Yadda Ake Tsara Budurwa Cikin Sauki [A Waya ko Haduwar Farko]
Ina saurayin da yaga budurwa yana so amma baisan yadda zai iya tinkaran ta koyi mata magana ba, bai kamata kaji kunya ba soboda hakan ba shi ke nuna cewa baka cika namiji ba tunda mun san mata suna da ƙwarjini fiye da mu maza.
Domin sanin yadda ake tsara budurwa da kamu da sonka fiye da yadda kake zato a lokacin da bakayi tsammani ba, cigaba da karanta wannan rubutun dan samun karɓuwa wajen rabin ran ka!!
Yadda Ake Yana Budurwa Haɗuwan Farko
Tsara budurwa a farkon haduwa na da wahala ga wanda bai saba ba. Amma ba abu mai wahala bane. Akwai salo kuma da iya wa. A wannan shafi, zamu nuna maku yadda ake tsara mace a burge ta a farkon haduwa.
-
Kayi Koƙarin Lura da Halayenta Kafin ka Nufi Wajen ta.
Ka lura da halaiyan budurwar na wasu makonni ko watanni don sanin ko tana da namiji a rayuwarta, wuraren da take yawan ziyarta, mutanen da take yawan mu'amala da su, manyan kawayenta, da dai sauransu.
Ta ko wani hanya dai ya zamanto an san ciki da wajen ta don gano yanayin tsarin rayuwar ta. Hakan zai taimaka sosai wajen sanin hali ko salon da ya kamata a nufe ta da shi. Mata sun kasance masu hali daban-daban, don haka, fahimtar ta yana matuƙar anfani.
Kar Ayi Mata Gaggawa.
Da farko, kada ka fito kamar kana gaggawa wajen amincewar ta. Za ka fizge mace idan ka yi ƙoƙarin tura ta cikin wani abu - ba sa son shi. Ka tuna cewa dangantaka tana tasowa a hankali, don haka ba za ta fara soyayya da kai ba a farkon gani, amma idan ka ci gaba da nuna kyawawan halayenka, za ka iya samun dama daga baya.
Kayi Koƙarin Nuna Karfin Hali da Kuma Karfin Zuciya.
Mata suna son maza masu yin magana da ƙarfin gwiwa. Wannan bai kamata ya zama abun ruɗu ba tare da samun babban girman kai ba. idan kawai manufar ka ita ce nuna yadda kake da ban mamaki, ina mai tabbatar maka da cewan za ka dawo ba tare da komai ba.
Kasancewa da gaba gaɗi yana nufin kasancewa da ƙarfin hali don fara tattaunawa mai sauƙi da mace kuma a ci gaba da yin ta ba tare da yin hargitsi da ruɗani ba. Kada ka yi ƙoƙarin zama " masani" kuma ka yi magana da muryar da ba naka ba na asali don ban sha'awa - wannan zai sa taki baka kullin sauraro. Ka kasance da asalinka kuma ka nuna mata cewa kana sha'awar ta da gaske.
Gabatar da Kanka Amma Kada Ka Bar Ta Ta Lura da Manufar Ka.
Nemo hanyoyi masu jan hankali na gabatar da kanka kuma ka tabbatar ka sami lambarta wayan ta a wannan matakin. Hanya ɗaya ita ce yin abota da ɗaya daga cikin ƙawayen yarinyar. Ranar da ka hange su tare, ka taho wurinsu don yin ɗan hira kaɗan kuma ka bar ƙawat yarinyar ta gabatar muku da juna.
A madadin, kar a yi amfani da wani can daban a matsayin na uku. Zauna kusa da ita a cikin aji, coci, ɗakin karatu, ko sauran wuraren jama'a. Gabatar da kanka nan da nan ko bayan zama kusa da ita so da yawa. Kana iya neman ƙawarta ta zauna tsakanin ku da ita idan ka kasance cikin fargaba ko ƙunya.
