200+ Sakonnin Soyayya Na Dare

 

1 - 100 = sakon zuwa ga saurayi

101 - 200 = sakon zuwa ga budurwa

Sakonnin Soyayya Na Dare Zuwa Ga Saurayi

  1. Masoyi na, dafatan ka wuni lafiya? Kamar yadda kake cikin tinani na tun safiyar yau har zuwa wannan daren, inaso kasani cewa haka zan cigaba da kulawa dakai gobe, jibi, gata har zuwa daren da bazai zo. Ka kula mun da kanka.

  2. Duk dare idan na zauna ina kallon taurarin dake sama suna haskaka samaniya, babu tinanin danake yi kamar lokutan da muka kasance tare da juna muna soyayya. Ka nuna mun so ta hanyoyi daban daban. Ka barni da duk dalilin da zai sa nakara sonka, ka dauke duk wani dalili da zai sana ki ka. Ina kaunar ka habibi na.

  3. Duk sanda kake tare da ni, komai nawa ninkawa yakeyi. Bana iya boye farin cikin da nake ciki a duk sanda muka hada ido da kai. Harso nake safiya tayi ta wuce, rana tazo ta tafi, soboda nasan idan dare ta kusanto, kana tafe akan hanyar zuwa inda nake. Ai dole na kasance cikin farin ciki.

  4. Dama ace kana tare dani wannan daren, dana kara tabbatar maka da irin kaunar da nake maka. Zuciya ta har wani irin yanayi na farin ciki take shiga duk sanda za kazo gare ta.

  5. Masoyi na, tunda katafi ka barni a wannan lokacin zuciya ta ke ta tinani akanka, nayi kokarin sanyaya hakan amma tafi saurara ta. Abunda take bukata itace muryar ka. Shin ko zaka iya bamu labarin so?

  6. Aduk sanda dare yayi, rana sai taje kewaye, awannan lokaci mutane na amfani da hanyoyi daban daban dan samun haske, amma kuma ganin ka duk dare tamkar kasancewa cikin haske ne.

  7. Ina matukar so dare tayi amma bana so naga ta kare soboda awannan lokaci ne zuciya ta take azarfafa mun tinanin ka. Hakan sai yasa ni kewar ka. Ina kaunar ka masoyi na.

  8. Safiya lokacin nazari da tinani akan rayuwa, shikuma rana lokacin aiki. Amma shikuma wannan lokaci mai albarka, lokacine na hutu, soboda haka, dafatan kana lafiya hubbi na, idan ka kamo hanyar zuwa nan, kazo da sauri.

  9. Masoyi na, inaso kayi mun wani abu guda daya. Yau nasan ka gaji sosai bayan ka tashi daga aiki. Dan haka inaso ka zauna agida, kada kaje ko ina, ka zauna ka huta kayi bacci da samun isashen lafiya. Kasan lafiyar ka tana da matukar faida a rayuwa ta.

  10. Kasan mene ke sani farin ciki duk dare? Hankalin ka na tare dani. Da rana hankalin ka na kan aikin da kakeyi. Da safiya hankalin ka yana kan yan gidan ku, amma duk dare, wannan lokacin tawace ni kadai. Wannan ya isheni farin ciki.

  11. Masoyi na, bansan inda kake yanzu ba, amma inaso kasani cewa, aduk inda kake, kasaka a zuciyar ka zuciya ta da taka sunzama daya. Ka kula mun da kanka. Barka da wannan daren.

  12. Nifa nagaji da jiran ka, kayi sauri kazo, zuciya ta ta kosa tagan ka. Ji take kamar tafita daga jiki na tazo gare ka dan daga sanda ta ganka, kamar anyi mata bishara da kasancewa cikin farin ciki

  13. Masoyi na, barka da wannan lokaci mai faida. Inaso kasani cewa duk abunda kasaka a ranka kuma ka bisa da addua, ana dacewa sosai. Dan haka inaso kasaka duk wani buri da kake da ita a wannan dare. Ina maka fatar nasara.

  14. Masoyi na, haryanzu kiran ka nake jira kafin na kwanta bacci. Muryar k ace zata sa naji dadi dadin bacci. Ina kaunar ka habibi.

  15. Daga sanda rana ta fadi, sai taurari su fara bayyana a cikin samaniya suna haskaka wa. Dan haka nakeso dani da kai mu kasance acikin farin ciki wuce yadda muke ci a baya. Inaso na kula da kai tamkar ina kula da kaina, inaso in kula da kai tamkar ina kula da dukiya na. Kai na daban ne a cikin irinka ba adadi.

  16. Naso da’ace muna tare a wannan daren soboda iskar daren nan, kyanta na shata a kusa da masoyi na, ayayin da yake bani labara. Matukar nasamu hakan, bazan taba manta irin wannan yanayin ba.

  17. Duk idan na tina lokutan da muke kasance wa tare, sai naji ni cikin wata yanayi tamkar bana wannan duniyar. Amma kuma kuma a zahiri gani acikin ta. Habibi na, inaso kayi mun alkawarin kulawa da zuciyar ka fiye da yadda ka saba kula da ita.

  18. Rayuwa kenan, da safe natashi bana kusa da kai. Da rana kuma na wuni ina tinanin ka, da dare yayi, sai na sakaka a idanu na. Kullin idan nafara tina irin nishadin da kake bani sai naji kamar karka tafi. Ina kaunar ka.

  19. Masoyi na, idan banfada maka abunda ke cikin zuciya ta ba, gaskiya banyi ma kaina adalci ba. Duk sanda muke tare da kai, ka tafi, kwalla ce ke zuba a idanu na, banso muna rabuwa da juna. Amma kuma babu yadda muka iya.

  20. Barka da wannan lokaci mai albarka habibi na. Aduk sanda tinanin ka tazo mun, sai naji kamar nazama tsuntsuwa ina tashi acikin sama. Idan na kwanta bacci nafara tinanin ka, soboda in tabbatar da ba mafarki nake ba, sai na tsunguli kaina. Daga nan nasan ba bacci nakeyi ba. Babu rabon da ya wuce samun saurayi irin ka a doran kasa.

  21. Ni yanzu na daina kewar ka kasan meyasa? Soboda idan bamu tare kana cikin zuciya ta. Idan kuma dare yayi kafin na kwanta sai na ji muryar ka. Idan kuma nafara bacci kana zuwan mun a mafarki na. Ina kaunar ka.

  22. Inaso kasani cewa, kamar yadda rana ke da matukar amfani gun bada haske da kuma samar wa shuka sanadari, haka kake a cikin zuciya ta, ka shigo cikin zuciya ta, ka haskaka ta ka samar mata da farin ciki da nishadi. Babu abunda zai sana rabu da kai sai dai rai yayi halin sa.

  23. Masoyi na, dafatan ka wuni lafiya, barka da wannan dare mai tarin abun mamaki. Nakasa bacci soboda yawan tinanin ka. Gaskiya nakosa nasaka a idanu na gobe. Dafatan zamu hadu goben.

  24. Kafin na hadu dakai, duk dare idan na zauna saina rasa mene ke mun dadi. Bansan meyasa hakan ke faruwa ba. Amma kuma abun mamakin shine daga ranar da na fara ganin ka, duk wannan ya daina. Sai na fahimci cewa akwai wata gurbi a rayuwa wanda kai ne ka cika ta. Nayi dacen samun ka. A kwana lafiya habibi na.

  25. Masoyi na, dafatan ka wuni cikin koshin lafiya; ya aiki kuma? Inaso na maka wata tambaya guda daya; idan ina tinanin ka, natsuwar da nake samu tana tafiya ne da lokutan dana dauka ina tinanin ka, wannan kauna ce?

  26. Yau na kasa cire tinanin ka a cikin zuciya ta. Nasan yau agajiye kake. Ina so na kara jaddada maka kauna ta agare ka. Ka kulamun da kanka. Ina mana fatar mu wayi gari lafiya.

  27. Kaine namiji mafi mahimmanci a rayuwa ta, duk sanda tinanin ka yazo mun, sai naji wata kwarin gwiwa ta shige ni. Duk abunda nakeyi tinanin ka yazo mun, cikin farin ciki da nishadi nake wannan abun. Zuciya ta na mika gaisuwar ta gare ka, ka amshe ta hannu biyu.

  28. Duk ranar dana kuma nagama ba tare da nagan ka ba, wannan ranar cikin kunci nake wuni. Shiyasa nakeso duk safiya nakeso naji muryar ka, duk dare kafin na kwanta na zolaye ka. Hakan yasa na dau waya na da mahimmanci.

  29. Habibi na, dafatan kana cikin koshin lafiya kamar yadda nima nake ciki. Meyasa baka fara bacci ba. Ko dai kana kewa ta ne. Kayi hakuri safiya nayi zaki ganni cikin farin ciki da aminci. Karka damu hubbi na.

  30. Nasan yanzu kana agajiye masoyi na, kuma kasan nace maka ka daina gajiyar da kanka. Babu damuwa yanzu zanbaka tatsuniya mai dadi dan hankalin ka ya kwanta. Ina fatar hakan ta saka farin ciki.

  31. Na kwanta amma nakasa bacci. Kuma nasan kaima haka bakayi bacci ba. Tunda muna kewar juna, sai mu zauna tare dukkanmu har safiya. Dafatan ka wuni lafiya.

  32. Tunda ka shigo cikin rayuwa ta, farin cikin danake ciki ya linka, nishadin danake ciki ya linka, Karin gwiwan danake samu ya karfafa, abubuwan alkhairi suka yawaita duk soboda kai. A littafin tarihin rayuwa ta, kaine a farko.

  33. Yau ne kawai bamu hadu da kai ba soboda uzuri yayi maka yawa. Kwana daya kawai, amma jinake kamar munyi shekara 5 bamu hadu da juna ba. Aduk sanda ka samu lokaci, ina nan ina jiran ka zuwan ka. Ina kaunar ka.

  34. Kace mun baka taba soyayya ba, amma kuma yadda kake kula ni bai nuna hakan ba. Ni har na fara kokwanto akan hakan. Indai gaskiyar kafadamun, wannan babbar rabo ne kasamu wanda ba kowa ke da irin ta ba.

  35. Masoyi na, barka da wannan lokaci, nakasa samun sukuni a zuciya ta wanda kuma muryar ka ke samar da ita. Inaso kayi ma zuciya ta magana, tana nan tana jiran ka. Ina kaunar ka.

  36. Masoyi na, inaso kafada mun, mene ne kake yi duk dare bayan ka koma gida soboda zuciya ta na fada mun kana wahalar kanka bayan kasan kana da ni. Bana so kana shiga damuwa habibi na.

  37. Kasan wani abu? Duk sanda naje kwanciya banji muryar ka ba, baka tura mun sako ba, sai naji kamar nayi maka laifi ne. Idan laifi nayi maka kayi hakuri habibi na. Bani so kana fushi da ni. Barka da wannan lokaci.

  38. Inaso ka kalli sama cikin wannan dare ka nuna mun wani tauraro ne nawa. Nayi nasarar nemo taka cikin sauki. Zuciya ta takosa ta ganka.

  39. Barka da wannan lokaci habibi na, nazo maka da wani abun mamaki. Kasan meyasa duk dare kake jin hankalin ka a kwance, soboda duk damuwar daka dauko tin safiya, rana ta dauke maka ita, da dare tayi sai ka kasance cikin far’a ayayin dani kuma hakan ke sani nishadi. Ina kaunar ka.

  40. Nurul hayaty, inaso nayi maka godiya akan abubuwa wanda ta sanadiyar ka ce nasame su. Kullin cikin nishadi nake kasancewa, duk dare kuma na kwanta cikin nishadi. Ina matukar godiya da hakan.

  41. Dare lokaci ne wanda mutane ke zama suyi tinani akan abubuwan da sukayi a wunin gaba daya daga safiya har daren. Dan haka na turo maka fure ta soyayya tare dayi maka fatar alkhairi ayayin da kake wannan tinani. Ina mana fatar dace wa aduk abunda mukeyi na alkhairi.

  42. Masoyi na, aduk lokutan dake cikin wuni, babu lokacin da nafi so kamar dare irin wannan. Soboda a wannan lokaci ne kake hutawa bayan ka tashi daga aiki. A wannan lokacin ne nake sakaka a idanuna. A wannan lokacin ne zuciya ta ke kwance cewa kana lafiya.

  43. Kasan wani abu, inda nake, me nake yi, inaso kasani cewa a cikin zuciya ta, kaine sarki. Yadda kake so, hakan za’a aiwatar. Daga ranar da muka hadu har yau, naga abubuwa wanda banyi tinanin zansame su ba, sunzo gare ni.

  44. Dare lokacin ne wanda zaisa ka manta duk wani kuskure dakayi da rana. Dan haka inaso ka saka hankalin ka a ruwan sanyi dan hankali na yana tare da kai. Ina kaunar ka habibi na. 

  45. Habibi na, idan a misali aka bani damar na sake wata rayuwa bayan wannan, duk inda ka shiga, sai na nemo ka dan kara wata rayuwar tare da kai. Duk inda kasaka kafa, bakin ciki da damuwa basu iya su leko ba. Nayi matukar dace da samun ka.

  46. Lokaci yayi wanda zaka manta da duk wani abu daya faru yau da kuma shirya wa duk abunda zai faru gobe. Inaso kasani cewa, aduk halin da kake ciki, ni da zuciya ta muna tare da kai. Ina maka fatar nasara.

