100+ Sakon Nuna Kewa Zuwa Ga Saurayi da Budurwa
Karanta sakonnin nuna kewa zuga ga saurayi da budurwa. 50 din farko zuwa ga saurayi. daga 50 - 100 zuwa ga budurwa.
Sakon Nuna Kewa Zuwa ga Saurayi
Barka da wannan lokaci habibi. Dafatan kana lafiya? Tinda ka nisanta dani na shiga damuwa. Tinanin ka yafara rinjaya ta soboda banda wani aiki sai tinanin ka. Idan akwai laifin danayi maka, kayi mun afuwa.
Nasa wa kaina yin wata gasa tsakani na da zuciya ta. Nayi tinanin nayi wuni daya batare da nayi maka magana ba. Amma ina so na tabbatar maka da cewa halin dana shiga ba abunda zanso nakara fuskanta bane. A farko na dauki abun wasa, amma kuma hakan yasa na shiga wata halin mara dadi. Ina kaunar ka hubbi na.
Masoyi na. Duk da dai bamu kusa da juna soboda lamarin yau da kullin. Ina so kasani cewa zuciya ta bazata taba daina son ka ba koda me zai same ta. Ka shigo cikin rayuwa ta ka kyautata mun, yanzu lokaci nane nima nayi hakan. Ka kula mun da zuciyar ka kada komai ya same ta.
Ina ji mutane suna cewa lamarin ciwon so ba kamara bace, amma nayi watsi da hakan soboda bantaba tinanin wannan ciwon zansame ta ba. Na shiga wata yanayi wanda babu abunda nakeyi face tinanin ka safiya, rana, da kuma dare. Shin zamu iya haduwa yau ko gobe. Ina son ganin ka.
Babu abunda ke sani kewar ka kamar na juya na kalli gefe naga baka awurin, na dauka waya ta, na kira ka bata shiga. Wannan lamari na tasar hankali na soboda bana iya jure wannan halin da nake ciki. Masoyi na, dafatan kana lafiya habibi na. Ka kala mun da kanka.
Tafiyar kwana daya kawai kayi amma jinake kamar kayi tafiyar shekaru 10. Meyasa zuciya ta ke kewar ka haka ne. Dan Allah habibi na, kayi sauri ka kamala abunda kaje yi ka dawo gareni. Allah ubangiji ya kiyaye mun kai dare da rana. Ina kaunar ka
Duk idan na kwanta ban ganka ba, banji muryar ka ba, baccin bata ba mun dadi ko kadan, ji nakeyi kamar wanda ke zazzabi soboda halin da muke ciki babu banbanci. Ina matukar kewar ka baby na.
Meyasa nake gani kamar matsayina a zuciyar ka yana rage wa. Duk sanda nake so naganka, alokacin wani abu naka ke taso wa. Haka zan hakura dan nasan bazan ganka ba. Amma ina rokar ka wata alfarma guda daya, idan akwai inda na bata maka rai ko nayi wani wanda bakaji dadin sa ba, kayi mun afuwa ka dawo gare ni. Ina kaunar ka.
Yana matukar taba min zuciya ta yanzu baka samun lokaci na kamar yadda kake dashi abaya. Nayi duk yadda zanyi nagane dalilin hakan, amma nakasa sanin meyasa. Ina rokar ka kasance tare da ni soboda zuciyata ta kasance cikin farin ciki.
Kullin idan na zauna sai nayi ta tinanin yadda rayuwa ta zata kasance duk sanda ka nisance ni. Hakan zai matukar tabani sosai. Burin zuciya ta shine ka kasance akusa da ita akoda yaushe. Ina matukar kaunar ka.
Da zaka iya ganin zahirin abunda ke cikin zuciya ta, da kagane cewa duk abunda baki na yake furta maka gaskiya ce. Bantaba kaunar wani da’ namiji kamar yadda na mutun maka ba. Har mamaki nakeyi akan hakan. Ina matukar kewar ka.
Barka da wannan lokaci baby na. Dafatan ka wuni lafiya cikin aminci? Kullin idan na zauna, bana da wata aikin yi saidai tinanin ka babu dare babu rana. Koda yaushe hakan ke faruwa. Kazo gareni masoyi na ka magance mun matsalar danake fama da ita.
