yan uwan ka ma. Idan ka mace na yawaita ma magana ko da yaushe, koda a ce baka ganta. Shima ya fado cikin ire iren alamomin so da kauna. Ta yadda zaka tabbatar da hakan shine in tama magana baka amsata ba, zaka cewa bata ji dadi ba.

6. Shawara

Yana da jerin alamomin so kaga budurwa tana yawaita baka shawara a duk sanda kowa ke gudun ka ko in ka shiga wani hali kana neman mafita. Zaka ga tana iya bakin kokarin ta taga ce wannan abun da kake nema ka same ta ta hanya sassauka.  Duk macen da kema hakan, karka sake wani yasa ka rabu da ita, dan zai sa kayi nadamar yin hakan.

Alamomin Namiji Na Son Budurwa

1.Farin Ciki

Yana daga alamomin so kiga namji ya yawaita kasance wa cikin farin ciki. So ce kawai zata sa shi hakan. Inbai yi maki magana alokacin ba karki damu, nan ba da dadewa ba zuciyar sa zata aiko shi. 

2. Nunaki Ga Abokan Sa

In namiji na yawan nuna ma abokan shi ke ko kuma kiran sunan ki a tsakanin abokanshi hakan na nuna cewa kina da matukar mahimmanci a rayuwar sa. Hakan na da shi cikin jindadi da annashuwa. Sai yaji kamar yafi kowa in yayi hakan.

3. Mutunta Ki

Wasu lokutan zaki ga namiji baki mai komai ba, ba abunda ya hada ku, sai kiga duk in ya ganki, gurinsa yaga yafaran ta maki rai dan hakan muradinsa ne. Wannan ma yana daga cikin alamomin so da kauna. Amma ba kowacce bace zata gane hakan.

4. Yawan Tambaya Akan Ki

Duk namijin da kika ga yana yawan tambaya akan ki. Alamar so ce ta gaskiya. Inku ka kwana biyu baku hadu ba ya ringa kiranki ko ya tura maki sako ta hanyar amfani da waya ko kuma ya turo a gaisheki. Toh in hakan ya faru, alamar soyayya ce.

5. Son Ganin Ki

Inbaku hadu kwana biyu ba sai ya kira ya tambaye ki ina kika shige. Da kin kalle shi, kiga kuna yawan haɗa ido ko da yaushe. Kada kiyi tunani biyu wannan soyayya ce ba komai ba. Kallon fuskarki na bashi nishadi mai matuƙar ƙayatarwa shiyasa a koda yaushe yake son kallon ki.

Abubuwan Da Ke Gyara Soyayyan Maza 

1. Ɗaukan Hutu Daga Masoyiya

Ɗaukar hutu ya kasance abun mamaki ne a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan dake gyara soyayyan maza, amma a ringa ɗaukar yan kankanin hutu daga masoyiya na wani ɗan lokaci.

Kowa na bukatar wuri ko kuma lokaci a wajen soyayya. Masu bayar da shawara kan soyayya sun tabbatar da hakan ya kamata, kuma yin haka yana ɗa tasihi da gaske a soyayya.

2. Yawan Bada Kyauta.

Bada kyauta ga budurwa yakan ƙara wa soyayyan namiji ƙarƙo , da kuma tunawa mosoyiya da cewan ana tunaninta. Masoya na gaskiya suna mutunta wa juna, bayar da kyauta ga juna, shima wani ƙari ne. a taƙaice, bayar da kyauta abune mai karfi da gaske, wadanda ake yi ba tare da sanin wanda za'a ba ba yana ƙara zumunci sosai, musamman ma a soyayya.

Ka girmama yaren soyayyar masoyiyarka. miasali, mata suna da hanyoyi daban-daban ta godiya idan akayi masu abunda suke so. Zaka kasance cikin jin daɗi sosai idan ka ga ta ɗan bar harkokin ta dan ta sami lokacin ka, saboda kana mutunta zaman tare da kuma kasancewa tare. Ƙadan daga cikin hanyoyin mutuntawa wa masoyiya shine yawan bayar da kyauta a gareta.

Abubuwan Da Ke Gyara Soyayyan Mata

1. Kar Ki Kasance Mabuƙaciya a Kullun.

Kasancewa mabuƙaciya da yawan biyo yana iya kawo matsala tsakanin masoya. Idan kin zamto mai son ganin sa a ko da yaushe, ko kuma ki ringa tunanin shine kawai a duniyarki, toh hakan na nuna kina buƙatar da yawa daga garesa.

Kasancewar mace haka yana kawa gundura ga maza. Kina tunanin wannan halin zai taimake ki wajen riƙe shi, amma yana da haɗari sosai.yana korar sa.