  47. Kasan wani abun alkhairi da dare kuwa? Lokaci ne wanda idan mutum ya zauna yayi tinani da nazari, yana iya cinma burin sa cikin sauki. Dan wannan lokaci, babu wani takura ko hidimar da zakayi ma wani sai naka hidimar. Dan haka, ina maka fatar nazari mai amfani.

  48. Ina so nafada maka wani abun mamaki, a duk sanda na zauna tinanin ka yazo mun, sai naga ko ka kirani ko kuma ka turo mun sako. Hakan sai yasa nakeso kullin na ringa kasancewa cikin tinanin ka.

  49. Masoyi na, yau tinda na tashi da safe nake tinanin ka har zuwa daren nan gashi ina kuma tinanin ka. Wannan alamun wani abun alkhairi zai faru kenan. Muna maraba da jinsa. Ina kaunar ka.

  50. Inaso kasani cewa duk sanda bamu tare da kai, bana kasancewa cikin jindadi, duk da dai hankalina na kwance, bana samun natsuwa kamar yadda nake samu idan muna tare da kai.

  51. Babu wuri mafi kyau, tsari, kwalliya, kwanciyar hankali, abubuwan nishadi dana alkhairi, abubuwa na ban dariya masu sa nishadi kamar cikin zuciyar ka. Dan haka ni achan nakeso na zauna. Ina maka fatar alkahari da kuma fatar tashi cikin farin ciki da koshin lafiya.

  52. Ina maka fatan alkhairi tare da manta duk wani abun da ke damun ka duk dai baka fada mun ba. Kasan wani abu? Ina kaunar ka.

  53. Dare basu cika a wurina matukar nida kai bamu hadu ba. Duk da dai taurari na haskaka sama tare da saka mana kwanciyar hankali. Babu tinanin da nake yi illa ranar da fuska ta zata kara ganin fuskar ka. Dafatan kana lafiya?

  54. Kasan wani abu? Kana ko ina a rayuwa ta. Idan muna tare, zuciya ta na cikin farin ciki. Idan bamu tare, kana cikin tinanin ka. Aduk sanda kuma bacci ya dauke ni, sai nayi mafarkin ni dakai muna cikin farin.

  55. Masoyi na, inji manyan mu sunyi wata karin magana cewa “babu wajen dayafi kwanciyar hankali kamar gida” dan haka yanzu, kaine gidan, nikuma zanyi duk abunda zai sa nakasance a cikin wannan gida kofa a kulle soboda kada nasamu abokiyar takara.

  56. Ina cikin bacci nafarka soboda akwai abunda na sabayi duk dare da banyi ba. Masoyi na, ina kaunar ka bil haqqi.

  57. Tunda nake, bantaba ganin, fuskar mai kyan kallo kamar taka ba. Bantaba jin wani murya mai dadin ji kamar ta ka ba. Kuma wata yanayi dayafi sakamun natsuwa kamar kasancewa tare dakai.

  58. Rayuwa dai ance da sauki take. Dan haka inaso kayi mun wata alfarma. Ka mayar da bakin ciki na nishadi. Ka mayar da bata na zuwa nasara. Ka mayar da lokutan bakin ciki na zuwa nasara. Kai kadai nake bukata dan chanza duk wani abu sabanin kyau a rayuwa ta.

  59. Duk sanda na kalli tauraro a cikin samaniya, sai naji tamkar kai nake kalla, hakan sai ya kwantar mun da hankali sai naji kamar nazama sarauniya a wata masauratar.

  60. Inji mayan mu masana rayuwa suka ce, babu wata lokaci datafi dare acikin wuni. Zaka fita aiki ka dawo gida agajiye. Amma shi dare kana gida kana hutawa. Mafi yawancin abubuwan dake sa farin ciki, duk sunfi kasancewa a dare.

  61. Ni yanzu bani da wata damuwa, kuma banda wani dalilin kasancewa cikin damuwa. Soboda ina da saurayi daya tamkar darin wasu. Ina kaunar ka sosai.

  62. Masoyi na, barka da wannan lokaci. Kashigo cikin rayuwa ta ka share duk wata bakar kala ka sanya mun farar kala. Duk wani rashi ya kowa samu. Nagode da shigowar ka rayuwa ta.

  63. Amfanin ka a rayuwa ta, bazai iya misaltuwa ba. Inda ban hadu dakai ba, tayaya zan iya tsallake duk wannan kalu balen rayuwa wanda na fuskan ta. Barka da wannan lokaci habibi na.

  64. Duk sanda bamu tare, duk wata magana da mukayi lokacin muna tare dakai, suke mun yawo acikin kaina. Kai din jigo ne a cikin samarai na musamman.

  65. Sarki a rayuwa ta, akanka nasan wata mafarkin na zama gaskiya, tunda duk abunda nayi mafarkin sa, ina samun hakan cikin kankanin lokaci. Kaine ainihin kwatance abunda zuciya ta ke bukata.

  66. Awannan kwanakin, babu abunda nake tinani kamar yadda nake ji aduk sanda muke tare ko kuma ina zaune ni kadai. Yanzu haka da sunan ka ake kira na. Barka da wannan lokacin masoyi na.

  67. Zuciyata ta tanadar maka da wani abun mamaki. Amma kuma bazan fada maka mene ne ba sai mun hadu dakai gobe. Ina kaunar ka habibi na.

  68. Kaine irin saurayin da zuciya ta ke bukatar samu kuma tasamu hakan. Duk wani abunda kakeso nayi maka, zanyi hakan matukar zai sakaka farin ciki. Barka da wannan lokaci.

  69. Ina so na kara tina maka cewa ina kaunar ka. Kamar yadda kake cikin farin ciki akoda yaushe, hakan ne sirrin farin cikin da nake ciki.

  70. Bansan inda zan saka kaina idan ka rabu da ni ba. Bana so wannan tinanin yazo mun. kaine wanda zuciya ta ke son gani a duk yini. Ka kula mun da kanka baby na.

  71. Duk abunda nayi, soboda kaine. Duk abunda na fada, da manufar ka nafadi hakan. Tinanin ka ya baibaye duk wata zabi da nayi ma kaina duk soboda kaunar da nake maka. Barka da wannan lokacin.

  72. Na tina ranar daka fara kusanta ta. Nayi tinani da fatar kasancewa da kai tazama alkhairi. Cikin ikon Ubangiji, gashi fatar da nayi tazama dagaske. Kayi mun abubuwa wuce yadda nake tinani akanka. Ina kaunar ka.

  73. Murmushin ka yakan tina mun da ranar da muka fara haduwa. Wannan ranar ba abunda zan iya mantawa cikin sauki bane. Duk idan tinanin yazo mun, murmushi kawai nakeyi cikin farin ciki.