Kayi Koƙarin Sa Ta Dariya.
Idan ta yi dariya yayin da take tare da kai, wannan alama ce mai kyau. Koyaya, bai kamata ka yi wasa da wannan damar ba. Kafin yunƙurin yin wani abu, bari yarinyar ta zama abokiyar ka kuma ka sa ta amince da kai. Dole ne ta san cewa ba ka shirya karya zuciyarta ba kuma ka damu da yadda take ji.
Ka Kasance Mai Gaskiya Kuma Mai Buɗaɗɗen Zuciya Tare Da Ita.
Babu wani yabo da kwarkwasa a zahiri idan ta ji rashin aminci a kusa da kai kuma ba za ta amince da kai ba. Idan ka yaba mata, ya kamata ka yi hakan daga zuciyar ka, kana faɗin abubuwan da kake so da gaske game da ita .
Kada ka ji tsoron rashin jituwa da ita, muddin ka mutunta ra'ayinta, ka ba da dalilai masu kyau da ya sa kake tunaninta ta takamammen hanya, kuma kada ka yi mata barazanar yarda da ra'ayinka. Wanene ya sani, watakila za ta ƙara girma a gare ka saboda kai mutum ne mai ƙarfin hali wanda ba ya jin tsoron faɗin ran sa.
Ka Nuna Kana Ƙaunarta da Gaske.
Akwai bambanci tsakanin abokantaka mai sauƙi da kuma sha'awa ta ainihin ko ta ƙauna. Ya kamata ta ga ko ta fahimci cewa da gaske kana son sanin ta sosai kuma, ka gano halayenta. Yi mata tambayoyi game da harkokinta na rayuwa kuma ka yi mata magana da yawa a lokacin da ta dace. Saurari a hankali ga abin da take faɗi, kuma koyaushe ka yi kokarin kallon cikin idanunta, wannan alama ce cewa kana sauraro yadda ya kamata.
Ku Yi Abota Da ita Amma Ba Da Daɗewa ba Don Kada ta Maida Alaƙar ta Abokantaka.
Ka wadata kanka lokacin da ta gayyace ka zuwa wani abu na faruwa kuma ka daidaita ta idan ka rasa. Ka gayyace ta zuwa abubuwan da suke na sha'ani kai ma, amma kar ka sa ya zama kamar kana son bayyana niyyanka. Abokan ka kuma za su iya gayyatar ta zuwa sha'ani a madadin ka, ko kuma kana iya nunawa a duk inda ta halarta idan sha'anin a buɗe take ga kowa.
Yaba Mata Sau Da Yawa.
Tabbas, idan ka wuce gona da iri tare da yabo mai daɗi da rashin tunani, yarinyar ba za ta gamsu da waɗannan kalmomin wofi ba. Maimakon haka, ya kamata ka nemo lokaci, wuri, da kalmomi don yaba mata da gaske kan abin da kake so ko yake baka sha'awarta game da ita. Kar ka yi mata yabo da yawa game da kamanninta.
Mata suna son jin kyau, amma kuma suna son jin cewa ana son su fiye da kamannin su kawai, don haka ka mai da hankali kan halayenta.
Ka Zama Mai Tsafta.
Wannan matakin yana da mahimmanci fiye da yadda kake tunani. Yawancin mata suna alfahari da kyan gani da ƙamshi, don haka suna yaba maza masu tunani iri ɗaya. Idan ka yi sakaci game da tsaftar ka, ka kasance cikin shiri don baza ta amince da kai ba. Tsaftace gashi, tufafi, da jiki sune cikakkar dole-sanya idan kuna son burge mace.
Duk yadda ka iya rike zancen, zata ji kyamarka idan kana da wari ko gumi.
Yadda Ake Tsara Budurwa a Waya
Ka Iya tsara budurwa a waya? toh idan baka iya ba, akwai matsala. A wannan lokacin da muka tsinci kan mu, ya kamata ka iya yana budurwa a waya. Kabi ka idojin da muka lissafa a kasa idan kana son ka san yadda ake tsara budurwa a waya.
Kasan Wata Irin Mace Ce Ita
Yakama ta a matsayin ka na namiji kasan wace irin yarinya kakeso ka yana. Ba ko wata mace bace zaka kira kayi mata magana a waya ba. Wasu matan ma cewa zasuyi kai ba ajin su bane tunda bazaka iya tarar su ba. Dan haka, wannan shine matakin farko na yadda ake yana budurwa a waya.
Ka tsaya ka karance ta tukunna, kasan me take so da kuma abinda bata so, hakan ne zai sa ka iya shawo kanta da sauki batare da kasha wahala ba dan haka, yana da matuƙar amfani.
Samu Lambar Wayan Ta
Bayan kayi nasarar sanin wace irin mace ce ita, sai kai ƙoƙarin samun lambar wayanta (inbaka dashi, hakan nada matuƙar wuya inbaka da wanda zai iya samoma). Samun lambar aiki ne mai zaman kanshi, sai dai kuma in kuna tare da ita dama to wannan mai sauki ne. Zaka iya samun lambar wayanta ta hanyar ƙawayen ta ko kuma abokan ta na karatu.
Amma kuma kasan ba kowanne bane zai iya baka. Amma dai in da gaske son ta kake yi, kuma ƙawayen suna son ku tare baka da matsala, don a take ma zasu iya baka lambar, shi yasa yana da kyau ace kana mutunci da wasu da cikin ƙawayen budurwar ka.
Ka Gaishe Ta
Bayan samun lambar wayanta, yanzu kuma aiki na gare ka. kasan yadda zaka yi mata magana kai tsaye batare da sakin layi ba. Wannan salon yadda ake yana budurwa a waya, shine wanda yafi buƙatar hikima, lissafi, natsuwa da tinani matuƙa kafin aiwatarwa.
Kasan yadda zaka gaishe ta wanda kafin ma ka faɗi abunda ke zuciyar ka zata gane inda ka dosa. Kasan irin gaisuwar da zaka yi mata. Ka tabbatar ka saka mata ƙosawa taji me zaka ce mata.
Kayi Mata Magana Da Tattausan Murya
Kasan mu maza, muryan mu a waya sai a hankali. Soboda haka kasan yadda zaka mulki muryan ka soboda tayi daɗi a kunnin ta ba wai da kafara magana ta yanke ma waya ba don bata jin me kake cewa ba.
Duk abin da zaka ce mata, yazamo ka haɗa da kalaman so wanda zai sa ta gane irin saƙon da zuciyar ka tazo mata da ita. Soboda haka, yadda zaka yi mata magana abun duba wa ne.
Kasan Abubuwan Da Zaka Fada Mata
Da an ce kalamai, sai kaji namiji yana faɗan abubuwa wanda bai kamata ya faɗe su ba matuƙar yana so a so shi. Ya kamata ka tsaya kayi tinanin me zaka ce mata in ta ɗauki kiran ka. Inso samu ne ma, ka rubuta don karka je kabada maza.
Karka ringa mai mai ta magana don hakan zai sa ka gundure ta. Kuma hakan zai sa kai da ita bazaku dai dai ta ba. In ma kayi wasa, ita da ƙawayen ta zasu mai da kai abun dariya kuma hakan ba abun so bane.
Kaɗan Haɗa Da Barƙwanci
Wannan matakin ma yanada matuƙar amfani cikin jerin yadda ake yana mace ta waya. Kasan suna yawan son abunda zai basu dariya sosai. Soboda haka, da kun ɗanyi magana kaɗan sai kasa barƙwanci a cikin maganar (amma kasan yadda zaka yi hakan cikin salo, kuma ba sosai ba).
Hakan zai sa tafara tinanin rayuwar ta tare da kai irin nishadin da zata kawo a rayuwar ta. In ma baka iya ba, ka koya soboda yana da matuƙar amfani sosai.
Kayi Mata Uzuri
A yayin da kake mata magana, ko me tayi maka, kar kasa ya dame ka. Soboda kasan mata akwai su da shagwaɓa da jan aji. Karka sa hakan ya dame ka. In kaga mace na maka hakan, bayan ka gaya mata sakon da zuciyar ka ke tafe dashi, Yakama ta ka bata lokaci tayi tinani akan ka, dan yin shawara akan in ka dace da ko saɓanin hakan. Amma in saɓanin hakan tazo karka damu dan zai iya cutar da kai.
Ka Nuna Mata Cewa Kai Cikkaken Saurayi Ne
Duk abun da ta tambaye ka, kayi mata koda ace yafi ƙarfin ka, kada ka nuna mata hakan, ka nuna mata zaka iya komai dan ita. Amma fa, ako me zakayi, kar ka sa alfahari, da sankai, dan zai iya lalata komai gaba daya.
Kayi mata abubuwa gwargwadon ikon da Ubangiji ya baka. Kuma kada ka nuna mata cewa abubuwan da kake mata kana yi ne dan wani abu da take dashi. Kasa ta gane cewa akan son da kake mata, komai ma zaka iya indai zai sa ta farin ciki.
Yadda Ake Chatting Da Mace A Tsara Ta
Hawa online ya zama abun zamani da yan mata suke so kwarai da gaske. saboda haka, mun rubuta wannan ban gare saboda wadanda suke so su koyi yadda ake chatting da mace.
Samu Username Dinta Na Yanar Gizo
Wannan salon sai maza masu kunya da fargaba a fannin tarar mata. Amma hakan ba wani abun damuwa bane. A san da kaga mace kuma bazaka iya tararta ka gayama ta ba kuma ta na da shafi a yanar gizo, kaga faɗuwa tazo dai dai da zama.
Sai kayi searching din sunanta a yanar gizo kamar su Facebook da WhatsApp (in kana da lambar ta) da dai sauransu wanda kasan tanayi. Sai ka tura mata sakon zama abota, in ta aminta kaga kasa mu damar tura mata saƙonni.
Kazama Mai Yawan Yi Mata Magana Sosai
Mu maza muna wata kuskure wanda bai kamata ace munayin sa ba kwata kwata. In muna chatting da mace, tun ranar farko sai muce ma budurwar muna son ta kokuma mu ce ta tura mana lambar wayan ta.
Hakan kuskure ne soboda in wata zata baka wata kuma bazata bada ba, zasu yi tunanin baka san ne kake yi ba. Wannan tsigar yadda ake tsara mace ta hanyar chatting yana matuƙar amfani sosai. Da fari ka ringa mata magana akai akai dan abokan ta kar ku tayi karfi daga baya sai ka sanar da ita abun da zuciyar ka ke ɗauka da ita.
In kace zaka yi gaggawa za'a iya samun matsala.
Karinga Yabonta a Duk Abinda Tayi
Mace na san wanda ke yabon ta sosai, ko da ace abun da tayi bai kai na yabon ba. Kamar in ta sa hoto a shafinta na yanar gizo, sai ka ringa like da comment sosai (in so samu samu ne, kazama na farko a koda yaushe).
Hakan zai sa ta fara tinani akan ka, daga nan zata fara karantan ka ba tare da kasan ma hakan na faruwa ba. In haka yacigba da faruwa, toh fa ka dace dan uwa.
Kasata Ta Gane a Kullin Kana Tare Da Ita
Kayi ƙoƙarin saka ta ta gane cewa kai na dan ban ne. Kamar kasa hankalin ta ya kasan ce akan ka a duk sanda kuke tare. In kuma kanada lambar wayan ta, zaka iya kiranta a duk lokacin da kasan bata aiki kokuma tura mata saƙonni dan gane yadda take ciki.