Abu kamar wasa amma yanzu yana neman zama wata abun daban. Masoyi na, ban san yadda kake ji a cikin zuciyar ka ba, amma ina rokar ka kada kayi fushi dani, zan iya shiga yanayi mara dadi soboda rashin ka. Ina matukar kewar ka habibi na.
Kawaye na suka tamabyeni mene ne idan na gani zai faran ta mun rai yasa ni farin ciki, nace masu kallon fuskar ka asanda kake murmushi. Suka kara tambaya ta mene ne zai saka ni fushi da damuwa, nace masu wuni daya batare da ji daga gare ka ba. Ina kaunar ka masoyi na.
Yanayin danake ciki yanzu, bantaba tinanin zan taba shiga irin ta ba. Amma gashi yau nashiga soboda kai. Zuciya ta tana bukatar ka akusa da ita a koda yaushe dan ta samu natsuwa. Ina rokar ka kafitar dani daga wannan yanayi mara dadi.
Ina matukar so naganka akusa dani. Yadda idan na juya kai zan gani, idan na kalli gaba na kai zangani, idan nadauki waya ta, sakon ka zangani. Inaso duk abunda zanyi yazamo akwai ka acikin ta. Hakan zai sani farin ciki sosai. Zuciya ta na bukatar ganin ka akusa da ita.
Bansan mene ake nufi da kewa ba, saida nayi wuni daya banganka ba. Banaso ko da wasa nakara shiga irin yanayin da na shiga soboda rashin ganin ka. Buri na na kasance akusa da kai akoda yaushe. Ka kula mun da zuciyar ka.
Aduk lokacin da kake fushi dani, babu abunda zuciya ta ke fada mun face nazo har inda kake nabaka hakuri, amma kuma damuwar itace bansan inda zan same ka ba. Inaso kasani cewa dai dai da sa’a guda, soyayyar ka bai taba raguwa acikin zuciya ta ba. Kai ke da sarautar zuciya ta dan haka ka rike mun ita hannu biyu.
Abaya bansani ba, amma yanzu kam nasani. Abu kamar wasa amma gashi yasa na fara kewar ka. Nayi tinanin zan iya yin wuni batare da na ganka ko naji muryar ka ba. Amma gaskiyar lamari itace hakan bazai yuba. Duk abunda zai sa nakara shiga irin halin da na shiga, na barta. Na rabauta da samun ka arayuwa ta.
Jiya bayan rabuwar mu daddare, sai naji kamar nayi kuka soboda bangaji da ganin ka ba. Nakosa naga ranar da zan bude idanu na naganka akusa dani cikin farin ciki. Mufita tare dan shakatawa. Ina kewar habibi na.
Kullin muna tare da juna cikin farin ciki. Amma gashi yau zamu dauki wasu kwanaki bamu tare da juna. Inaso kasani cewa matsayin ka a zuciya ta, babu abunda zai same ta. Zanyi kewar ka sosai masoyi.
Tunda muka je hutu, babu abunda na zauna nake buri kamar naga mundawo hutu mun kasance tare kuma. Kullin idan na zauna bani da wata aiki sai tinanin ka a koda yaushe. Babu abunda nakeyi wanda tinanin ka baya cikin sa, ina matukar kewar ka.
Aduk sanda nake tinanin ka, babu abunda ke faran tamun rai kamar na tina lokutan da muke tare cikin farin ciki da annashuwa. Hakan ke iya kwantar mun da hankali. Yaushe zaka dawo daga wannan tafiyar ta ka?
Jiya kace mun na kwantar da hankali na babu damuwa, amma haryanzu hankali na ya kasa kwanciyar, tun jiya daddare idanuna suke bude. Babu abunda banyi ba soboda nayi bacci ba, amma baccin yaki zuwa soboda na kasa samun natsuwa. Ina kewar ka sosai.
Tunda kayi tafiyar nan na daina samun sukuni, kullin ni banda aikin yi sai tinanin ka. idan na zauna a gida tinanin ka kawai nakeyi, idan naje shago, bana iya maida hankali nayi abunda yakamata. Tunda ka nisance ni nadai na samun sukuni. Ina kewar ka sosai.
Kashigo rayuwa ta ka cike gurbin dayake damuna. Kullin ina kasancewa cikin farin ciki soboda kana kusa dani, amma gashi yanzu zakayi tafiya. Ina so kasaka a ranka cewa zuciya ta na tare da kai kuma kullin zanyi maka addua har sai ka dawo. Ka kula mun da kanka.
Kwana 2 kenan da tafiyar ka amma yanzu har nariga nayi sanyi. Shin yaushe zaka dawo ne habibi. Kewar ka na shigar dani wata yanayi wanda babu dadin ji. Kadawo gare ni masoyi na. Ka kula mun da kanka.
Ina ganin kawai kamaka zanyi na kulle ka soboda kullin idan nafito kai zangani, idan zan ci abinci, kai zangani. Idan zan kwanta, kai zangani. Kaga ahakan, bazanyi kewar ka sosai ba kenan. Ina kaunar ka masoyi na.
Duk abunda zai sa ka nisance ni ba abunso bane awuri na, koda ace ban fada maka ba, yana nan acikin zuciya ta. Duk idan na zauna, bani da wata aikin yi sai kallon hotunan ka, saka call record wanda muka yi dan kawai hankali naya kwanta nasami natsuwa. Ina kaunar ka.
Duk ranar da banga fuskar ka ba, wahalar da kwakwalwa na nakeyi a wannan ranar. Zanen fuskar ka nake kwatantawa acikin tinanina wanda kuma ke kawo mun ciwon kai. Ni koda sau daya ne na kalle ka, ya wadatar mun.
Babu abunda ke natsar dani ya samun kwanciyar hankali kamar yadda kunnuwa na suke natsuwa suji murya ka yayin da kake zubar kalamai. Tunda muka hadu, har yau ban riga naga wata bacin rai ba.
Idan nayi wasu abubuwan sai ace kishi nakeyi, amma idan banyi abunda zai sa na zauna a zuciyar ka ba, me zanyi toh? Babu wuri mafi dadi da sha’awar zama kamar zuciyar ka. Shiyasa nakeso na kasance akusa da kai. Ina kewar ka sosai.
Ban tabbatar da sa’aoi 24 ne a rana daya ba, har saida nafara kewar ka. Duk bayar sa’a sai na duba waya ta ko sakon ka tashigo. Zuciya ta ji take kamar tafito neman ka da kanta, ina kaunar ka.
Aduk sanda ruwan sama ya dauke, shuka suna shiga wata hali marasa dadi dan wa’adin su ke neman karewa. Misalin irin yanayin danake shiga ke nan idan baka akusa dani. Ina kewar masoyi na sosai.
Dan Allah inaso nasani idan na bata maka rai. Lokaci guda kawai ka nisance ni ka daina zuwa inda nake. Kullin cikin tinanin ka nake wuni. Nayi kokarin jure hakan amma kuma ba abu mai sauki bane. Kayi hakuri ka dawo gare ni. Kewar ka nake.
Duk idan bamu tare da kai, bana iya samun natsuwa ko kadan. Abunda ke kwantar mun da hankali shine na dauki waya ta na kalli hotar ka. Wasu lokutan na gwanmace nayi bacci. Duk kewar ka tasa hakan.
Har kawaye na sun fara ganin sauyi game dani tunda ka nisance ni. Kullin fita nikeyi daga cikin su na zauna nikadai. Masoyi na, yaushe zaka dawo daga wannan tafiyar taka? Nakosa ka dawo gare ni.
Duk idan dare tayi na zauna nikadai ina kallon taurarin dake sama, sai na ringa tinanin irin lokutan da muke tare muna cikin jindadi da farin ciki, amma gashi yanzu bakada lokaci kamar yadda kake da ita abaya.
Duk da cewa idan bamu tare ina kewar ka, amma dana kalli zoben dake hannu na, sai naji sanyi acikin. Hakan na tabbatar mun da tarayyar ka dani. Ina kaunar ka habibi.
Ina zaune kashigo cikin rayuwa ta ka samar mata abunda ta rasa, ka magance mata duk wata matsala da take fuskanta. Yanzu kuma zakayi nesa da ita, nidai fata na shine, aduk inda ka tsinci kanka inaso kasani cewa ina kaunar ka har cikin zuciya ta.
Tafiyar kwana 1 yanayi na shekara1. Haka nake fuskanta tun daga ranar dakayi nisa dani. Amma kuma inaso ka maida hankali sosai a aikin ka. Kazamo wanda sukeji da shi. Zuciya ta tana kewar ka.
Duk da dai yazamo dole nayi karatu kafin naci jarabawa, babu yadda zan iya karatu ba tare da nagan ka ba. Masoyi na kazo gare ni na sami sukuni. Ina matukar kewar ka sosai.
Babu abunda ke sani damuwa kamar natashi daga bacci na duba waya ta baka turo mun sako ba, baka kira ni ba. Hankali na baci yake yi. Komawa nake kan gado na kwanta. Shin zamu iya haduwa yau masoyi na?
Yanzu nakara tabbatar da babu wuri mafi niashadi da farin cikin zama kamar cikin zuciyar ka. Daga ranar daka koma makaranta na fara shiga kunci, karamin abu ke bata mun rai. Zuciya ta bazata iya jure rashin ka akusa da ita ba.
Ya akayi nabar zuciya ta tasani cikin azabar so. Nakasa hakuri na shiga damuwa da kunci sosai. Ka taimaka mani ka tausaya mini ka dawo gare ni. na shigo inda ke saka zuciya tiriri.
Ina kewar ka masoyi na rabin raina. Yau kwana 2 kenan bamu hadu ba. Nasan aiki yayi maka yawa. Inaso aduk abunda kakeyi, ka kula mun da zuciyar ka fiye da yadda kake kula da kanka.
Zuciya ta, idanu na, kunni na, jiki na, gabobin jiki na duka, burin su su ganka akusa dasu. Ganin ka ko jin muryar ka shine muradin su. Ko zasu samu hakan yau? Ina kaunar ka.
Duk idan nafara kewar ka, sai na kwanta nayi bacci ko dan nayi mafar kin ka. Wasu lokutan ina dacewa wasu lokutan kuma sabanin hakan. Yanzu kai nakeson gani a zahiri ba’a hoto ba. Ina kewar ka sosai.
Nayi sa’ar samun saurayi kamar ka. Matukar na fada maka ina kewar ka babu abunda kake kamar kaga kazo gare ni. Ina matukar godiya da farin ciki da hakan. Ka kula mun da kanka.
Kullin da safe idan na tashi, sai nayi maka adduar tsari daga muggan mutane. Da rana nayi maka adduar dacewa. Daddare kuma nayi maka adduar tashi cikin koshin lafiya da jindadi. Zuciya ta na matukar kewar ka habibi na. Ka kula mun da wurin zama na cikin zuciyar ka.
Saƙonnin Nuna Kewa a Soyayya Ga Budurwa
Ba tare da ke ba, rayuwar yana zama tamkar babu kowa, kuma zuciya ta ta fi komai a gare ni, na damu da Ita sosai. Ba za ki iya tunanin yadda nake kewar ki ba.
Ina da wani Babbar damuwa. Na kamu da wata cuta da ake Kira da "ina kewar ki sosai kuma ina da bukatar ganin ki a yanzu " Don haka, zaki iya taimakawa kuwa?
Yayin da na zauna, ina kokarin fuskantar matsalolin rayuwa na ta yau da kullun, Abinda kawai nake iya tunawa shine yadda nake kewar ki. Na ƙosa na kara sa idanu na akan ki.
Babbu shakka, na san wannan soyayyar da muka raba zai kasance tare da ni har abada. Amma da akwai laifi idan na so wannan abin dake tsankanin mu ya kara ƙarko? Na yi kewar ki da har ko wani gaɓa a jiki na yana son ganin ki!
Komai da na kalla, yana tuna mun da ke, Saboda kin kasance komai a rayuwa ta da ma rayuwar ita kanta. Duk da haka, yanzu baki nan tare da ni. Allah ya dawo dake lafiya.
Ina kewar komai tattare da ke. Kyakkyawar idanun ki dake kallo na a kowanne safe, ga kamshin ki mai lullebe ni, ga kyakyawar murmushin ki mai tabbatar mun da cewa akwai kyawu a duniya, dan Allah kiyi ki dawo. Ina kewar ki.
Na faɗa cikin rigima da kaina, saboda rabin jiki na yana son ya kyale komai kawai saboda kasancewa da ke, kuma ɗaya rabin yana son ya jira ki dawo don mu ci gaba da rayuwar mu tare. Ina kewar ki sosai da kullun ina rasa matakin da zan ɗauka.
Masoyiya, kin san akan ki zan iya zuwa ko ina komin nesa, saboda in kara ganin ki ko da sau ɗaya ne kawai. Amma rayuwar mu ta zo a yanayin da bazan iya zuwa ganin ki ba. Hakan ba yana nufin soyayya ta gare ki ya ragu bane. Kewar ki ya zame mun abin yi ko da youshe.
Tun lokacin da kika tafi, ina jin wani kaɗaici tattare da ni, fiye da yadda uwa ke ji idan bata ga ɗan ta ba. Ina matuƙar son dawowar mu tare.
A wannan lokaci na yanzu, mafarki na, tunani na, fata na, kamai na, ke ce. A gaskiya ba zan iya ɓoye irin kewar da nake miki ba. Ina matukar kaunar ki masoyiya ta. Ki ji daɗin ki.
Idan kina tare da ni, komai yana zama kamar wata yanki ne na tatsunniya. Amma idan baki tare da ni, kamar ni na babbar tauraro a muguwar fim. Da fatan zaki dawo gare ni nan ba da jimawa ba.
Ranar da na fara ganin ki shine farin wani nau'i na farin ciki a rayuwa ta. Har kafin tafiyar ki, ni na mutum mafi farin ciki a kaf duniya. Amma da tafiyar ki, na koma mafi bakin ciki! Ina kewar ki fiye da yadda kike tunani.
Da wannan saƙo, ina son ki sani cewa saurayin ki shine wanda ya fi kowa ƙadaici a yanzu haka saboda masoyiyar sa batan nan tare da shi. Rashin ki a kusa da ni yana cutar da ni. Ba zan iya jiran ranar da zaki dawo gare ni ba.
Na san bai wani daɗe ba da rabuwar mu , amma gaskiyar magana shine na fara kewar ki a sekan ɗin da kika faɗa mun "sai anjima". Ko sekan ɗaya bana iya yi cikin daɗi.
Kowanne dare nake kokarin barci domin ɓa daina tunanin ki yana komawa ko in ƙasa barci saboda yawan tunanin ki da mamaye mun zuciya, ko kuma ki fito mun a cikin mafarki. Mafarki akan rayuwar mu da ke. Wannan shine yadda nake kewar ki.
Gujewa daga gare ki yana sa ina jin kamar ina jin tamkar ban cika ba. Kamar an haife ni ne nayi amfani kawai idan kina tare da ni. Don haka, ki dawo gare ni masoyiya.
Babu macen da ta fi ki kyau, ko ta fi ki koƙari. Haka kuma babu wanda nake kewa a yanzu kamar ki. Wannan shi yasa duk na bi na ƙosa ki dawo. Da fatan kina cikin ƙoshi lafiya.
Barka dai masoyiya, ramin da kika bari bayan tafiyar ki yana da girma soai da har yanzu na kasa cike shi. Na fahimci ta hanya ɗaya ce kawai zan iya cike ta. Shine idan na sanya idanu na akan ki! Kewar ki nake sosai.
Na san bai dace ba ace maza suna kuka, amma nisanta na da ke na wannan tsawon lokaci yana gab da sani na rasa hankali na. Da ma na juya wuya na ina gan ki a baya na.