  74. Kasan yadda na dauke ka a zuciya ta kuwa? Mutane suna daukan ka masoyi da kuma saurayi agare ni. Amma ina farin ciki sanar da kai cewa a zuciya ta, kafi hakan sosai. Kazamo kamar amini wanda narasa samu. Wannan gurbin kaine ka cika ta.

  75. Akwai wani abu da kamin wacce bazan taba manta tawa ba. Ka kara tabbatar mun da cewa akwai mutanen kirki a wannan duniyar. Kuma nagode da hakan. Ina kaunar ka baby na. Ba karamin farin ciki nakeji ba idan nakira ka da babyn baby.

  76. Misali yanzu na cire ka a zuciya ta, babu abunda ya rage a cikin rayuwar tunda dama kaine acikin ta duk wani a wurin soboda kai yake wurin. Ina maka fatar alkhairi baby na. Ka kula mun da kanka.

  77. Ina kaunar ka kuma zan iya zuwa ko ina a duniyar nan na tabbatar wa duniyar kai nawa ne soboda duniya ta tabbatar da soyayyar da nake maka. Ina kaunar ka hubbi na.

  78. Tunda ka shigo cikin rayuwa ta komai ya chanza. Idan na zauna har tinani nakeyi akan yadda rayuwa ta take kafin zuwan ka cikin ta. Ka bani duk abunda kayi alkawari kuma ka kara da abunda ma baka fada ba. Ina matukar godiya da hakan kuma ni ma ina da kyautar da nake so nayi maka.

  79. Nagode wa Ubangiji daya hada mu tare da juna. Idan muna tare da kai. Natsuwa, farin ciki, da duk wani damuwa duk tafiya suke yi. Idan kuma baka nan, sai naji kamar an cire mun wani abu cikin zuciya. Barka da wannan lokaci mai abun mamaki.

  80. Kalamai bazasu iya misalta irin farin ciki da nake ciki alokacin da nake tare da kai ba. A wannan lokacin zan iya bada kyautar duk wani abu da na mallaka. Ka nuna mun kauna fiye da yadda nake tinani. Ina kaunar ka habibi na.

  81. Bara nafada maka wani abunda baka sani ba. Duk sanda muke waya da kai, sai nayi recording soboda nasan ba kullin ne muke tare ba, ba kullin muke magana da juna ba. Dan haka idan nafara kewar ka, sai nasa najishi kamar inajin waka sai naji sauki a zuciya ta.

  82. Masoyi na, nasan yanzu ka kama hanyar zuwa gare ni. Idan zaka fita daga gida, ka nemi tsarin ubangiji yayin da zaka fito daga muggan abubuwa. Kuma ka roki ubangiji ya had aka da duk wani alkhairi akan hanyar ka ta zuwa nan. Zuciya ta na nan tana jiran ka kuma tana farin cikin da zuwan ka. Ka kula mun da kanka.

  83. Banso na kasance a cikin tinanin ka soboda kana iya daina tinanin. Ina so na kasance acikin rayuwar ka soboda hankalin ka ya kasance a kaina ko da yaushe. Ina kaunar ka hubbi na. 

  84. Kai kyakkyawa ne, san wanda tasamu kin wacce tayi rashin sa’a. Nakasa cire ka daga tinani na, na kasa samun sukuni. Inaso kasani cewa akwai wacce ta damu da kai. Ka kula mun da kanka.

  85. Babu abunda ke bani kwarin gwiwan kasancewa da kai kamar na tina cewa kana tare dani kana kauna ta. Hakan yasa mun natsuwa sosai. Na daina tinanin komai sai soyayyar ka. Barka da wannan lokaci aminin rayuwa ta.

  86. Ina so kafin ka kwanta, Kamanta da duk wani abunda ke damun ka. Ka saka a ran ka kamar kafi karfin haka. Bana so kana shiga cikin damuwa. Ina kaunar ka.

  87. Tinda dare mukr samun lokacin haduwa da juna, inaso duk idan zakazo wuri na kafada mun soboda nasamu nayi maka kwalliya danka kara ganin kyautar da Ubangiji yayi ma sarauniyar ka.

  88. Ance irin yanayin da kaga mutum acikin sa daddare ke bada zahirin yadda wunin sa ya kasance. Kuma naji dadin ganin yanayin ka wannan dare kuma ina fatar ya cigaba da kasance wa a haka.

  89. Inaso aduk abunda zakayi kazama na daban yadda sai kowa yasan da kai. Inaso duk inda naje na bugi zuciya ta nace kai habibi na ne. Ina kaunar ka. Bani so komai ya faru da kai.

  90. Dare shine mafi soyuwan lokutan da mutun zai iya zama ya huta gajiyar sa, dan haka kaje ka kwantar da hankalin ka kahuta. Kasan banso komai ya faru da kai habibi na.

  91. Lokacin manta damuwa da kuskure yayi. Soboda haka inaso ka manta duk wani damuwar da kake ciki ka huta cikin natsuwa da aminci.

  92. Na turo wa zuciyar ka da sako; sako wacce kai bazaka gane ba sai zuciyar ka kadai. Ina kaunar ka habibi na, ka kulamun da kanka. Kasa nazama ta daban acikin yanmata.

  93. Safiya ta wuce, rana ta wuce, yanzu kuma dare ne. Duk wani rashin farin ciki da ka dauko tun safiyar yau zuwa yanzu, inaso ka bar su duka a bayan ka. Ka kasance cikin annashuwa kamar baka taba shiga damuwa ba.

  94. Aduk abunda kake nema, ina maka fatar kasancewa a kololuwan sa, kazama wanda kowa zai ringa yin koyi da, kazama wanda za’a ringa misaltawa. Inaso kazama sarki a zuciya ta.

  95. Na bukaci soyayyar ka, kabani kyautar zuciyar ka. Na bukaci farin ciki da natsuwa, ka bani har da kanka kyauta. Kasa nazama tauraruwa mai haskakawa. Ina kaunar ka masoyi, ka kula mun da kanka.

  96. Idan na zauna na fara tinanin ka, manta ko wani aiki nakeyi. Bana iya bada misalin irin halin da nake ciki. Amma dai nasan cewa ina cikin farin ciki matuka. Ka kula mun da kanka. Bana so na rasa ka habibi na.

  97. Masoyi na, kamar yadda nabaka soyayya ta, haka nakeso kaima kabani taka. Kamar yadda nabaka zuciya ta, haka nakeso kaima ka bani taka. Duk sanda na kalli fuskar ka, sai naji kamar ina tafiya acikin iska. Dan Allah baby na, karka guje ni.

  98. Aduk sanda nake tinanin ka, sai na koma gida na zauna na kalli sama soboda naga taurarin da yafi kowani taurari haskakawa. Idan naga wannan tauraron sai naji dadi soboda nasan duk kyauwun sa bai kaika ba. Ina matukar kaunar ka. Dafatan kana lafiya jigo acikin sarakuna.