2. Ki Basa Lokacin Ki Sosai.

Nasan na faɗi cewan ɗaukar hutu da kuma samun ƴanci a soyayya yana da kyau, amma a wani ɓangaren, baza ki iya ɗaukan lokaci mai tsawo ba ba tare da shi ba. Idan ba haka ba , mai yiuwar soyayyar zata mutu.

Soyayya na buƙatar kulawa, don haka, a ringa ɗaukan lokaci tare da shi ta hanyar fira ko wani makamancin hakan don ƙara ƙarkon soyayyar.

3. Nuna Masa Godiya

Kowa na son godiya da yabo daga masoyansu, me yasa kike tunanin taki daban ne?

Ko wani ɗan kankanin abu yayi, a gode masa , hakan zata sa ya ci gaba da yin waɗannan abubuwan don ya ganki cikin jin daɗi a ko da yaushe.

Alamomin Yaudara a Soyayya

Yaudara yana da haɗari sosai kuma ya kasance ɗaya daga cikin matsalar da ake fuskarta a yayin soyayya. A yayin da wasu suke kau da fuska a lokacin da suka fara ganin wasu halaye daga masoyan su, wasu sukan fara zargin yaudara sakamakon wasu munanan halayen da masoyan su ke nunawa.

1.  Mummunan Canji a Tattaunawa

Samun irin wannan canjin a soyayya ba abu bane mai kyau ba. Idan baku samun tattaunawa ingantacce daga masoyan ku, basu bada labarin abunda ya awku a yininsu,  ko kuma a daina faɗa maku "I love you" , mai yiuwar akwai matsala a ƙasa.

  • Za'a iya gano canji a tattaunawa ta waɗannan hanyoyi kamar haka:

  • Idan ana share maganganun ku

  • Canja abinda ake magana akai don rashin natsuwa

  • Idan ana shiru ba tare da wani dalili ba

  • Ƙin amsar tambaya idan anyi musu.

  • Yawan zargi maimakon tattauna matsalar dake ƙasa.

  • Yin anfani da yaren jiki ta hanyar kulle idanu ko kuma jujjuya su.

2. Ƙarya

Rashin gaskiya a soyayya babbar haɗari ne. Wannan rashin gaskiyan na iya zamo yin ƙarya kan ita kanta yaudara, ko kuma ƙarya kan wani abu na daban.

Alamomin Yaudara Game Da Ƙarya Sune:

  •  Zaku sami masoyan ku suna muku ƙarya akan wasu irin abubuwa na rayuwa.

  • Idan ka tambaye su da wa suke tare ko menene suke yi, zaku fahimci rashin natsuwa a tare da su.

  • Idan masoya sun kasance suna abubuwa a sirri.

3. Gujewa

Idan masoyi ya zamo mai gujewa, wannan alama ne na yaudara. Wani sahin, mutane masu yaudara sukan guji masoyan su don kar a zarge su ta hanyar auna masu tambayoyi akan inda suka je ko suke.

Hanyoyin Gane Gujewa a Soyayya Sun Ƙunshi:

  • Zaku ji kamar an guje ku.

  • Masoyan ku ba su son fita ko yin abubuwa tare da ku kuma

  • Zaku fahimci ransu a ɓace idan suna tare da ku.


4. Canjawa a Tunani

Idan masoyan ku na nuna kiyayya ga abubuwan da suka zamo suna so a abaya, ku tattauna da su ku gane abun da ya kawo wannan canjin. Amma idan kuna zargin yaudara, wannan alama ne da ke nuna yaudara a soyayya.

5. Zasu Zarge Ku Da Yin Yaudara.

Idan mutum ya zamo ba shi da gaskiya akan wani abun da yayi, zai iya turo wannan rashin gaskiyan ga wani ta hanyar tunanin shi ma haka yake, su ringa zargin kai ma ai hakan kake yi. A hali irin wannan, masoyan ku na iya zargin ku da yin yaudara ko da ka kasance kana basu alamun gaskiya.

Idan tana zargin ka da yin yaudara, ko in ka tambaye ta tana mayar maka da shi, toh babban alama ne tana yaudarar ka.

Gabatarwa

Hanyoyin gane soyayya na da yawa gaske , soyayya na da saukin ganewa in har zamu ringa Lura da waɗannan hanyoyin da muka faɗakar asama.

Soyayya ta kan canza da kuma girma a kowani lokoci, kuma mutane su kan nuna ta ta hanya daban-daban. Ko wani irin matsala a soyayya mai wucewa ne in har muka kasance a shirye don ganin cewa mun maganta su.

Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa