100+ Soyayya Text Messages Dan Neman Kauna
Mun jero maku sakon soyayya na text messages zuga ga saurayi da budurwa. 50 zuwa ga saurayi, 50 zuwa ga budurwa.
Soyayya Text Messages Dan Neman Kauna Zuwa ga Saurayi
Bazan iya kimanta soyayyar da nake maka da ruwa ba, kasan meyasa? Soboda muna iya dadewa bamu sha ruwa ba. Bazan iya kimanta soyayyar danake maka da abinci ba soboda muna azumi ba tare da cin abin ci ba. Amma duk wani dan adam da halittu gada daya na bukatar iska a rayuwar sa. Kamar yadda mutum ke neman iska dan rayuwa a saukake, haka zalika zuciya ta da gangan jiki na ke bukatar ganin ka tare dasu.
Masoyi na abun alfahari na, yau natashi daga bacci ina mai farin ciki wanda bansan dalilin hakan ba. Amma kuma abu guda daya da na sani shine, zuciya ta tana bugawa yau ta dalilin natsuwar da take samu soboda kai.
Na zauna na tambayi kaina mene ne nake bukata a rayuwa ta wanda zai zamo silar farin ciki da nishadi a gare ni. Abun mamakin shine duk sanda nayi ma zuciya ta wannan tambayan, tinanin ka kefa do mun a rai. Ina kaunar ka.
Abaya mun kasance abokan juna, amma kuma zuciya ta ta kamu da soyayyar ka a lokacin da banyi tsammani ba. Bansan yadda zan tinkare ka da wannan maganan ba. Amma ina so na sanar da kai cewa ina kaunar ka fiye da yadda kake tinani.
Nakasa gane meyasa duk sanda muka hadu da kai nake ji kamar ranar nafara ganin ka. Wannan da me zamu kira ta?
Yau bayan na tashi da safiya na zauna ina tinanin ka sai ga hawaye yana zuba a fuska ta. Soboda zuciya ta tana kewar ka. Babu abunda zuciya ta take nema sai kusancin ka gare ta.
Aduk ranar duniya, soyayyar da nake maka a zuciya ta karuwa take cikin zuciya ta. A farko na mai da hakan wasa amma gashi son ka ta bayyana a rayuwa ta bana iya jure rashin ganin ka.
Aduk sanda aka fada mun wani abu akanka sai naji kamar soyayyar ka ake kara saka mun a cikin zuciya ta. Yanayin da nake shiga ma kawai ya isheni.
Daga rana irin ta yau, na dauki alkawarin kaunar ka da kyautata maka har sai randa zan daina numfashi a duniya.
Kasan wani abun mamaki? Kaf abubuwan da sai tare dasu nake kasancewa cikin farin ciki, kaine kan gaba. Rayuwa ta na bukatar ka acikin ta.
Idan na kalli fuskar ka babu abunda nakeyi face godewa ubangiji da yayi sanadiyar haduwa ta da kai. Kashigo rayuwa ta kabani kyautar ban taba tsammani ba.
Na shiga rudani wasu lokutan akan zabar wani irin saurayi nake bukata arayuwa ta, amma haduwar mu ta bani bayanin dana dade ina nema.
Da’a ce za’a bani damar chanza rayuwa ta, abu na farko da zanyi shine nemo ka tun daga farkon rayuwa ta dan kaine kadai ke iya kwantar mun da hankali.
A lokacin da muka fara haduwa, banyi tsammanin zaka kasance dalilin fita ta daga bakin ciki zuwa farin ciki ba. Amma yanzu kam na gamsu da komai. Ina kaunar ka.
Haryanzu banmanta ranar da ka shigo cikin rayuwa ta ka samar mun da nishadi ba. Ranar abun tinawa tace akullin.
Masoyi na rabin raina, inaso kayi mun alkawarin kulawa da kanka. Matukar kayi mun hakan, nayi alkawarin zama irin macen da ka dade kana mafarkin samu. Wannan shine muradi zuciya ta. Shin zakayi mun hakan?
Kowa na magana akan yadda soyayyar su take tafiya. Amma ni duk bai dameni ba dan kuwa tamu batayi dai dai da tasu ba. Kamar yadda ka maida farin cikina taka, haka zalika na dauki alkawarin faranta maka harkashen rayuwar mu. Muna fatar ubangiji ya cika mana burin mu.
Ka shigo rayuwa ta kasa duk abunda nake dauka bai da amfani a rayuwa ta yazamo mai amfani. Abubuwan dana dauka wasa sun zama da gaske. Yanzu nakara sanin mene ake nufi da sarki mai kishin sarauniyar sa.
Nadade ina nemar wata shashin zuciya ta, amma kuma banganshi ba. Amma kuma sai gashi ina kallar fuskar ka ita nafara gani. Sai dai kuma bansan yaushe ka dauke ta ba.
Hubbi na, bara nafada maka wani abunda baka sani ba, nasan kana so na sosai, amma kuma abunda baka sani ba shine soyayyar da nake maka tafi wacce kake nuna mun.
Duk idan na zauna, walau nikadai, tare da kawayena ko kuma yan uwa na, babu abunda ke hanani tinanin ka, zuciya ta kewar ka take yi a koda yaushe.
Gani a zaune a cikin gida banda wani aikin yi soboda nagama duka. Habibi na, ya kake gani idan kazo ka dauke ni mu fita ganin gari?
Gaskiya wannan sanyin yayi yawa gaskiya. Amma fa nasan dalilin meyasa nake jin sanyi. Bakomai bane sai dan baka akusa dani. Kataho gare ni.
Duk sanda na bata maka rai ko nasaka cikin damuwa, babu abunda ke kwantar mun da hankali kamar naga wannan bakin cikin ta dawo farin ciki.
A rayuwa ta bansan mene ake nufi da kalmar jindadi ba sai da kaddara ta ta hada ni da dakai. Bantaba tinanin zanso wani da’ namiji kamar yadda nake kaunar ka ba. Gaskiya kai na daban ne a cikin dubu.
Inaso nabaka wata kyauta soboda kaima ka bani kyaututtu ka da dama. Na baka kyautar zuciya ta, kai na, farin cikina. Duk yanzu suna hannun ka komai kaga ya dace kayi. Ina kaunar ka habibi na.
Kasan yadda nake son ka kuwa, ba karamin kishi nakeyi ba idan naga wata ya’ mace a kusa dakai. Hakan na saka ni cikin damuwa sai naji kamar za’a kwace ka daga wuri na.
Na zauna na tambayi zuciya ta menene take son gani kullin da safe da kuma mene ne take son gani da rana sa’an nan kuma menene ke bata nishadi daddare? Amsar dai bai wuce masoyi na. zuciya ta muryar ka take son ji da safe, kai take son gani da rana. Matukar duk wannan ya samu, cikin dare kuma sai jin dadi soboda duk abunda take bukata ta samu.
Masoyi na, tun daga ranar da na bude maka zuciya ta ka shiga, haryanzu ban kara ji, ko da wasa, ban kara fuskantar bakin ciki ko damuwa ba.
Kadan kulle idanun ka ka bude sai ka fadan mun mai kagani, soboda nidai a sanda na kulle idanuna, ina kulle wa, kaina fara gani agaba na bayan na bude idanu na. Kaga abunda tinanin ka tasa mun.
Masoyi na abun kauna ta, a ranar daka ce mun zaka kula da ni kamar yadda kake kulawa da kanka, zaka saka ni cikin farin ciki kamar yadda kake ciki, na dauka duk kana wasa ne, amma sai gashi abunda na dauka wasa ta fara faruwa. Nagode sosai.
Abu mai kyau ne ace a wannan duniyar ansamu wanda farin cikin ka ke samar masa da nasa farin cikin, to nayi wannan sa’ar. Ubangiji ya hadani da saurayi tamkar sarki acikin sarakuna, jarumi acikin jarumai, shugaba a cikin manyan mutane. Nikuma mena ke nema yanzu? Ai babu komai. Kuduri ta ta gama cika.
Nashigo cikin rayuwar ka nace maka zan saka farin ciki, amma kaika sani kafin na saka. Nace zan saka nishadi, amma kafara saka ni nishadi kafin na saka. Nace zan so ka fiye da yadda nake son kaina, amma kuma kana nuna mun so fiye da yadda kake nuna wa kanka. Nagode sosai.
Wasu lokutan idan na zauna sai na rasa mene ke sani farin ciki. A wannan lokacin sai na tina ina da masoyi wanda zai iya yin komai soboda na samu farin ciki.
Masoyi na, ka zo gare ni soboda zuciya ta tasamu sukuni, a halin da take ciki, kai kadai take da bukatar gani soboda ta natsu. Ina kaunar ka fiye da yadda nake kaunar rayuwa ta. Ka kula mun da kanka.
Kafin na hadu da kai, ban dauki wayata tana da amfani ba, amma haduwar mu tasa na gane mahimmancin waya ta a rayuwa ta. Babu abunda ke bani nishadi kamar ka kirani ina kwance muna waya. A wannan lokacin zan iya bada kyautar duk wani abu dana mallaka ba tare da nasan nayi hakan ba.
Masoyi na, aduk sanda nafara tinani akan sunan da zan kira ka da ita, sai nayi wuni ina tinani amma ban samun sunan daya dace da matsayin ka a rayuwa ta. Meyasa hakan ne?
Kasan wani abu? Ranar da ka fara tinkara ta da soyayyar ka, nayi tinanin kawai kana neman wacce zaka kira budurwa ka ce, amma sai yanzu na fahimci farin cikina kake nema. Nikuma nayi maka alkawarin saka ka cikin farin ciki har zuwa ranar da zan daina numfashi.
Habibi na, kazo nabaka wata labari mai dadi, amma kafin nan sai kafada mun menene yasa baka kirani jiya ba, duk kasani cikin damuwa. Kasan yanayin da nake nake shiga ta dalilin ka?
Nagama cewa bazanyi soyayya ba sai wani lokaci, amma gashi kasa na karya wannan alkawarin dana daukar ma kaina. Da’a ce duk samaran duniyar nan irin ka ne, da yan mata sunji dadi.
Zo gareni na shayar da kai zumar soyayya kamar yadda kasani farin ciki. Koda kana nan koda baka nan, gurbin ka a zuciya ta, babu wanda zai iya kwace gurbin ka acikin zuciya ta.
Shin zaka iya bani shawara akan yadda ake rike saurayi? Soboda nakara himma da chanza salo dan na cigaba da mulki a zuciyar ka.
Idan kace sarautar zuciyar ka nice aciki to a tinanin ka waye to zai yi mulkin a cikin tawa zuciyar? Baka da wuri mafi nishadin zama da mulki kamar cikin zuciya ta. Ga makullin zuciya ta nabaka kyautar ta a yau. Kayi mulkn kai gwargwadon iko.
Kasan yadda nake son ka kuwa? Idan bangan ka ba a rana jinake kamar mun dauke shekaru masu yawa bamu hadu ba. Ina rokar ka habibi na, ka kasance a tare dani.
Masoyi na, yakamata wata rana mufita cikin gari tare muje muga irin halittar da ubangiji yayi cikin girman sa da izzar sa. Kaga nan gaba zamu samu labarin da zamu bawa iya’yen mu.
Dafatan ka tashi lafiya? Jiya bayan mungama waya nakasa kwanciya soboda zuciya ta takasa jurar rashin ka a kusa da ita. Amma kuma muna godewa ubangiji daya bamu ikon tashi yau cikin koshin lafiya.
Inaso ka kalli cikin idanuna kace mun kana sona. Nikuma zanyi duk abunda kake so kafin kyapta ido. Ni yanzu babu abunda nake nema face soyayyar ka.
Bantaba shakuwa da wani saurayi a rayuwa ta kamar yadda na shaku da kai ba. Ina fatar wannan tarayya tamu yazamo abunda kowa ke sha’awar yin irin ta.
Zan iya komai akan ka, matukar zan samu kaunar danake bukata, ta dalilin ka kullin nake dariya. Musamman lokacin da kake kallo na kana murumushi. Murmushin ka duniya ce.
Inaso ka soni kamar yadda nasamu zarrar sonka. Duk sanda wani abu ya bata maka rai ko kana cikin damuwa, ina rokon ka masoyi na, kafada min dan na kwantar ma da hankali. Zansa kamanta duk wani damuwar da kake ciki cikin sauki. Babu abunda bazan iya yi soboda kai ba. Ina kaunar ka.
Soyayya Text Message Dan Neman Ƙauna Zuwa ga Budurwa
Barka da war haka mabuɗin zuciyata. A duk lokacin da na sa idanu na akan ki, sai inji tamkar wani ɓangaren jiki na ya fita. Dan Allah ki amince da ni ko zan sami sauki; Nayi alkawarin sonki so na tsakani da Allah.
Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniyar mata. Na zo da ɗan wani bukata, zuciya ta tayi duba ga duk matan da suke faɗin duniyar nan, babu wacce ta ji tana so illa ke. Don Allah ko zaki iya biyan min wannan bukatar?
Na san cewa ni ba gwani bane a soyayya, Wata qila ma ni ba irin wanda kike so bane da soyayya. Amma ina mai roƙo gare ki da ki bani dama in nuna maki irin son da nake maki.
Ban san menene so ba, domin bani taɓa soyayya ba. Amma duk lokacin da nake kusa da ke sai in ji zuciyata tana bugawa da sauri. Cin wani irin asiri kika yi mun ne? Ni fa na faɗa cikin soyayyar ki.
Gaisuwa gare ki babbar aminiya ta. Na san mun daɗe acikin abokantakar mu da har jin kanmu muke tamkar yan'uwa. Amma abunda ke ruɗa ni shine, a duk wannan shekarun da muke tare, zuciya ta bata iya son wata ƴa mace. Don Allah ki karɓi ƙauna ta.
Dukannin abokai na gani suke kaman muna soyayya da ke. Jin hakan daga gare su sai na ga ba karamin dacewa zamu yi ba, a matsayin saurayi da budurwa. Ban sani ba ko ke ma kina ganin hakan?
Ni fa na lura da wani abu, a duk ranar da nake ganin ki, sai in ringa jin wani daɗi a cikin zuciya ta, sauran ranakun da bana ganin ki kuma sai in ji sunyi tsawo. Ballantana ma idan naje kwanciya da daddare, sai naji kamar gari ba zai waye ba. Cin menene hakan take nufi?
Cin menene yasa nake ji kamar ke wata gaɓa ne na jiki na? Menene yasa a duk lokacin da nake ciwo, da na ganki sai in warke? Menene yasa nake jin kamar ba zan iya rayuwa ba idan ba tare da ke ba? Don Allah ki amince ki zama budurwa ta.
Barka dai kyakkyawa. Na daɗe ina mafarki akan ni da ke muna soyayya. Na ɗauki tsawon lokaci ina nazari akan wannan mafarkin, sai naga ashe son ki ne ya mamaye mun zuciya da har tunani na. A duk lokacin nayi yunkurin faɗa maki, sai inji na ƙasa. Allah yasa mafarki na ya zama gaskiya a zahiri.
Da akwai wani abu tattare da ke, Kin sha babban da sauran matan da nake gani. Kin sami guri a zuciya ta kin zauna; bata samun sukuni idan bata ganki ba. Ki yarda ki zama masoyiya ta mu kafa tarihi a soyayya!
Da fatahn kin tashi cikin ƙoshin lafiya. soyayyar ki tana sanƴa ni hauka. Na rasa yarda zana yi. A duk lokacin da nake kusa da ke, bana iya maida hankali akan abunda nake yi. Ke kaɗai ce kawai zata iya mani magalin wannan damuwa. Ki sautata wa zuciya ta.
Da akwai wata yarinƴa, muryar ta na sani nishaɗi, murmushin ta tamkar magani ne a waje na, takun ta na bani natsuwa. Ina ma ace zata ɗauke ni a mastsayin saurayin ta! Da na zama mutum mafi fari ciki a faɗin duniyar nan. Ita wannan yariƴar dai ban san ta ba, amma nasan ita ke karanta wannan saƙon.
Ƴar kyakkyawa. Ya kasance 'yan watanni da sanin junar mu, kuma na ji daɗin kowane lokaci daga yan watannnin.. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi tare. Shi ya sa nake tambayarki ki zama budurwata.
Ke sarauniya ce. Wata nau'in da ya dace da duk kyawawan abubuwan rayuwa. Bari in kula da ke. Bari in zama mutumin ki. Ina so na zama wanda zaki kira naki. Kalma ɗaya ce kacal zai ɗauke ki kuma mu zama na juna.
Ina tunanin yadda nake iya rayuwa ba tare da ke ba a rayuwata, da kuma yadda na kasance tare da ke a rayuwata. Ina ganin yanzu ina bukatar ki a rayuwata. Eh wannan ni ne nake tambayarki ki zama budurwata.
Ana kiran sunanki, kwatsam hankalina zai tashi. Ina jin kamshin turarenki sai kwakwalwata ta lalace. Ina ganin ki kuma hakan ma ya fi muni saboda ya ina fara jin kamar an shanye duk iskan da ke cikin duniyar. Ba zan iya numfashi ba tare da ke ba. Ina so ki zama budurwata.
Wannan sakon ya sha bamban da sauran sakonnin da nake aiko maki. Eh, barka da safiya. Ee, ina son ki. Amma wannan ina neman ki zama budurwata. Zan jira amsar “eh” daga gare ki. Ina son ki
Yau, na kawo karshen bincikena. Na samo ƴar yarinya kyakkyawa, kuma ita ce ke karanta wannan saƙo a halin yanzu. Zaki zama budurwata?
Na tuna karon farko da muka fara yin magana. Na tuna tunanin yadda muke magana da kuma haɗa kan ƙananan abubuwa waɗanda ba su da mahimmanci. Amma abinda ya kama ni ke nan. Ke gaba ɗaya kin mamaye min zuciya. Yanzu kamar ba zan iya cire ki daga cikin raina ba. Ina so ki zama tawa.
Ina son ki a matsayin ƙawa da 'yar'uwa, amma ina so in so ki a matsayin budurwata, kuma matata nan gaba in Allah ya yarda. Ya ke maryam, za ki zama budurwata?
Kowane bangare na rayuwata cikakke ne ko kuma kamar sun cika, ban da bangare guda. Wannan bangare yana buƙatar ki cika shi. Da wannan nake neman ki zama budurwata, kuma ina fata za ki ce eh.
Bayan zama tare da ke, na san cewa, babu mace kamar ki. Akwai abubuwa da yawa da zan yarda in daina. A yau, ina tunanin lokaci ya yi da ya gamata in faɗa maki babban abu ɗaya da nake so daga gare ki. Zaki zama masoyiyata?
Sannu, masoyiya. Ba na kallan ki a matsayin abinda nake ganin ki a da. Yanzu ina ganin ki a matsayin wanda zan iya iya kira da masoyiya. Ina so ki zama budurwata ki barni in tsaya maki a duk lamuran ki. Ina fatahn samun amsa mai kyau.
Assalamu alaiki. Na zo da magana marar daɗin ji, magana ce mai daɗi a waje na amma ban san yarda zaki ɗauke ta ba. Duk lokacin da nake tare da ke sai inji ruhina gaba ɗaya ya amsa. Ji fa nake kaman na kamu da son ki.
Barka dai. Nayi zaman tare da mata da yawa, daga ƙawaye har zuwa maƙota. Amma ban taɓa jin yarda nake ji ba game da ke. Kin kasance mace ta daban a waje na. Zan yi farin ciki matuƙa idan har zaki amince da soyayya ta gare ki.
Ban taɓa sanin yanda ake ji ba idan an faɗa soyayya sai da na kamu da son ki. Abun ya baki mamaki koh? Ehhh! Na fara sonki tun daga ranar da na fara ganin ki. Kuma na san ke ma kina so na. Mai zai hana mu haɗe, mu ma muji yarda ake ki?
Tsakanin lokacin da na aiko maki da wannan saƙon da lokacin da amsar ki zai zo gare ni zai kasance mafi tsawon lokaci a rayuwata. domin wannan rubutun ba na komai bane illa ki zama budurwata. Yanzu jira ya fara.
abinda nake so in yi a yanzu shi ne in haɗu da ke in gaya maki abinda ke cikin raina. Amma tunda ba zan iya zuwa wurinki ba a yanzu, wannan saƙon zai mara girɓin. Ina so ki zama budurwata. Ina fata ke ma kina son na.
Yau an fara mani akan bayani mai haske kuma yana ƙara kyau. Amma hanya mafi kyau don kawo karshen ranar shine kasancewa da ke a matsayin budurwata kafin yau ya ƙare. Allah ya tabbatar mun da nufi.
Ya kike ƴan mata? Ina aika wannan saƙon ne saboda a yanzu wannan ita ce hanya mafi sauki da zan iya faɗa maki zuciyata. Ina so ki zama mun kasoyiya kuma ina fatahn kina so ki zama tawa. Ina son ki.
Da fatahn kina lafiya. Ki tuna na faɗa maki na ga wata ina so. Ina ganin sauran abinda ban gaya maki ba shine, Ke ce wannan macen. Don haka, don Allah, ki zama budurwata.
Lokaci ya yi da zan zauna da wata, wacce zata kwantar min da hankali. Kuma ke ce nake so kuma ke nake bukata. Don Allah, ki amshi ƙauna ta.
Ban taba tabbatar da wani abu ba kamar yadda nake son kasancewa cikin soyayya da ke. Na san akwai abubuwa da yawa da za mu iya aiwatar a tare, kuma ina fatahn ra'ayin ya zama ɗaya.
Masoyiya. Wannan yana da wuyar faɗi, amma na duba kuma na kammala cewa rayuwata ba za ta cika ba idan ba ke a cikin ta.
Akwai wani abu da nake so in tambaye ki na ɗan lokaci, amma na ɗan jinkirta saboda ina so in tabbatar da lokacin da ya dashe. Ina tunanin yanzu ne ya dashe. Don haka ina tambaya, ko za ki zama budurwata? Don Allah a ba ni eh a matsayin amsa.
Da fatahn ranarki tayi kyau kamar kyakkyawar fuskarki? Da fatahn yana da ban sha'awa kamar kyakkyawan murmushin ki? To, ina son wannan fuskar da murmushin su zama tawa daga yau. Ko ya kika gani?
Ina da shawara. Cewa mu yi sauran rayuwar mu tare, muna rayuwa cikin biyayya da ƙauna. Kina son wannan shawarar? Kin a so mu bi ta?
Akwai abubuwa da yawa da nake kiran ki a gaban abokaina. Ina so a sami ɗan canji. Ina so in kira ki budurwata a gabansu daga yau. Eh, ina so ki zama masoyiyata. Da fatahn ke ma kina son hakan.
To ga ni nan na sake mika gaisuwata. Amma yau, na zo da wata bukata. Zan yi shi a cikin tambaya guda: za ki zama budurwata?
Yanke shawara na iya zama da wahala, amma akwai lokuta, irin wannan, duk wani zaɓi da kike ɗauka ba zai ɗauke maki wani abu mai kyau ba. Amma ina so ki yanke shawara ko za ki so in zama saurayi a gare ki. Domin ina son ki a matsayin budurwa ta.
A yau, na farka da ɗawainiya ɗaya a zuciyata kuma yanzu kawai zan iya yin shi. Wannan shine in nemi ki zama budurwata.
Barka da safiya. Ban san yadda safiyarki ke tafiya a halin yanzu ba, amma ina fatahn abinda zan tambaye ki zai kara masa yaji. Zaki zama budurwata?
Da fatahn kin tashi da tsare-tsare na rana ta musamman? Idan haka ne, to ina ganin wannan shine abu na musamma game da ranar: cewa ina neman ki zama budurwata daga yau.
. Na yi tunani game da ƙayyadaddun bayanan da kike so a cikin mutum kuma ina ganin na cancanci hakan. To, ke kuma duk kina tafsiri na ga macen da nake so. Don haka menene zai hana mu taru muyi rayuwar mu tare?
Daga karshe na yanke shawara akan abinda nake so kuma, da fatahn cewa ke ma kina son hakan. Da wannan shine nake neman ki zama budurwata.
Ina fatahn wannan saƙon ya same ki da jin daɗi. musamman yadda saƙonni irin wannan ke canza yanayi na mutum. Ina so in kasance da ke a matsayin abokiyar tarayya a cikin soyayyar mu. Ina jiran amsa.
Yarinya. Akwai abubuwa da yawa da zan iya gaya maki, amma abu mafi nauyi a raina, wanda zan kawar da shi, shine abinda zan faɗa da farko - kuma yanzu. Ina son ki zama budurwata?
Ina so in yi amfani da rayuwata gaba ɗaya don faranta maki rai, kuma na yi alkawarin kasancewa tare da ke a cikin kowane yanayi mai kyau da mara kyau. Zan zama dutsen ki, goyon bayanki, kuma babban abokin ki. Zan ƙaunace ki da dukan zuciyata.
Ina son komai game da ke: tunanin ki, ra'ayin ki game da rayuwa, burin ki da sha'awar ki, kuma ba shakka, kyawun ki. Don Allah ki yarda ki zama budurwata a yau.
Ba zan iya fatahn samun ingantacciyar rayuwa fiye da wacce zan yi tare da ke ba, idan kin bani dama.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here