  99. Duk wani abu wanda nake bukata a wurin wani namiji, duk ka hada duka kai kadai. Bani kallon wani kuma tunda abinda nake nima ina dashi acikin gida na. Kaga hankali na ya kwanta. Ka kula mun da kanka.

  100. Dafatan ka wuni lafiya? Inaso yau idan ka tashi daga aiki kazo muje mu shakata. Kullin kana wajen aiki baka samun lokaci. Yau kazo muje mu shakata a wata daular masoya dan muma mu ajiye tarihi. Muma mu shaida haka.

  Saƙon Soyayya na Dare zuwa budurwa

  1. Zuciya ta za ta kasance tare da ke a wannan dare da sauran daren da zasu zo nan gaba. Ina tunawa da kyawun dake cikin ran ki kowace rana da kowane dare. Soyayya ta da son ki na haskakawa a wannan dare.

  2. A kowane dare, yayin da taurari ke haskakawa, zuciya ta tana karyawa, ina son hasken ki, kyalli na soyayya a cikin idanun ki. A daren yau, na hango ki kusa da ni kuma ina jin daɗin kasancewar ki. Na so ace  kina nan tare da ni wannan kyakkyawar lokaci. Ina fatahn zukatan mu za su cika da so da ƙauna mai zurfi.

  3. Lokacin da dare ya zo kuma hasken ke bushe, kyandir shine kawai tushen hasken mu. Muna ɗaga gilashi zuwa kyautar soyayya. Hankalin mu yana gudana kuma zukatan mu suna tashi. Allah ya tabbatar mana da nasara.

  4. Ranar tana ƙarewa, kuma lokaci yayi da za a maraba da dare. Yau magariba ce mai kyau tare da alamun ɓarna a cikin iska, don haka ki ji daɗin sa'o'in dare masu daɗi yayin da suke wanzuwa. Dare zai yi tasiri sosai idan zukatan mu suka buga a matsayin ɗaya. Barka da dare.

  5. Akwai wani abu da ya fi annashuwa da daɗi fiye da dare mai kyau? Dare mai daɗi yana kama da farar daffodils da jajayen wardi. Ke tawa ce; Ni kuma naki ne, kuma na yi miki alkawarin aminci. Rayuwa kamar waƙa ce. Don haka rufe idanun ki, kuma zan rufe nawa yayin da muke rera waƙar soyayya. Tare da ikhlasi, ina so in yi miki barka da dare.

  6. Wannan maraice, Ina mafar ki game da tafiya cikin wurin shakatawa tare da ke, zuciyata tana narke da jin daɗin taɓawar ki tare da kowane matakin da muka ɗauka. Maraice shine lokacin sirrin mu don yin tunani a kan abubuwan da ke faruwa a rana. Don haka yanzu, ina yin miki barka da dare mai annashuwa da barci mai daɗi.

  7.  Ina tsungulin kaina kowace rana don tabbatar da cewa ba mafarki nake yi ba. A duk lokacin da na kalli idanun ki, ina mamakin yadda zan iya kawar da ke. Don haka, wannan maraice mai ban sha'awa, bari mu nutse cikin tekun soyayya! Ina fatahn daren mu zai cika da nishaɗi.

  8. Fiye da yadda kike tunani, Ina son ki tun daga kan ki har zuwa ƙafar ki. Zuciya ta tana ƙuna a duk lokacin da na same ki cikin ɓacin rai, kuma hakan na sa ni bakin ciki. Kina cire duk wani farin ciki a cikin zuciyata lokacin da ba ki tare da ni. Kamar faɗuwar rana ce dake ɗauke dukkan haske da ita a wannan maraice. Ina fatan kin sami rana mai ban mamaki. Barka da dare, masoyiya ta.

  9. Tunani ba game da ke ba ya kasance maras ma'ana. A duk lokacin da na ji muryar ki, ina jin kiɗa a kunnuwa na. Barka da dare, masoyiya ta. Faɗa min harshen soyayya mai daɗi da tafarkin soyayya da ya kamata mu bi. Ki ba ni ƙarfin hali don fuskantar gobe.

  10. Tun lokacin da na fara soyayya da ke, duk lokacin da muka yi tare yana da ban mamaki. Amma ki amince da ni, mafi kyawun har yanzu yana nan tafe. Idan ace na sami wuri ɗaya na zauna, zan zaɓi zuciyar ki, in kuma ace kalmomi uku kacal zan faɗa, kin san me za su kasance.

  11. Abinda nake so fiye da zuciya ta shine ke, domin idan ba ni da ke, zuciya ta za ta daina bugawa. Wannan tuni ne na gaggawa don sanar da ke cewa ina tunanin ki yayin da nake kwance a gado na. Barka da dare, kuma ki tuna kiyi mafarki game da ni domin babu shakka zan gan ki a cikin mafarkina.

  12. Murmushin ki tana da mahimmanci a gare ni, ba wai don a zahiri ina jin daɗin ganin murmushin ki ba amma don yana gaya mani cewa kina farin ciki. A koyaushe ina son ganin ki cikin farin ciki. Barka da dare, masoyiya.

  13. Da ace za ki iya ganin kanki yadda nake ganinki ki ji wa kanki abinda nake ji a gareki, zaki gane cewa kece gareni. Barka da yamma, masoyiya. Komai yawan mutanen da ke cikin gini, duk sun shuɗe a gaban ki da hasken ki. 

  14. Labarin soyayyar mu shine labarin da na fi so. Ina karanta shi akai-akai idan dai tamu littafin labari ne. Ina mamakin yadda na sami damar tsira duk waɗannan shekarun ba tare da ke a rayuwa ta ba. Ba za a iya maye gurbin ki ba. Barka da dare, masoyiya ta.

  15. Na fara jin ina son ki tun daga ranar da farko da na fara ganin ki. Ban san za ki zama muhimmin bangare na rayuwa ta ba. Ina son ki sosai. Rana na iya faɗuwa, amma duk duniya ta tana haskakawa lokacin da kike nan.

  16. Ba ki da masaniya sau nawa na yi tunanin ki a yau. Ba zan iya jira in gan ki in ji yadda ranar ki ta kasance ba. Kina da hanyar canza rana mai wahala zuwa mai daɗi da murmushi. Maraice tare da ke sihiri ne.

  17. Tabbas na ƙaunace ki a rayuwar da ta gabata domin ba zan iya tunanin zuwa gida wurin kowa ba sai ke. Kina sanya dare abinda na fi so a sauran lokuta na rana. Yanzu da dare ya sake zagayowa, ya kamata ki sani ba zan iya barin rana ta wuce ba tare da saki farin ciki ba.

  18. Ina son komai game da ke. Zan gaya miki wannan da farin ciki kowane dare, don ki iya yin barci da sanin ke ce macen da na fi so a duniya. Ina son yin dare na tare da ke. Duk inda kike shine inda na fi jin daɗin kasancewa.

