100+ Sakon Soyayya SMS ga Saurayi
Sakon Soyayya SMS ga Saurayi
Masoyi na, duk sanda na fada maka ina son ka, kayarda dani dan kuwa har cikin zuciya ta nake kaunar ka. Soyayyar ka ke samar mun da natsuwa. Dafatan ka tashi lafiya.
Ina so na roki wata alfarma guda daya a wajen ka, zuciya ta na matukar kewar ka, tana bukatar ganin ka a kusa da ita. zan samu hakan?
Yau yazamo karo ta ba adadi wanda zuciya ta take rera mun wasu kalamai kuma take samun ita a baki. Ina son ka habibi na.
Duk da cewa baka tare dani yanzu amma ban damu ba, kasan meyasa hakan? Soboda nasan nan bada jimawa ba masoyi na zai zo gare ni. Wannan ya isheni farin ciki.
Duk sanda kawaye na suka tambaye ni mene ne abunda nafiso? A wannan lokaci kalaman ka da sunan ka kawai baki na ke iya fada.
Dazu, yanzu, anjima, gobe, jibi, har ranar da zan bar duniya, batare da ko kwanto ba, nabaka kyautar zuciya ta har abada. Dan Allah ka kula mun da ita.
Bantaba tinanin wata rana zato zo da nida kai zamu kasance masoyan juna ba. Amma gashi kaddarar ubangijin mu ta hadamu. Duk abunda zai kara shakuwa a tsakanin mu, shine abunda nake muradin aikata wa.
Nayi tinanin zan iya misalta irin kaunar da nake maka, amma sai gashi nakasa soboda bansan daga ina zan fara ba. Soyayya tsakani na dakai ba abun misaltawa bane. Dafatan ka wayi gari lafiya.
Aduk sanda aka anbaci kalmar so, zuciya ta hotonka take gani, kunnu wa ta muryar ka suke ji, idanu na kai suke hanje, hanci na kuma kamshin turaren ka suke ji.
Na fara kaunar ka tun kafin ka tinkare ni da manufar soyayyar ka. Amma bansan da wani ido zan kalle ka nafada maka ina kaunar ka ba. Ina kara gode wa ubangiji dan nasami babbar rabo.
Kamar yadda akace soyayya na sama cikin iskar da muke shaka, kaine ne dalilin kasance wa ta a raye. Dan Allah ka cigaba da sona kamar yadda nake son ka hubbi na.
Duk idan naci abinci ko nasha ruwa yakan ishe ni da wuri, amma bantaba jin soyayyar ka ta isheni a cikin zuciya ta ba.
Duk sanda na kulle idanu na, kai nake gani, idan na bude idanu na, sai na kara ganin ka. Babu abunda nakeyi a wannan duniyar ba tare da nayi tinanin ka a ciki ba.
A gaskiya bansan yadda zan kira irin wannan soyayyar tamu ba. A kullin kara ji nake kamar yau muka fara haduwa. Duk macen da take da saurayi irin ka tasamu komai a wannan duniyar.
Bana tinanin akwai wacce ta taba son ka kamar yadda nake son ka a wannan rayuwar. kullin zuciya ta bataso kana nesa da ita. tana kewar ka aduk sanda bamu tare.
Kashigo cikin rayuwa ta ka bani dalilin kasance wa cikin farin ciki, abunda nake tinanin na rasa ya dawo gareni. Kwarin gwiwan da kake bani kawai ta ishe ni farin ciki. Ina sonka masoyi na.
Masoyi na, bakomai yasa na tura maka wannan sakon ba illa na tina maka cewa akwai wata yar budurwa tana nan cikin farin ciki soboda kai. Ina kaunar ka.
Duk wani abu da nake nema daga da’ namiji, duk sun bayyana a wurin ka. Dan haka babu abunda bazan iya yiba dan cinma burina na kasance wa tare da kai ba.
Nafara sonka tin daga ranar da muka fara haduwa a duniyar nan. Kuma inaso kasani cewa bazan taba daina kaunar kaba matukar ina numfashi.
Duk sanda muke zance nake kallon cikin ida nun ka, ji nake kamar kada ka tafi ka barni. Amma babu yadda na iya. Amma abun farin cikin shine kullin mafarki da tinanin ka yakan raje mun kewa. Habibi na, ka kula mun da kanka.
Duk daren da banji muryan ka kafin na kwanta ba, wannan daren bata cika soboda bana bacci mai dadi. Jinake kamar muna fada da juna. Muryar ka nakeson ji a kullin.
Duk sanda aka ambaci sunan ka, sai naji kunya soboda an kira sunan rabin raina. Kasan yadda nakeji a zuciya ta kuwa duk sanda tinanin ka tazo mun?
A cikin samari dubu, kai kadai ka fito daban, kai kadai muradin zuciya ta, kai kadai abokin rayuwa ta, farin cikin zuciya ta na tare da kai. Wannan soyayyar ina zata kaini.
Soyayyar ka tasa nazama kamar sarauniya mai haskakawa cikin yammata. Dana tina kalaman ka sai naji kamar anbani kyautar da tafi kowanne a duniya. Ina kaunar ka.
Kafin na hadu da kai, banda wani aiki sai tinanin waye zai soni, waye zai kasance silar farin ciki na? sune tambayar da nake wa kaina. Amma haduwa da kai tabani duk wani amsar da nake bukata.
Duk sanda na kalli fuskar ka sai nayi addua acikin zuciya ta. Kasan wani addua nakeyi? Ina kara godewa ubangiji daya hadani da kai a wannan rayuwar.
Rayuwa ta tare da kai tasa yanzu bana shiga damuwa ko kadan. Babu abunda ke kwantar ma da hankali kamar farin ciki na. Ni dai fata na karka manta dani a wannan duniyar.
Idan akace nayi bayanin rayuwa a cikin kalma daya tak, babu abunda zan ce a matsayin amsa ta face sunan ka. Kai ne cikar rayuwa ta.
Duk rintsi duk wuya, duk halin da zaka shiga, inaso ka saka a zuciyar ka bazan taba guje maka ba. Domin araina kagama yi mun.
Kafin na hadu da kai nayi tinanin rayuwa ta cikakkiya ce, amma shigar ka cikin ta ta nuna mun cewa abunda nake zato bahaka bane.
Abunda yasa nake kara sonka kullin shine baka taba bari na cikin tinani, damuwa ko wani munin hali ba, amma kuma kana karfafa mun gwiwa, kuma har ila yau, shawarar ka nake bi a kullin.
A lokacin da ake sanyi, soyayyar ka na samar mun da dumi, dan hakan sanyi baya damu na. A lokacin da ake zafi, soyayyar ka na sana iya shakar iska. Kaga ai banda damuwa.
Kafin nafara soyayya da kai, banaso naji ana furta kalaman so a inda nake, soboda suna saka ni damuwa. Amma daga ranar da nafara ganin ka zuciya ta take muradin kalaman so.
Bantaba sanin ina da baiwa akan so ba sai da na hadu da kai. Haduwa ta dakai tasa na fahimci rayuwa ta sosai fiye da yadda nasan ta abaya.
Kamar yadda akace namiji na bukatar wuya, ita kuma mace na bukatar agaji. Ina mai neman alfarma daga wajen habibi na da ya rike hannu na ya sani a hanya mai bullewa.
Kasaka nagane wacece ni ba tare da nasha wahala. Wannan abu daka yi bazai taba sulwanta a zuciya ta ba. Ina masifar kaunar ka.
A duk sanda nafara tinanin ka sai naji kamar ina maye, soboda a wannan lokacin babu abinda ke kasancewa a zuciya ta face kai kadai.
Na dade ina zama cikin kadaici ina nema dalilin rayuwa a sauwake, sai ubangiji ya kawoka cikin rayuwa ta. Yanzu wannan kadaicin ya gushe soboda zuwan ka.
Nasan bazaka fahimci cewa farin ciki na da natsuwana na samuwa ne a sanda kake cikin koshin lafiya. Maganar gaskiya bazan iya jurar rashin ka a cikin zuciya ta ba.
Masoyi na, samun gurbi a cikin zuciyar ka tazamo muradi da kuma burin da nakeso na cinma wa a rayuwa ta.
Koda ace nagaji yau soboda aiki, hakan bazai iya hanani jin muryar masoyi na ba. Mahimmancin ka arayuwa ta tafi mun komai.
Wasu mutanen sun yarda cewa kudi shine karfi, masu kudi ke sarauta, amma na karya ta hakan soboda farin ciki da nishadin da nake samu daga wurin ka tafi mun komai har kudi.
Kasan meyasa nake godewa ubangiji, mutane sun dade haryanzu suna neman soyayyar gaskiya, gashi kuma cikin sauki nasami wannan son ta gaskiya.
Nasan kana tinanin cewa bai dace na bayayyana maka irin soyayyyar da nake maka ba yanzu, amma kayi hakuri zuciya ta ta kasa natsuwa ko kadan.
Duk sanda muke tare, sai naji kamar banaso wannan ranar ta kare, inna kalli fuskar ka, sai naji kamar kar mu rabu ka kasance cikin zuciya ta.
Idan ina lissafo dalilan farin ciki na, kana ciki, duk nasarar dana samu a rayuwa ta duk kaine a sama wajen ganin na cinma wannan burin ta wa.
Baka bukatar tambaya na akan irin soyayyar danake maka, ka guje ni na wuni daya kaga zahirin amsar da kake bukata.
Duk idan na kwanta bacci, sai nayi mafarkin kasancewa tare da kai a wannan duniyar. Ina maka fatan nasara da dacewa a wannan duniyar.
Bansan meyasa yanzu kishi nakeyi akanka ba. Banaso naga kawaye na suna magana akanka, sai naga kamar zasu kwace ka daga waje na.
Ganin ka akulin ba iya farin ciki kadai yake saka niba, ganin ka na saka ni cikin yanayin da bantaba shiga irinsa ba. Inaso na ringa ganin ka a kullin.
Abaya nayi tinanin zan iya zama ba tare da na ganka ba, amma halin dana riski kaina a ciki ba abunda zan iya tinawa bane. Kuma bana son hakan takara faruwa acikin zuciya ta.
Koda ace baka kawo mun ziyara ba, ni kam zan kawo maka ziyara dan zuciya ta bazata iya jurar kewar ka ba. Tana bukatar ka a kusa da ita a koda yaushe.
Masoyi na, duk sanda tinanin ka tazomun, yunwa da kishi daina jinsu nakeyi. Tinanin ka babu abunda yake kawo mun face farin ciki.
Na riga na hadu da samarai da dama, amma gaskiya haduwa dakai tasa nadai na wasu tinanin da nakeyi akan maza. Ka nuna cewa duk maza basu zama daya ba kuma ina godiya da hakan.
Duk idan nagan ka, sai hankali na ya kwanta, amma kuma duk sanda bamu tare, sai nashiga cikin damuwa kuma bani son hakan. Ina rokar ka ka kasance tare da ni.
Habibi na, meyasa a duk sanda na kalli fuskar ka, babu abunda nake gani face so da kauna? Shin akwai wani abu danayi daya sa kake so na haka?
Aduk sanda na kalli fuskar ka nace maka ina kaunar ka, toh har cikin zuciya ta ina nufin kaine kuma babu abunda zai iya chanza hakan.
Inaso nafada maka wani abu dan kullin shi ke yawo a cikin zuciya ta. Duk abunda babu kai aciki a rayuwa ta, to gaskiya wannan abu bai cika ba. Ina kaunar ka.
Kafin na hadu da kai, bana dariya, bana surutu, amma soboda kai, na dai na shiga cikin damuwa soboda ina da wanda zai sani farin ciki a duk sanda nake cikin damuwa.
A wannan tafiyar soyayyar mu, gaskiya babu abunda nake gani da kuma hanga a cikin ta sai farin ciki da cinma buri. Ka samar wa rayuwa ta mafita a sanda nake bukatar hakan.
Baka riga kazama miji na ba, amma soyayyar da kake nuna mun kamar ya zarce irin wanda nasa ba gani tsakanin wasu ma’auratan.
Wani abun mamakin shine kaf mutanen da na riga na hadu dasu a rayuwa ta, kai ka daine ka nuna mun soyayya ta gaskiya. Kuma ina godiya da hakan.
Ina matukar godiya da irin wannan soyayya da ka nuna mun. Haryanzu kullin sai na tina ranar farko da muka fara haduwa da juna.
Duk sanda aka tambaye ni wani rana nafiso a duniya, amsa ta itace ranar dana fara haduwa da kai a duniya.
Mafi soyuwar lokuta a wuri na sune lokutan dana ke satar kallon fuskar ka idan muna tare ba tare da kasan ina hakan ba.
Nafada maka wata sirri guda daya? Har so nake na kalle ka naga kana satar kallo na. Ka ga na samu abun tonar fadan ka ke nan.
Bara na fada maka abunda babu wanda ya taba fada maka daga zuciyar su, kai ne saurayi na farko dana fara gani wanda kyawun ka tasa na kasa bacci soboda tinanin irin halittar da ubangiji yayi maka.
A duk sanda na kalli fuskar ka, sai naji hankali na ya kwanta duk damuwa da bakin ciki sun gudu. Buri na a rayuwa shine na kasance a cikin zuciyar ka.
Kasan wani abun al’ajabi da ya faru yau kuwa? Yau na kasa maida hankali akan komai soboda tinanin ka kawai nakeyi.
Aduk sanda na kalle ka, babu abunda nake gani face farin ciki da far’a zalla. Bana bukatar komai a wannan duniyar matukar kana cikin zuciya ta.
Ina so ka ringa tinawa a kullin cewa ina kaunar ka kamar yadda duk wani halitta ke bukatar ruwa dan rayuwa mai inganci.
Komai game da kai ta daban ce. Yanzu bawai sai naganka kadai nake farin ciki ba, sunan ka kawai nagani yana sani cikin farin ciki matuka.
A kullin soyayyar ka a cikin zuciya ta kara yawaita yake fiye da yadda nake tinani. Bansan yadda hakan ta faru ba.
Babu abunda ke sani damuwa kamar mudade bamu hadu ba, jinake kamar kazo mu zauna tare. Ina matukar kewar ka.
Duk da cewa bamu tare, ji nake kamar kullin kana gaba na ina ganin ka. Ina so kayi mun alkawarin bazaka guje ni ba.
Bantaba tinanin idan nayi nesa da kai zanyi kewar ka kamar yadda nakeyi ba. Amma gashi kullin banda aiki sai kewar ka.
Aduk sanda nake zaune ni kadai, sai nayi ta kewar ka, tinanin ka kawai nakeyi, hoton ka kawai nake gani a cikin kaina.
Aduk sanda na tashi daga bacci duk safiya, sai na dauki waya ta na duba ko ka kirani ban dauka ba. Kiran ka danake gani ya kara tabbatar mun cewa kana kauna ta kuma nima ina kaunar ka.
Akwai abubuwa dayawa daya sa nake ji a zuciya ta bazan iya rabuwa da kai ba. Kuma wannan abubuwan bazasu misaltu ba. Amma idan kana son sanin su, sai kazo na fada maka.
Aduk sanda naji muryar ka kafin na kwanta, dadin da nake ji a wannan daren baya iya misaltuwa dan haka, duk abunda zai bata maka rai, zan daina hakan.
Inaso naje na kwanta ba dan ina jin bacci ba amma sai dan na kwanta nayi mafarkin ka muna shan soyayyar mu. Karka damu, idan muka hadu zan fada maka yadda mafarkin ta kasance.