Idan kina nesa da ni, kowanne ɗaya daga cikin ayyuka na, kalmomi na, da tunani na, yana komawa ne zuwa ranar da zan sake ganin ki. Idan ba ki, da gaske ba zan iya wani abubuwa ba.
Tun da kika tafi, ban taɓa daina tunanin ka ba ko da na lokaci ɗaya ne, kina zuwa mun a tunani ko da yaushe, ina ma ganin ki a ko ina. Dukkanin mata sun zama ɗaya da ke a waje na. Don Allah kiyi ki dawo gare ni.
Ban ma san ina raye ko bane raya ba. Tun da kika bar ni, ina raye a zahiri. Amma a waje, ina mutuwa a kowanne minti da zai wuce.
Babu shakka na san bai wani jima ba da tafiyar ki, amma ko wani sekan ya wuce sai na ji kamar shekara ɗari ne suka wuce. Fata na shine ki dawo nan ba da daɗewa ba cikin ƙoahin lafiya. Komin yaya nayi yunkurin rarrashin kai na, ba ya yiwuwa na sami farin ciki ba ke.
Ko da ya kasance muna magana da junar mu ta hanyoyin sada zuman ta, va za a iya haɗa shi da ganin ki a zahiri ba. Wannan shi yasa nake kara kewar ki a duk lokacin da muka yi waya. Ina son ki, so na hakiƙa.
Sanin ki shine abu mafi inganci da ya taɓa faruwa da ni. Yin rayuwa kuma a nesa da ke kuma shine mafi muni! Ina kewar ki masoyiya.
Bazan san garin yaya hakan ta faru ba, amma rayuwa ya bayyaanar da shi za mi rabu na wani ɗan lokaci. Baki san yatda na tsani haka ba! abin da kawai nake so shine na sa ido na akan ki, domin ina kewar ki fiye da yadda ɗan adam zai yi tunani.
Ta yaya zan iya bayanin yadda nake ji game da ke? Da kwai zafi, haushi, kuma kamar ma ba zan iya numfasawa ba. Ina kewar ki gimbiya ta. Allah ya dawo mu da ke lafiya.
Ke ce abinda na fi so kuma kawai magani da nake bukata don tsira. Ya masoyiya mafi kyawun budurwa, na gode don kasancewar ki amma na yi kewar ki da yawa a wannan lokaci.
Babu kowa a cikin zuciya ta in ban da ‘Ke.’ Babu abinda ya fi zafi kamar rashin kasancewa a kusa da ke. Don Allah ki zo wuri na. Ina kewar ki sosai.
Me ya sa Allah ya kirkiri kyakkyawar abu mai suna SOYAYYA, musamman ma da ya san saurayi kama na zai yi matukar damuwa da bakin ciki idan ya yi kewar budurwa irin ki? Ba na neman da yawa, abin da nake so in yi shine ganin ki a kullun. Ina kewar ki
Kewar ki ba al'ada ce kawai ba, jarrabawa ce mai kisa. Kewar ki ba kawai tilas bane, raɗaɗi ne mai tsanani. Mafi muni game da kewar ki shine, ba zan iya hana rai na tunanin abubuwan da za mu yi idan muna tare a yanzu ba. Ina kewar ki.
Hatta munanan dodanni ba za su iya ba ni tsoro ba kamar yadda nake jin tsoro lokacin da nake nesa da ke. Ina kewarki baby. Ba lallai ne in yi tunanin ki da gangan ba domin koyaushe kina cikin tunani na. Ina kewar ki masoyiya ta.
An gano ni da mummunar cutar “I Miss You” wanda a dalilin ta nake fama, kuma na kasa samun sauki, domin ba zan iya jurewa ba da kewar ki koyaushe. Ina kewarki masoyiya.
Kasancewa tare da ke ko da daƙiƙa ɗaya ina jin kamar samun rayuwa ta farin ciki. Kasancewa nesa da ke ko da na daƙiƙa ɗaya, kamar an kulle ni ne na tsawon rayuwa cikin wahala.
Ban san yadda zan bayyana yanayin zuciya ta ba. Zan rasa kalmomi kuma ba ma zan iya farawa ba. Kalli idanu na kawai za ki iya ganin zafin da nake ciki. Abinda nake so… shine in kasance tare da ke.