  19. Ba da daɗewa ba, na yi tunanin ko zan taɓa samun mace mai soyayya ta gaske a rayuwa ta. Sa'an nan na haɗu da ke, kuma daren nan ya sanya komai ma ya kara kyau. Ina kewar ki sosai dik lokacin da ba ki nan! Yi dare mai kyau, kuma ki sani cewa ina tunanin ki.

  20. Duk lokacin da aka yita tare da ke kamar mafarki ne. Kasancewar ki a rayuwa ta kamar hasken rana ne a sararin sama na dare. Mafi kyawun sashi na rana ta shine wanda na yi ta tare da ke. Ba zan iya jira in sake ganin ki ba. Barka da dare, masoyiya ta.

  21. Ke ce dalilin da yasa dare na ke cike da farin ciki da annashuwa. Na gode da kasancewa a cikin rayuwa ta. Ina fatan daren ki ya yi kyau kamar ke kan ki. Kin cancanci komai a rayuwa masoyiya ta. Barka da dare, kyakkyawar gimbiya ta.

  22. Duk yadda ranar ta kasance mai wahala, sanin cewa kina jira na a ƙarshen ta ya sa ina iya jure wahalar. Barka da dare, kyakkyawar sarauniya. Mafi kyawun faɗuwar rana ba komai bane idan aka kwatanta da kyawun da kIke kawowa rayuwa ta.

  23. Komai nisa dake tsakanin mu da ke, kina koyaushe a cikin zuciya ta. Barkan mu da dare.  masoyiya ta kuma budurwa ta. Ƙaunar da muke raba ita ce mafi kyawun abu a duniya. ita ce kyauta mafi daraja da zan iya samu.

  24. Kina sa zuciya ta ta yi tsalle a duk lokacin da na tuna da ke. Ke ce  abinda ya ɓace a rayuwa ta da nake ta nema. Allah ya cika daren ki da ɗumbun albarka.

  25. Ina ta kirga lokaci minti bayan minti kawai saboda ƙosawa na don ganin ki. A duk lokacin da rana ta faɗi, sai na ji na kara tuna da sa'a ta na samun ki a rayuwa. Barka wannan dare masoyiya ta.

  26. Ba shakka bana tare da ke a yanzu , amma ina tunanin ki kuma ina miki fatan kyakkyawan dare mai cike da ƙauna da farin ciki. Ke ce sarauniyar dake haskaka mun rayuwa.

  27. Barka da dare! Ina fatan kin sami rana mai kyau da albarka. Komai munin da ranar ki tayi, kyawun faɗuwar rana zai sa komai yayi daidai.

  28. Barka da dare ga rabin rai na. Allah yasa albarkar dake cikin wannan dare ya riske ki ya kuma saukaƙa al'amuran ki. Rayuwa tare da ke yana da daɗi.

  29. Na gode don sanya ranaku na kyau da dare na cike da farin ciki. Ke ce dalilin dukkanin murmushi da dariya na. Ina miki barka da wannan lokaci

  30. Babu ruwan yadda ranar ki ta kasance, ba za ki iya taimakawa wajen kin sha'awar kyawun wannan dare ba. Ina fata kina jin daɗi a yanzu! Barka da dare!

  31. Dare lokaci ne mai kyau don waiwaya baya ga ranar mu kuma muyi tunanin duk abin da muka yi. Yi farin ciki a wannan tare da tunani mai kyau.

  32. Fatan kina dare mai lafiya da annashuwa. Kin cancanci hakan bayan dogon gajiyar rana. Barka da dare, masoyiya ta! Ba zan iya jira don jin yadda kika yi ranar ki ba!

  33. A duk inda nake da abin da nake yi, koyaushe za ki kasance cikin rai na da cikin zuciya ta. Ina kewar ki da yawa a wannan dare!

  34. Dare shine damar mu don manta da kurakuran da muka yi a cikin rana, don haka zakiiya samun hanyar mafi daɗin mafarki. Barka da dare abar ƙauna ta!

  35. Idan ina da wata rayuwa da zan yi, zan sake zabar wani tsawon rayuwa tare da ke. Ina iya samun ainihin farin ciki da nishaɗi ne kawai idan kina rayuwa ta.. Ina son ki. Barka da dare.

  36. Yanzu lokaci ne cikakke don kawar da damuwar ki kuma ki shirya kanki don abinda gobe zata zo miki da shi. Sanya wannan dare ta fari a tafiyar ta tabbbatar da kyaun gobe.

  37. Rana tana faɗuwa kowane maraice tare da alkawarin sake fitowa da wayewar gari. Maraice suna cike da bege da zaburarwa. Fatan kina yin maraice mai ban mamaki!

  38. Wani lokaci, mafi kyawun abinda za mu iya yi ba tunani, mamaki,da kuma damuwa zamu yi ba. Numfasawa kawai zamu yi mu kuma yi imani cewa komai zai yi aiki don mafi kyau. Barka da dare masoyiya!

  39. Barka da dare masoyiya ta. Ina so ki dani cewa na yi tunanin ki a duk tsawon yini, kuma har yanzu ina tunanin ki ne kawai. Ina miki barka da dare. Allah ya albarkace mana wannan lokaci.

  40. Da na dubi faɗuwar rana ta yau, ke ce kawai abinda na ya faɗo mun a rai. Ina kewar ki a duk lokacin da nake nesa da ke. Allah ya kare mun ke a wannan dare.

  41. Barka da dare! Yayin da ranar take bankwana, ina fata za ki ɗauki ɗan lokaci don jin daɗin ɗan farin ciki da kowace rana ke kawowa. Ko yin amfani da lokaci tare da ƙaunatattuna, ko kawai samun lokaci don kulawa da kana ki. Ƙila wannan dare ya zama tunatarwa kan mahimmancin samun farin ciki a halin yanzu.

  42. Barka da dare kyakkyawar budurwa ta! Ke ce mafi kyawun abinda ya taɓa faruwa da ni kuma ina matukar godiya da samun ki a rayuwa ta. Na gode da kasancewa masoyiya a gate ni kuma ina son ki daga zuciya ta har ma fiye da haka. 

  43. Amimcin Allah ya tabbata ga kyakkyawar budurwa ta. Na gode da kasancewa tare da ni da kuma sanya kowace rana ta zama ta musamman. Ina son ki daga zuciya ta kuma ina son yin lokacin mu tare.

  44. Barka da dare ga aminiya ta. Kullum kina sa ni murmushi kuma ina godiya da hakan. Ina son ki daga zuciya ta kuma ina so in zauna tare da ke har abada.

  45. Barka da wannan lokaci ga mace ɗaya tal a rayuwa ta, ba zan taɓa so in rasa ki ba! Idanun ki sun shagaltu kuma kullum suna tuna min, yadda nayi sa'ar haɗuwa da ke.