A hakan ma inka yawaita kiranta ma hakan ma yana tasiri sosai. Sa'an nan kuma kabi komai a hankali.
Kayi ƙoƙarin Gane Matsayin Ka a Zuciyar Ta
Dan gane nasarar ƙudurin ka, kayi ƙoƙarin gane wanene kai a rayuwar ta ko kuma matsayin ka a zuciyar ta. Taya zaka gane hakan. Hanyoyi da dama kuwa. Inka kira ta, tayi saurin ɗauka ko kuma in bata ɗauka ba in ta kira ta baka haƙuri tace ma bata kusa da wayan, kokuma in ka tura mata sako ta shafinta na yanar gizo ta amsa da sauri fiye da yadda ta sa ba ansa wa. In hakan ta faru, hakan ma alamun nasara ce
Daga Nan Kuma Sai Ka Sanar Da Manufar Ka Ta Soyayya
Bayan ka san matsayin ka a zuciyar ta, sai ka sanar da ita saƙon da zuciyar ka ta aiko ka. Mafi yawanci, sunsan me kake tafe da shi, amma sunfi so kafaɗa da bakin ka. Hakan ne zai nuna in zaka iya kula da su ko saɓanin haka. Amma karkayi tinanin zaka samu amsar ko ƙarbuwa a lokacin, sai ka jira ta.
Kazama Mai Yawan Sata Farin Ciki a Lokacin Da Bata Yi Tsammani Ba
A wannan lokacin da take nazari akan ƙudurin ka, kazamo mai yawan sata farin ciki ta hanyar tura mata saƙonni na soyayya da na nishaɗi. Hakan zai sa ta gane irin matsayin ta a zuciyarka. Kada kace dan tace maka zatayi nazari ka koma ka zauna kana jiran saƙon yarda (zaka tsaya kallon ruwa, kwaɗo yayi ma kafa).
Ka bi ta kowacce hanya dan ganin kasa me ta, in so samu ne, sakonnin safe daban, na rana, da na dare haka yadda duk in ta hau online, tinanin ka kadai zata fara. Wannan tsigar yadda ake chatting da mace a yana ta yanada matuƙar mahimmanci dan samun karɓuwa da sauri.
Ka Bata Lokaci Danyin Nazari a Kan Ka
Bayan duk abubuwan dana lissafa, tana buƙatar lokaci, shawarwari daga kawayen ta ko wasu yan uwan ta. Dan haka, dan bata baka amsa da wuri ba, bashi ke nufin bata son ka ba. Ka jira, hakan ne zai sa taga ne cewa a duk lokaci zaka iya jure komai dan ita. Kuma hakan na daya daga cikin abubuwan da mace ke dubawa a halin saurayin su.
In ka cika takura ma ta, wa mata zata iya fushi ta ƙyaleka, kuma hakan ba shi kake so ba. Sai a kula sosai.
Kalaman Tsara Budurwa Masu Daɗi
Duniyar zamani cike take da kalmomi na kan layi wanda ta hanyar su, mutum zai iya tsara mace tare da shawo kanta. Tare da waɗannan kalmomi, zaka iya sanar da budurwan da kake so ta san abin da ke cikin zuciyar ka kuma, mafi mahimmanci, zuciyar ka.
Ga yadda ake gayawa yarinya ta zama budurwar ka idan har kana ƙaunar ta da gaske.
In a tambaye ni sunayen manyan abubuwan al'ajabi guda goma na duniya, zaki zama tara a cikinsu, na goma kuma shi ne yadda duniya ta iya ta ɗauke ki.
Kin cancanci duniya, kuma na san ba zan iya ba ki wannan ba. Don haka, zan ba ki abu mafi kyau na gaba: ita ce duniya ta.
Duk lokacin da na kirga ni'imata, sai na kirga ki sau biyu.
Abokai na suna ganin na haukace ta dalilinki. Abin ban dariya shine, gaskiya ne. Kyakkyawarki ce ta sa ni a gaba tunda na sa idanuna a kanki.