Tazarar da ke tsakanin mu ta saci farin ciki na, komai na rayuwa kamar maras amfani ne. Ina bukatar ki dawo ki cece ni daga wannan ƙuncin, ina kewar ki. Yadda kunkuru ke ji ba tare da harsashi ba haka nake ji ba tare da kasancewar ki ba. Ina kewar ki.
Akwai rami a cikin zuciya ta kuma mai gyara ɗaya tilo da zai iya toshe shi itace ke! Kar ki manta da kawo kayan aiki mafi mahimmanci waɗanda zasu taimaka wajen toshe wannan rami - murmushin ki da muryar ki! Ina kewar ki.
Ƙaunar ki kamar iska ce. Ba zan taɓa daina son ƙarin ta ba, amma ba zan iya taɓa shi ba, saboda ba ki nan kuma ina kewar ki sosai.
Ƙaunar ki abin al'ajabi ce kuma ba zan iya jira ba na gan ki idan na dawo daga ƙarshe. Don Allah kar a manta da ni, zan dawo da zarar na gama kuma in cika ki da kyauta. ina kewar ki.
A cikin dukkan mafarkai na, ban yi imani ba zan iya ƙare da wani mai ban mamaki kamar ki ba. Ina kewar ki! Ina kewar ki tun ranar da na tafi. Kin dace da ni kuma idan na dawo zan tabbatar miki da irin son da nake miki.
A yanzu ina jin kamar ni ne wata kuma ke ce rana. Basu taɓa ganin juna ba amma suna ci gaba da fatan zasu haɗu wata rana. Ina kewar ki.
Kewar ki tamkar wani guntun zuciya ta ya ɓace. Ba wata rana da ba na tunanin ki da duk abubuwan da muka yi tarayya da su. Ina kewar ki sosai.
Ina alfahari da ke baby. Kasancewa nesa daga gare ki yana da sauki sanin cewa kina koƙarin bin burin ki ne. Kin cancanci duk nasarar da zaki samu, kuma ina fatan Allah ya baki sa'a.
Shin kin san cewa ce wanda na fi so a duk faɗin duniyar nan? Wai ina son ki sani ne. Ina son ki kuma ina kewar ki masoyiya ta. Mutane biliyan takwas a duniya, amma ke kaɗai nake so.
Duk yadda na yi ƙoƙarin fitar da ke daga rai na, ba zan iya janye kai na daga tunanin ki ba. Buri na kawai shine in sake kasancewa cikin tarayya da ke. Ina son ki kuma ina kewar ki!
Ban taɓa fahimtar ainihin abin da ake nufi da kewar wani da gaske ba har sai da muka rabu. Allah ya dawo mun da ke lafiya.
Duk lokacin da na ji sautin isowar saƙo, ko kiran waya, koyaushe ina tunanin ke ne. Ina fatan sake ganin ki. Ba zan iya gano dalilin da yasa nake kewar ki ba? Kuma ban san dalilin da yasa zuciya ta ke son ganin ki da yawa ba? Wataƙila, saboda ina ƙaunar kine.
Ina kallon hotunan mu a yau, ina mamakin yadda kike da kyau. Ba kawai kyakkyawa bace ke, amma kina da kirki, hazaƙa, da karamci. Ina jin daɗin haɗuwa da ke.
Ba zan taɓa daina kewar ki ba, ko da ƙasa ta daina jujjuyawa, tsuntsaye sun daina tashi, kyandirori sun daina ci, kuma zuƙata sun daina bugawa. Kowane lokaci, in ba tare da ke ba, yana ina jin kamar zaki dawwama a nesa, kuma ba zan iya jure wannan kaɗaicin ba kuma. Ina kewar ki sosai masoyiya.
Ya masoyiya ta, ba zan taɓa iya jure radaɗin nisantar ki ba. Ba tare da ke ba, duniyar tawa tana da tawaya! Bana son idan zan faɗa miki abu in ga baki a kusa da ni. Ina kewar ki.
Comments
Post a Comment
Drop Comment here