  46. Barka da dare ga mafi kyawun mutum a rayuwa ta! Kullum kina tare da ni kuma ina da albarka a kan hakan. Ina son ki fiye da komai kuma ina addu'ar zaman mu tare ya kasance har abada.

  47. Gaisuwa ga mace mafi ban mamaki a rayuwa ta! Nagode da amsa addu'ata da kasancewa tare dani. Ina son ki daga cikin zuciya ta.

  48. Ba zan iya taimakawa ba sai dai an jawo ni zuwa kyawawan idanun ki, suna da jan hankali sosai. Ina son ki har tafiyar wata da dawowar ta kuma zan so ki koyaushe.

  49. Ina matukar godiya da samun ki a rayuwa ta, ke mai albarka ce. Ke ne tagwayen harshena kuma koyaushe zan kula da lokacin mu tare. Ina sonki daga zuciya ta kuma ina addu'ar soyayyar mu ta cigaba cikin fahimtar junar mu.

  50. Da fatahn kina lafiya! Na gode da kasancewa a cikin rayuwa ta da kuma raba soyayyar ki tare da ni. Ke ce babbar budurwa da zan iya tambaya. Ina sonki daga cikin zuciyata.

  51. Barka da dare kyakkyawa. Na gode da nuna min alheri tare da kasancewar ki da kuma raba soyayyar ki tare da ni. Idanun ki su ne tagogin ran ki, kuma ina iya ganin duk abinda nake buƙata tacikin su.

  52. Barka da dare amintacciyar abokiya ta. Na gode da ba ni dama da raba rayuwar kuli tare da ni. Na amince da ke da duk abinda kike, kuma na san cewa za ki kasance tare da ni koyaushe. Ina sonki, sweety.

  53. Duk lokacin da na gan ki kina murmushi, hakan yakan haska min duniya ta kuma ya cika ni da farin ciki. Ina son ki daga cikin zuciya ta. Barka da dare kuma na gode sosai da sanƴa ni murmushi a koyaushe.

  54. Barka da wannan lokaci na albarka. Na gode da kasancewa ni'imar da nake fata a koyaushe. Son ki na ƙara shige mun can cikin zuciya a yayin da kwanaki ke wucewa.

  55. Ina so kawai in sanar da ke cewa ina godiya a gare ki da ƙaunar mu. Barka da dare! Kina nufin duniya a gare ni, kuma ina fata kina yin dare mai kyau.

  56. Ina godiya a kowace rana domin kasancewar ki budurwa ta. Kin sa rayuwa ta ta cika. Barka da dare, kyakkyawa. A kowane dare, ina gode wa duniya don kawo ki cikin rayuwa ta. Ina son ki fiye da komai.

  57. Na yi babbar sa'a  da samun ki a rayuwa ta! Kasancewa tare da ke shine kawai abinda ke da mahimmanci a wannan duniyar. Barka da dare, masoyyiya!

  58. Ke ce dalil ina na komai, komai rayuwa zata jefa mana. Barka da wannan dare, masoyiya ta! Ina fatan kina samun dare mai kyau kuma ki sani cewa koyaushe ina tunanin ki.

  59. Ya masoyiya mai girma, ya ya kike yau? Na tabbata cewa duk abinda kike yi yana tafiya yarda ya kamata gare ki. Ina fatahn dare mai ɗumi da ban mamaki a gare ki. Ina son ki Darling!

  60. Tun wayewar gari kina cikin zuciya ta, ina neman wata dama ta mika miki soyayyata. Wannan rubutu shine dabara na na nuna miki irin son da nake miki. Ina son ki, barka da dare.

  61. Ba a banza nake cikin rayuwar ki ba. Ina cikin rayuwar ki ne don faranta miki rai a cikin tafarkin ki na neman rayuwa. Ki sani cewa kina da wani mai son ki a nan. Barka da dare abar ƙauna ta.

  62. Komai munin ranar ki, mai yiwuwar al'amura ba su kasance kamar yadda kike tsammani za su kasance ba. Ki sani cewa wani yana son ki a nan kuma ni ne mutumin. Ina miki fatahn Kyakkyawan dare Gimbiyata.

  63. Rayuwa ba za ta kasance mai inganci ba tare da samun ki a cikin ta ba. Kina da daraja fiye da duk abinda zan iya samu. Kyakkyawan dare a gare ki, Mafi soyuwan aba a wajena na.

  64. Ta yaya za a iya kammala lissafi na rayuwa ta ba tare da sanya ki cikin lissafin ba? Ke ce dawwamammiya, kowane abu mai canzawa ne. Ke ɗin na musamman ne. Mu kwana lafiya masoyiya.

  65. Halin rayuwa bazai yi miki adalci ba, amma ki tabbata cewa koyaushe zan kasance a wurin don in yi miki adalci a kowane lokaci. Na gode da kasancewa a wuri na masoyiya ta, na yi kewar ki.

  66. Barka da dare farin ciki na, na gode da kasancewa a tare da ni don sanya rayuwa ta zama koyaushe tana haske. Babu wanda zai iya yin wannan idan ba ke ba. Kei ce kawai mafi kyau ta kowace hanya. Soyayya mai yawa a gare ki!

  67. Hasken da ke cikin dare na,  ke ce ke tsara shi, ke ce wanda koyaushe ke sanya dare na ya zama abin sha'awa da ban mamaki. Kina da kyau sosai, ina son ki, barka da dare, budurwa ta.

  68. Yaya maraicen ki ke tafiya masoyiya?  Na tabbata kina jin daɗi! Ci gaba da fashewa. Fatah na yana tare da ke daga zuciya. Barka da dare, rabin rai na.

  69. Yayin faɗuwar rana, Da fatahn zaki manta da dukan wahala da ƙalubalen da ranar ta sanya a zuciyar ki. Barka da wannan lokaci, abar ƙauna ta.

  70. Kina da himma sosai, zan iya tabbatar da hakan. Wannan ya sa kika cancanci samun hutu mai daɗi. Da fatan za a ɗauki ɗan lokaci kuma a huta. Yi maraice mai daɗi tare da shakatawa.

  71. Ba zan daina cewa na gode don sanya murmushi a kan fuska ta daure ba. Kin kasance mai tasiri wajen sanya murmushi a fuska ta. Ina son ki koyaushe.

  72. Dole ne in yi murna da abu ɗaya game da ku; kina da kyakkyawar zuciya, kuma ina son sauraron ki a kowane lokaci. Tare da ke dariya ya zama al'ada. Ji dadin maraicen ki, aminiya.

  73. Ina ganin rana ta ba ta cika har sai na sami shigar ki a rayuwa ta. Na gode don ko da yaushe kina cika min rana ta. Ina son ki, kuma ina fatahn Allah ya tabbatar miki da alkhairi.