Wani lokaci ina tunanin zama kofi. Me yasa kike tambaya, Ina hassada da ganin kofin kofi da ke sumbantar leben ki a kowace safiya.
Ina so in sayi littafi amma na yi tunani, me zai hana ni da ke mu ƙirƙirar namu labarin? Na san zai yi miki daɗi sosai.
Kafin in hadu da ke, ban taba sanin yadda ake yin murmushi ba gaira ba dalili ba, sai da muka haɗu.
Ina son ki fiye da tunanina. Ina tunanin ki kowace rana saboda ke ce rana ta. Ina so in ƙaunace ki kuma in riƙe ki a cikin zuciyata koyaushe. Don Allah ki zama budurwata.
Da a ce ina da buri guda ɗaya na tsawon rayuwata , zai zama da in san ki tun haihuwana kuma in kasance tare da ke har tsawon sauran rayuwata.
Kasancewar soyayya ta kasance kamar karin gishiri ne ko cika baki, amma hakan ta canza tun daga ranar da na faɗa cikin soyayyarki. A Lokacin da na ce ke ce komai na kuma zan yi miki komai, ba cika baki nake yi bai.
Ina mamakin yadda madubin ki ke ji idan kin kalle shi kowace rana. Dole ne ya zama wani cikin jin dadi don kallon kyakkyawar fuskarki kowace safiya.
A cikin mafarkina, ke kaɗai nake gani. Amma, a azahiri na, ina so in so ki har abada. Don Allah ki bani daman yin hakan.
Ina son ki ne ba don ko yadda kike bane kawai ba amma saboda wanda zan zama idan kika amince da ni.
Na san ni daya daga cikin zababbun ’ya’yan Allah ne kamar yadda aka nufa na haɗu da ke, na kamu da sonki kuma ina fatahn mai da ke tawa.
Ki ƙaunace ni kamar yadda nake ƙaunarki, kuma zan ƙaunace ki kamar yadda kike so. Ki ɗauke ni a matsayin saurayin da kike fatah a cikin mafarkinki, ni kuma zan sa mafarkinki ya zama gaskiya.
Soyayya haukace. Ba zan iya bayyana dalilin da yasa nake jin wannan haɗin da ba za a iya kwatantawa da ke ba. Na tabbata ke ce sauran rabina. Kira shi wauta, amma ban damu ba. Wannan shine mafi kyawun abin da na ji a cikin dogon lokaci. Kuma a gare ki ne.
Kowane bangare na rayuwata cikakke ne ko kuma kamar sun cika, ban da bangare guda. Wannan bangare yana buƙatar ki cika shi. Don haka nake neman ki zama budurwata, kuma ina fatan za ki amince.
An ce soyayya abu ne mai hadari ga wanda bai shirya ba. Amma ina matukar sha'awar, kuma ina so in yi kasada da son ki.
Murmushin ki tsararrun haske ne. Yana haskaka duniyata kuma yana haskaka gabana. Ina fatahn za ki zama hasken rana na har abada.
Yau, na kawo karshen bincikena. A ƙarshe, na sami ɗaya a gare ni. Zaki zama budurwata?
Daga Karshe
Tsara budurwa na iya zama ba abu mai sauki ba musamman ga samari masu ƙunya. Don tsara budurwa ba tare da jin ƙunya ba, sai ka ajiye ƙunya a gefe. Wani zubin sai a rasa abin da za'a faɗa mata, Amma tare da waɗannan matakan da muka tanadar a sama, za ka iya tsara ko kuma yana kowace mace kuma ka sami ƙaunarta.
Kuma ayi koƙarin ƙulla abota da ƙawayenta don sanin abubuwan da take so da kuma yadda za'a fuskance ta.
Muna godia
ReplyDeleteAllah bamu sa'a
🥰🥰🥰✔️✔️✔️
ReplyDelete