Na turo maka wannan sakon ne soboda nakasa bacci dan zuciya ta taki samun natsuwa. Dafatan kana lafiya masoyi na.
Abunda ke sani farin ciki a kullin shine farin cikin da kake sani duk dare kafin na kwanta. Muryar ka nakeji kullin kafin na kwanta.
Masoyi namaka laifi ne? tinda safe na tashi daga bacci amma haryanzu baka riga ka kirani ba. In akwai laifin danayi maka kayi hakuri habibi na.
Zani sakar maka so kayo riko, kar naga kaji ya, idan kai haka so zai karu tsakanin mu dan, da shakuwa akan samu yarda, har so ta sanya kama da juna.
Idan waya ta ta buga sai zuciya ta ta cemun; ki dauka da sauri kafin ya yanke, tana tinanin kece, amma daga sanda ta fahimci ba ke bace ke kira, sai taji ba dadi.
Da farko nayi tinanin kawai abota ke tsakanin mu, amma zuciya ta ta kasa samun sukuni dan takamu da soyayyar ka. Bansan yadda wannan sakon zatayi maka ba. Nidai ina fatar baza kayi fushi dani ba.
Irin yanayin dana ke shiga soboda kai, bantaba jin irin sa ba. Aduk sanda muke tare dakai, jinake kamar anbani sarauta. Kamar mulki na hannu na.
Bayan na rabu da saurayi na, nayi tinanin bazan kara soyayya da wani ba. Amma haduwa ta da kai tasa nagane cewa ba duka aka hadu aka zama daya ba. Ina kaunar ka.
Ina godiya da irin wannan soyayyar da kake nuna mun. farin cikin danake ciki yasa yanzu yan gidan mu suna kishi akaina soboda farin cikin danake samu basu samun irin ta.
Zan iya zama daga safiyar rana zuwa daren rana ina kallon fuskar ka ba tare da kiyapta idanu ba. Matukar hakan zai sa naji na gamsu da ganin ka a rana.
Yana matukar wuya na nuna ma mutum yadda nakeson sa, amma gashi soboda fargabar kada na rasa ka, tasa na tinkare ka. Ina kaunar ka.
Ina matukar alfahari da irin namijin da ka zama. Kazamo irin saurayin da duk mace ke marmarin samu a rayuwar su. Gaskiya naji dadi sosai.
Aduk sanda nake cikin bakin ciki ko damuwa, soyayar ka kawai tana bani dalilin kasance wa cikin farin ciki. Matukar kana cikin farin ciki, to hankali na ya kwanta.
Na kwanta ina mafarki jiya daddare, babu abunda nake gani face kai kadai kana kallo na kana murmushi.
Maganar gaskiya, ina tsoron maza kafin na hadu da kai, amma kabani duk wani dalilin da zai sana kwantar da hankali na idan muna tare. Nagode sosai. Kai abun alfahari ne a wuri na.
Komai game da kai duk gaskiya. Babu karya a tattare da kai. Soyayya da kai tasa nagane cewa farin ciki tsakanin masoya na tare da namiji wanda yasan darajar sarauniyar sa.
Ga sako guda daya daga zuciya ta zuwa ga zuciyar ka. Ina matukar kaunar ka. Ka kasance tare dani a zuciyar ka.
Yau na tashi da safe ina tinanin babu wanda ya damu dani, amma kuma sai gashi ka kirani kana tambaya ta na tashi lafiya. Wannan itace kyauta mafi soyuwa dana samu a yau.
Ina kaunar ka. Wannan kalmar dana fada har cikin zuciya ta nafade ta. Zuciya ta na bukatar ka a kusa. Kazamo tawa ni kadai.
Tnx
ReplyDeleteB B N
ReplyDeleteHey
ReplyDeleteHello
ReplyDeleteUmmusuleim
ReplyDeleteNass
So
ReplyDelete