  74. Ana bukatar manyan abokai a wannan tafiya ta rayuwa. Babban abokiya da kike kasance babu shakka mai albarka ne a gare ni har abada. Ina girmama ki sosai. Sai da safe masoyiya, mu kwana lafiya.

  75. Kyawawan dare shine, duk yadda ta kasance,  yana zama mai daɗi matuƙar zan gan ki ko na ji muryar ki. Yi dare mai daɗi.

  76. Rayuwa ba ta jurewa bane, rayuwa wajen shaƙatawa ne. Jin daɗin rayuwa yana sa rayuwa ta cancanci rayuwa. Shin zan iya buƙatar ki ɗauki wani ɗan lokaci ba tare da ke a rayuwa ta ba? 

  77. Ina fatan kina jin daɗin kan ki a duk inda kike a yanzu.. Abinda nake so a gare ki a wannan dare shine jin daɗi mai yawa. Ki ci gaba da jin daɗin daren  ki komai naki ne.

  78. Kuna iya duba ko'ina kuma ba ki ga dalilin yin murmushi ba. Ina da wani dalili da ya kamata ya saki murmushi. Ki cinka dalilin! Ina cikin rayuwar ki. Wannan ya cancanci yin murmushi!

  79. Ina yi muku fatan dare mai ban sha'awa mai cike da nishaɗi da ban sha'awa. Tabbatar cewa ana kula da ke koyaushe. Komai duk sun kasance naki ne, ki ji daɗn ki.

  80. Abin da nake yi a inda nake a yanzu yana da matukar muhimmanci. Kamar yadda suke da mahimmanci, ba su da mahimmanci kamar faɗin barka da dare zuwa gare ki. Ke ɗin ta musamman ce!

  81. Babu wani abu da zai mamaye zuciya ta da ba zan tanadar miki wuri ba. Kina rufe babban sarari a cikin zuciya ta. Ina son ki sosai.

  82. Na sami dakuna da yawa a cikina na don abubuwa da yawa. Abin mamaki, na gano cewa yanzu kin mamaye ko'ina. Dole ne ki kasance da ƙarfi sosai, Ya ƙaunatacciya ta. Ina kara son ki

  83. Na yi farin ciki da samun ki a matsayin mai mamaye ɗakin da ke cikin zuciya ta. Ina dubawa a ciki sai na ga macen da ta dace ita ne ke mulki a can. Ki ci gaba da mulkin duniya ta, ina son ki.

  84. Abu ɗaya ne a sami aikin da ya cancanta, wani abu kuma samun hannun mai iya aiki wanda zai iya aiwatar da shi. Ni ne aikin, ke ce mai zartarwa. Na gode da kyautata min. Barka da dare, masoyiya ta.

  85. Da a ce an mika zuciya ta a hannun wanda bai san darajar ta ba, da lalacewa ta faru a yanzu. Na yi farin ciki da kika san darajar zuciya ta. Na gode don kiyaye zuciya ta.

  86. Ba na buƙatar damuwa da abinda kike da shi ko abinda ba ki da shi. Matukar kina da ni, ki tabbata, komai zai daidaita gare ki. Ci gaba da nuna min ƙauna tawa!

  87. Barka da dare masoyiya ta, ko akwai wani abu da ya isa ya hana ni son ki? Lallai, ba komai! Ƙauna ta gare ki madawwamiya ce. A yi dare lafiya. Soyayya mai yawa a gare ki a yau!

  88. Barka da dare bugun zuciya ta. Yana da matukar farin ciki samun ki a matsayin na musamman wanda zuciyata ke so. Yaya ranar ki ta kasance? 

  89. Barka da dare masoyiyata kyakkyawa. Wannnan dare ta kasance tamkar ki. Cike da launuka, kyakkyawan kyawawa. Da fatahn zaki yi barci mai daɗi.

  90. Barka dai sarauniya, ban buƙatar tambayar yadda ranar ki ta kasance! Ina jin girgizar nasarar da kika samu a yau. Nasarar ki ita ce farin ciki na. Ci gaba da nasara, ya masoyiya!

  91. Komai kyawun safiya ko yadda hasken rana ke haskakawa, dole ne su mika kan su ga wannan dare. Allah ya sa duk abinda ke cikin rayuwar ki a wannan dare ya kawar miki da wuya. Ki ji daɗin daren ki!

  92. Dubi sararin sama, yana da haske da ban mamaki. Wannan shine abinda dare zai iya ba ki. Mai yiwuwar wannan dare ya kawo miki mafi kyau. Ji dadin shi, Sarauniya!

  93. Sannu masoyiya, ina fatahn kina samun dare mai karfafawa kamar yadda nake samun tawa a nan. Tabbatar kina yin hakan. Barka da dare, Ƙaunar rayuwa ta.

  94. Dare yayi ba tare da tuntuɓar ki ba. Wannan ya kamata ya ba ki dalilin da ya sa bai kamata ki damu da wani abu ba. Haka magariba take zuwa ita ma. Haka kuma nasarar ki za ta zo. Barka da yamma masoyiya!

  95. Ina so in yi miki barka da dare marar hargitsi da tashin hankali. Allh ya kawar miki da duk tashin hankalin da ke kewaye da ke a wannan dare mai albarka. Ina son ki sosai.

  96. Babban dare ga Babbar  Sarauniya ta. Wannan rayuwa ba za ta hana ki girma da nasara da ake nufi da ke ba da yardan Allah. Ki Kasance mai karfin imani,  manyan abubuwa suna kan hanya. 

  97. Dare lokaci ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali. Da fatan za ki sami kwanciyar hankali ta kowane ɓangare. Barkan mu da dare sarauniya ta.

  98. Duba sama ki ga faɗuwar rana tana faruwa a hankali. Tabbatar cewa za a magance matsalolin ki ta haka. Allah ya tashe mu lafiya masoyiya, na san zaki fito mun a mafarki na na yau!

  99. Barka da yamma ga kyakkyawar sarauniya. ina so ki kasance da ƙarfi sanin cewa ina tare da ke don ba ki hannun taimako. Barka da dare, ina son ƙaunar ki sosai!

  100. Yayin da kika ga wannan saƙon, na tabbata zaki yi dariya sosai. Ci gaba da dariya, Ina cikin rayuwar ki ne don sa ki yin hakan. Rana ta faɗi yau tare da cikakken tabbacin gobe zata sake fitowa. Idan babu abinda zai hana rana, babu abin da zai iya hana ki. Masoyiya, ki ci gaba da jin daɗin wannan dare.


Comments

Popular posts from this blog

1000+ Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Harda Nishadantarwa 2023

180+ Sakonnin Soyayya SMS na Safe, Rana, da Dare [Masoya Maza da Mata]

Kalaman Yabon Budurwa